Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 84

Chapter 84

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta tashi "bari naje nasan ana jirana. Don Allah ka kirani fa" Yayi murmushi "in sha Allah ina zuwa gida zaki ji wayata" Sai da ta soma tafiya ta dan daga murya yadda zaiji tace "Yassar" Ya juyo yana kallonta "dama karya nake yi, so nake kawai kace kana sona" daga haka ta tafi. Ya zauna yana sosa keya. Yana tunanin ko dai soyayya a jinin dangin Jikamshi take. Tasha fada kuwa a wurin Mami. To bukatarta ta biya ko kadan ranta bai baci ba. ****** 'Yan uwan Asmau sunyi gaba da harda yi mata tayin ko zata bi motar Umar tunda Ainau ce kawai a ciki. Col. Ishaq ya jefi Shemau da kallo harda harara ta kwashe da dariya. Dama tsokanarsa tazo yi. Sai da yayi sallama da abokansa sannan yazo ya sameta a inda yace ta jira shi. Jikinta yayi sanyi tunda taga ya sallami 'yan motar tasu. Har wani dan tsoronsa take ji. Ya kula da canjin yanayinta a ransa yace baki ga komai ba. Hannunta ya kama ya tayar da ita suka nufi wurin motar yaki sakin hannun. Wani iri take ji daban don bata saba ba. Idan ba bisa lalura ba tana iya rantsuwa banda Abubakar babu wani namiji da ba muharraminta ba da ya taba mata hannu. Shima jin hakan yake har ransa. Ya dade yana jiran ranar da Asmau zata halatta gareshi ya tabata batare da tsoron zunubi ba. Sai ma lada da zai biyo baya. Gaba ya bude mata ta zauna sannan ya zagayo ya zauna wurin dreba. Ya tayar da motar sannan ya kamo hannunta ya dora akan giyar. A haka ya saka giyar ya soma tuki cikin nutsuwa. Zuciyar Asmau ta kusa ballo kirjinta don tsoro. "Tunanin me kike yi ne" Ta dan rufe idonta ta bude "babu komai" muryar nan a salihance take fita. "Are you sure, har tunanin abinda zan iya yi miki daga nan zuwa na kaiki gida bai zo kanki ba?" Ta shiga kifta idanu kamar mara gaskiya. Saboda dare ne kuma titin babu motoci sai tsiraru shiyasa yake iya kallon bangaren da take. "Kinyi shiru, bari na fada miki abinda naji zuciyarki tana cewa" Kallonsa tayi tana jiran taji abinda zai ce. Shima sai da ya dan juyo sannan ya mayar da ido sa ga titi. "Zuciyarki tace yau dai gani ga Jikamshina a matsayin maya da miji. Daga nan zuwa ya kaini gida zanyi kokari ko kiss ne nayi masa" "La'ila ha ilallahu, ni banyi wannan tunanin ba..." Asmau ta fada tare da cukwikuye kanta cikin mayafinta. Kunya taji har bazata iya misalta ta ba. Shi kuwa dariya yake mata. Yana son wannan kunya ta Asmau. " ko kwana daya bamuyi da aure ba har kin fara karyata ni?" Ta dan dago kanta daga kan cinyarta da ta rufe "ba haka nace ba fa" Nishadi kawai yake ji gashi ga Asmai a matsayin maaurata. Ya daga gira daya "to yaya, kin amince kinyi wannan tunanin?" Ta soma girgiza kai sai taga ya bata fuska. Tayi saurin cewa "Allah Sarki banyi ba amma dai naji nayi tunda haka kake so nace" "Good girl, that means I will get one kafin mu rabu yau." Ta turo baki don ta san idan ta sake magana wani abin zai kuma fada. A hakan ma bata tsira ba ya kalli dan bakin ya sha janbaki "Mayar da lips din mana, ai ba yanzu za'ayi ba sai mun isa gida. Naga alama kin fini zumudi". Kwafa tayi tana tunanin me zatayi masa, tukinsa yake hankali kwance. Tace "Jikamshina" "Yes sweetheart. Kinsan fa yanzu duk wani suna da ake kiran masoyi a duniya zan kiraki dashi" "Zan rama ne." Yayi dariya "dama haka nake so. In ce wani abu ki rama yanzu?" Ta gyada kai "I want to hug you" Ta bata fuska a shagwabe "wallahi zan maka kuka" Ya sami abinda yake so. Tana jinsa yana dariya ta ja mayafi ta rufe fuska har suka isa gidan Jafar. Yaron makota da yake masa gadi ya bude ga motarsa nan alamun sun dawo. Ta kama kofa zata bude taji ta a rufe. Yace mata "Kiyi hakuri kiyi min magana please" Ta noke kafada, ya ce "to shikenan ina zuwa. Umarni na baki kada ki bude kofar nan" Itama nata salon ramawar kenan yau duk abinsa bazata yi masa magana ba har ya tafi. Tana kallo ya bude ya fita ya zagayo ta gefenta ya bude mata. Sai da ta ziro kafafunta waje kawai ya durkusa a gabanta ya kafa kafar ya cire mata takalma yana bin yatsun kafar yana matsawa. Kasa magana tayi saboda bata yi zaton abinda zaiyi mata ba kenan. Ga kunya kamar tayi ihu. Har fargaba take kada wani ya fito ya gansu. Ta dan ja kafar ya rike sosai ya cigaba da matsawa yana magana a hankali. "Tun dazu kike dingishi kina tunanin zan bari ki shiga ciki ne kice wata tayi miki tausa a kafa?" "Don Allah ka dena kada yaya Jafar ya fito" tana magana idonta na kan kofa. "Matsoraciya bari kiga wani abu" bata ankara ba taji yayi mata daukar jarirai. Abinka da dogon soja tashi yayi ya nufi hanyar kofar gidan da ita. Asmau ta gama tsurewa ga tsoro tasa hannuwanta biyu ta kankame masa wuya "Ji...Jikamshi don Allah ka saukeni" "Anki din, ki sassauta rikon nan kin shake ni" Ta dan marairaice "idan aka fito aka ganmu fa" "Zaki sa na shiga dake har dakin da kike kwana idan bakiyi shiru ba" Shirun tayi don kada ta kara tunzura shi. Kanta a wurin kafadarsa ya cigaba da tafiya ta lumshe idanu. Komai nasa daban yake mata. Aure dadi aure lada yau ba tsoron fada take yi ba idan da wani zai fito ya gansu. Ko waye sai dai taji kunyarsa sabanin da wani namijin ne kawai da babu aure a tsakaninsu. Taji tsoron a kamasu sannan ta hada da lodin zunubi. Allah Ya kara karemu daga soyayyar tabe tabe babu aure wadda wasu suke yiwa kallon burgewa. Tunaninta ya katse da taji ya ajiyeta a bakin kofa sannan ya bata takakmanta. Ya daidaita fuskarsa da tata ta hanyar rankwafowa ya rage tsaho suna jin numfashin juna. Idonta a rufe don fargaba. "Ina jin na cancanci wannan kiss din da kika yi tunani dazu" Bata bude idon ba taji ya hada bakinsa da nata. Alhamdulillah cikakken farinciki yana tare da aure. Da da yanzu ta kwatanta sai taji yanzu duk da tana jinta kamar akan kaya kada wani ya fito kuma shima tana jin kunyarsa amma yanzu ne hankalinta ya kwanta. Yanzu ne taji nutsuwar kasancewa da namiji-mijinta. Ya dan dago kansa yana karewa fuskarta kallo kamar kada ya barta yace "saura ladan nauyi da na sha" . Tar ta bude idon "gaskiya bani da nauyi" "Ba kiji yadda zuciyata ke bugu bane da na daukeki." Ya dora hannuta daidai kirjinsa ya sake kissing dinta. "Ke dai ba na nauyinki bane, tsabar dadin kasancewa dake ne. Ba don ina jin kunyar Umma ba sai dai a biyoki da kayanki gobe" Kunya tasa ta kasa kallonsa. Ya rungumeta sosai a kirjinsa zukatansu na kara son juna "yau zanyi bacci mai dadi Matar Jikamshi. Ina fata kema zakiyi. Sai gobe idan mun hadu a dakinki"

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});