Chapter 41
Chapter 41
kinji." Matar da tayi masa waya tace "ai wannan Zinayu taga ta kanta. Tun dazu ake kawo kararta." Amatullah tace "Zinayu nace fa ba Zinayu ba". Daga matar har danta sai da suka yi dariya sosai. Asmau ta gaishe shi ya amsa fuskarsa a sake yana kallon Amatullah. Yarinyar ta shiga ransa lokaci guda. Matar ya kallo yace "Hajiya gara kizo ku tafi gida nasan kin kwaso gajiya da yunwa. Munyi waya da Falalu za'a janyo motar gobe. Da kinyi min waya tun kuna hanyar ai da na turo mota daga Jos din." Murmushi tayi "kai babu komai fa. Na tura Bilkisu da Shafiu a siyo musu abinci ne kafin mu tafi." Ta dubi Asmau "kin kira 'yan uwanki kuwa? Ya kamata a san halin da kuke ciki kada suji shiru" Shiru Asmau tayi, to ita wa zata kira bayan yanzu bata da numbar kowa a gidansu. Ta sunkuyar da kanta kasa kawai ta sako karya "babu kudi ne a wayar, amma nasan zasu kira idan suka ji shiru." Hajiya ta dan bata rai "haba ke kuwa, me ya hana tun dazu kiyi min magana da tuni an siyo ko na baki tawa ki kira. Kai taimaka a samo mata kati ta kira gidansu. Wane layi gareki?" Ba karamar kunyar taji ba. Tayi karya sun dauka gaske ne. Duk da dai kudin wayar dama bai wuce flashing ba tace "MTN". Cikin ladabi ya mike zai fita Amatullah ta riko masa riga kamar zatayi kuka "Baba zan bi ka" Wata waya da Asmau ta tabbatar mai tsada ce ya zaro daga aljihunsa ya mika mata "gashi ki rike min yanzu zan dawo" Bata so ba haka ta sake shi ya fita. Kafin ya dawo Bilkisu ta shigo dauke da ledojin take away na abinci. Shima mutumin sai gashi ya dawo ya mikawa Hajiyarsa katin ta bawa Asmau. Na dubu daya da dari biyar ne guda hudu duka matar ta bata. Tayi ta godiya a son ranta daya ma ya isa. Bilkisu ta durkusa har kasa tace "Uncle ina wuni" "Lafiya kalau, ya gajiyar hanya?" Ta amsa masa da lafiya, ya shiga tambayarta kanwarsa dake Jos wadda ta kasance mahaifiya ga Bilkisun. Asmau dai kashe wayarta tayi sai tayi kamar ta saka katin guda daya sannan ta tashi ta koma gefe kamar tana waya don karfin hali harda kwatancen asibitin. Bata san duk abinda take yi Soja na kallonta ba. Mamaki ne ya kama shi da ya fuskanci me take yi. Tana juyowa suka hada ido yayi mata wani irin kallo. Babu shiri ta sauke nata idon ta basar duk da idanunsa sun tsorata ta. Hajiya ta tashi "to mu zamu tafi ni sunana Hajiya Lubabatu wannan jikata ce." Bilkisu na dariya tace "Uncle kuma dan fari da ba'a fadar sunansa" Ya kai hannu zai rankwasheta "Hajiyar tawa kike tsokana ko. Hajiyata kyaleni da wannan yarinyar zan miki maganinta." Kana ganin Haj Lubabatu kunya take ji bata son wasa da dan nata. Asmau tayi murmushi tace "ni sunana Asmau. Nagode sosai Hajiya Allah Ya saka muku da mafificin alkhairi" "Amin, gobe in sha Allah zamu dawo don nasan dakyar a sallameku. Idan mutan gidan sun zo ki gaishesu" Asmau tace to ta tashi zata rakasu Haj Lubabatu ta dan tsaya ta dauko wayarta daga jaka ta mikawa Bilkisu "bani numbarki saboda kira ko da akwai wani abu." Duk da ta gode da taimakon da matar nan tayi mata amma bata so alakar tayi tsaho. So take yi ta koma gida asirinta a rufe. Yanzu da Amatullah babu lafiya dai bazata iya tafiya ba don bata san yaya zasu tarbeta ba, bai kamata taje musu da lalurar 'yar da suka so a zubar da cikinta ba. Number kawai ta kirkira da ka ta karanto Bilkisu ta kwafa a wayar Hajiya. Hajiya sai sake cewa tayi "yauwa to kirata sai ta samu tawa numbar a wayarta ko." Ji tayi cikinta ya murda kada asirinta ya tono. Sa'arta daya ta kashe wayar tace "wayar ta mutu yanzu amma zan saka chaji idan an kawo wuta" Haj Lubabatu tayi murmushi "to babu komai. Ga abinci nan ki tabbatar kin bata yanzu. Safinatu Allah Ya baki lafiya kinji". Daga haka Haj Lubabatu ta fita Asmau na binta da sakon addua. Shima dan nata zai fita Amatullah ta dage shi zai bata abinci ba Umminta ba. Da murmushi a fuskarsa yace mata yanzu zai dawo ba nisa zaiyi ba. Yana dago kai Asmau ya gani tana kallonsa don tabbatar da abinda yace. Wannan karon murmushin da yayi mata mai nuni da ta kiyayi dawowarsa sannan ya fita. Ai kuwa ta hau Amatullah da fada akan me zata ce ya bata abinci. Yarinya ta bare baki tana kuka, takaici duk ya ishi Asmau don ta tabbatar zai dawo tunda ya sake barin wayarsa. ***** Har bakin mota ya raka su Hajiya tana tambayarsa yaushe zai tafi gida yace yana son lallaba yarinyar nan ne saboda kada tayiwa mamanta rigima. Haj Lubabatu tace "Allah Sarki ai nima ta bani tausayi. Karshenta tana yarinya sosai uban ya rasu shiyasa ta damu da ganinsa yanzu. Nasan dole hakan ya rinka dagawa babarta hankali." "Nima haka kawai naji ta shiga raina Hajiya" Da alamun tausayi a fuskarta tace "ai na sani, kai da son yara kuma. Bari mu wuce sai ka dawo" Bai bar wurin ba har sai da motar ta fita daga gate din asibitin sannan ya koma ciki. Hankalinsa sam bai kwanta da Asmau ba. Yana tunanin ko dai irin matan nan ne masu damfara ko kuma tana da sirrin da bata so a sani. ***** Amatullah sai kuka take yi saboda irin fadan da Asmau take yi mata. "Idan baki rufe min baki ba nida ke ne. Haka kawai daga ganin mutum sai ki dage shine babanki. To nan ba aljannah bane kuma na fada miki yana can. Bude bakinki ki karbi abincin...." Sallamarsa ta sake ji cikin muryar da ta gama ganewa yanzu. Amatullah na ganinsa ta matsa daga kusa da Asmau har allurar da ake yi mata karin ruwa ta soketa ta tsala ihu. Kukanta yaji har ransa ya matsa da sauri ya gyara mata ya bi Asmau da harara, ita kuwa ta matsa gefe rai a bace. Rarrashin Amatullah yayi sannan ya bata abincin kamar ba soja ba ya mayar da kansa yaro a gabanta. Ko sau daya bai yiwa Asmau magana ba har sai da Amatullah tayi bacci sannan ya tashi. Wayarsa ya miko mata fuskarsa babu alamun wasa ta dan ja da baya. "Karbi mana, numbarki zaki saka min" Tayi kicin kicin da fuska "Na bawa Hajiya" "Na sani, ina son karba saboda na kira 'yata anjima". "Da ka barshi ma, saurin mantuwa gareta kana fita zata mantaka" Ya dan daga gira "ke kadai kike son faruwar hakan banda ni da ita. Nasan bazata manta ni ba." Duk da haka Asmau taki karbar wayar tana adduar ya fita kawai. Tunda an biya musu kudin asibitin ba yau ta fara ba, guduwa zatayi idan dare yayi. Ya tsareta da ido "na fa san ba numbar daidai kika bawa Hajiya ba. Kuma nasan baki kira kowa ba dazu. So ki bani numbar tun girma da arziki kafin na fara bincike a kanki." Duk da ta tsorata harararsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103