Chapter 56
Chapter 56
ba don yana ganin mutuncin Qasim din ba tun ranar da ya gansu da Asmau da a lokacin zai fada masa. "Yarinya dake duk kin rikita min lissafi. Amma zan rama ne, sai kin shigo gidanki" "Nima fa ka rikita min" "Me kika ce?" Zancen zuci ne ya fito fili tayi saurin toshe bakinta. Ta rasa inda zata sa kanta don kunya. Tana ji yana mata dariya don yasan bata so yaji abinda ta fada ba. "I love you Matar Jikamshi. Nasan bazan kara samun nutsuwa ba idan ba aurenki nayi ba. Na riga na fadawa Hajiya amsarki nake jira a fadawa iyayena maza. Idan kika zabi Qasim zan tayar da yaki a zuciyarki" Wani dadi ne taji yana ratsata. Ashe tana da rabon samun farinciki a rayuwarta. Ita ma tana son shi kuma ta shiryawa duk wani nau'i na gori da zai iya zuwa daga danginsa. Abinda ake gudu ya riga ya faru sai dai a kiyayi gaba. " 'yarka da Yassar ma bazasu barni ba idan na zabi wani ba kai ba. Da ka tashi sai ka hada da zuciyata data Amatullah kuma harda ta kanina." Da tasan irin yadda yake ji a ransa da ta rage yi masa magana ko don ta sassauta masa. Ajiyar zuciya yayi har tana jin sautin "Say you love me please" ya fada cikin sanyin murya. Yau daya zata sakaya kunyarta ta farantawa mai faranta mata "I do love you _Jikamshina_" Kafin ya kara magana ta kashe wayar gabadaya don tasan zai sake kira. Kwanciya tayi akan gado tana juyi ita kadai zuciyarta kamar an wanke mata. Shi kuwa rike yake da wayar a hannu yana murmushi. Hmmm bari dai ace an daura musu aure. Ranar Asmau zata san tana da masoyi. Zaiyi iya kokarinsa wurin nuna mata soyayya da cewar itama har yanzu tana da darajarta a cikin mata. Abinda ya wuce a baya sai ayi ta addua da fatan Allah Ya yafewa musulmi kurakuransu. ***** Tana ta maimaita hirarsu a kwakwalwarta tana dariya Amatullah ta shigo "Ummina Umma tana kiyanki" Ai da sauri ta sauko daga kan gadon. Shaf ta manta Umma tace tana son ganinta. Saurin da take yi yasa Amatullah tace "Ummi guduwa zamuyi ne? Me nene akan gadon?" Asmau tayiwa kanta dariya sannan ta dauki Amatullah tana juyi da ita. Soyayyar Jikamshi ta zame mata wani bangare mai mahimmanci a rayuwarta. Tana juyin tana dariya. Amatullah tana tayata duk da bata san dalilin murnar Ummin ta ba "Ummi abin dadi ne ya fayu?" "Shine zai faru in sha Allah Ama, muma Allah zai bamu rayuwa mai tsafta kamar kowa" "In ce Alhamdulillah?" Amatullah ta tambaya "Fadi kinji Aman Ummi" Sai da ta gama murnarta ta kama hannun Amatullah suka fito. A falo ta barta ta karasa dakin Hajjo. Kafin ta shiga taji muryar Anti Bintu tana magana sama sama da ji kasan ranta a bace yake "Yaya Bara wallahi Asmau tana son Ishaq. Don ta fada miki zata sallamesu duk su biyun kawaici ne kawai. Ita a tunaninta bata da wata kimar da namiji zai aureta. Don Allah kada ku shiga tsakaninsu. Hajjo kiyi mata magana " Hajjo tace "Bintu nima ba wai naki Ishaq bane. Ki tuna wacece Asmau, tana da tabon da babu ruwan da zai wanke shi duk duniya. Qasim da iyayensa sun san komai game da ita kuma dazu muke ji ashe saboda ita yaki aure tuntuni wai kada kishiya tayi mata gori ko habaici" Anti Bintu tace "to duk abinda yayi ai ba wai sunyi da ita zata aure shi bane. A yadda na kula da irin son da Ishaq yake mata ba zai hakura kai tsaye ba." Umma kanta tasan wanda Asmau take so amma bazata iya yiwa Alh Adamu musu ba kamar yadda shima yaji nauyin Mal Musa. Idan ta biyewa Bintu jan zancen kawai za'ayi ta yi azo zumunci ya sami rauni. "Bintu don Allah ki bar zancen nan. Komai ya kure tunda ranar lahadu zasu zo kawo kudi. Itama sai tayi hakuri ta karbi kaddara" A fusace Anti Bintu ta mike "ni bazan zuba ido ina kallo a cuci yarinyar nan ba. Ba kwa tunanin kada *abinda ake gudu* ya sake faruwa? Don kaddara ta fada mata shikenan kuma bata da damar zabar wanda take so" "Abinda ake gudu ya riga ya faru kumq shine yasa dole duk muyi hakuri. Kina jin da hakan bata faru da rayuwarta ba zan amince da auren nan ne? Yanzu kuwa bamu da bakin magana tunda mu za'a taimakawa. Ki dena bata bakinki akan maganar nan. An gama yanke shawara tun dazu" Hajjo ta rasa yadda zatayi da su biyun. Kowacce ta kafe har suna neman yin fada "don Allah kuyi hakuri. Bintu kece karama, mu taru kawai mu tayata addua." Hawayene kamar an kunna famfo yake saukowa daga idanun Asmau. Dama shiyasa Qasim yace ta jira zuwan lahadi? Yanzu shikenan tun ba'aje ko'ina ba an datse mata samun farinciki daga wurin Jikamshi. Duk maganar su Umma kuma gaskiya suke fada. Ita din tana da tabo a rayuwarta. Wannan yasa a komai shawararta zata zamo ta karshe. Iyaye zasuyi ta ganin kamar komai suka yanke shine alkhairi gareta. A sanyaye ta shiga dakin ta zauna a kasa. "Umma indai auren Qasim kuke gani shi yafi dacewa dani na amince" Anti Bintu ta taso ta tayar da ita tsaye. "Asmau wace irin magana ce wannan. Ishaq kike so kuma na shaida yana matukar sonki. In Allah Ya yarda shine mijinki" Umma taji tausayin Asmau har ranta amma yadda abin yazo musu ne basu da yadda zasuyi "Bintu na dauka mun gama maganar Ishaq dinnan" "Yaya Bara'atu bazan bar maganar ba sai naji daga bakin Ishaq ko shi din ya hakura" Cikin kuka Asmau tace "Anti Bintu ki bar maganar kawai. Allah Yasa hakan shine mafi alkhairi" Tashi tayi ta fita jikinta duk babu kwari. Gobe in Allah Ya yarda zata kira Jikamshi ta bashi hakuri. Bata san wace irin rayuwa kuma zatayi da Qasim ba. Mutumin da bata taba jin sonsa ko kadan a ranta ba. ABINDA AKE GUDU🙆🏽42 Batul Mamman💖 Sallar isha kawai tayi ta kwanta sai kuka. Ganin bazai fishsheta ba yasa ta tashi ta dauro alwala ta soma nafila. Yi take tana kuka tana kara istigfari. Rokon Allah take Ya yafe musu kuskuren da suka aikata wanda har yau yake bibiyar komai na rayuwarsu. Daga nan tayi adduar fatan samun nutsuwa da dukkan wanda Allah Ya kaddara zata aura. Tana sallar Anti Bintu ta shigo da niyyar sake bata baki ta tarar tana sallah. Gefen gado ta samu ta zauna tana jiran ta idar. Tunanin wannan al'amari ne ya rinka damunta. Idan akace *abinda ake gudu*to ba faruwar laifin ake ji ba. Abubuwan da zasu iya biyo bayansa. Asmau ta dade tana ganin tasirin hakan a rayuwarta tun ranar da Abubakar ya rasu. Miji ya rasu ranar daurin aure sannan a sami amarya da ciki. Ai ko a iya nan aka barta ta kafa tarihi a rayuwa wanda duk mutumin da ya santa idan suka hadu sai ya tuna. Ga 'ya ta haifa itama nan gaba tana kara wayo zata iya bukatar jin waye ainihin babanta. Idan kuma marasa tausayi cikin mutane suka goranta mata yanayin haihuwarta ko na sakan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103