Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 81

Chapter 81

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yi dariya, Sabira tace "ai dacewa dai kin gama. Wallahi ki rike baban Amatullah tsakani da Allah. Irin yadda yake sonki kadai ya isa ya nuna miki cewa Allah Yana jin adduar bayinSa. Abinda ya rage kawai ki bi duk wata hanyar kyautata masa yasan cewa shima ya auri mai sonsa." Ummy mai salon tana mata gyara tana nade shawarar da Sabira ke bata itama zata gwada a nata gidan. ***** Ranar da daddare Col. Ishaq ya dawo gida a gajiye saboda ya tsaya karasa wasu ayyuka kafin hutunsa na aure ya fara washegari. Har wani aiki za'a turo shi Liberia ya samu aka bawa wani. Suna magana da Mami da ta iso a ranar ne yaji waya. A zatonsa Asmau ce don yau aiki yasha masa kai tun wayar safe bai kara kiranta ba. Da ta kira ma bai ji ba sai daga baya ya gani ya aika mata da text. Bakuwar numba ce ya dauka tare da sallama. Muryar da yaji ko bata fadi sunanta ba bazai taba mantawa da ita ba. Badariyya... Ko aurenta ya mutu ne???? ABINDA AKE GUDU🙆🏽53 Batul Mamman💖 Amsa sallamar tasa tayi suka gaisa a mutunce. Shiru ya biyo baya ya katse shi ta hanyar tambayarta ya maigidanta da danta Nabil. Dan gyaran murya tayi tace "Uhmm Ishaq dama dazu naje yini gida ne aka bani katin bikinka. Ashe aure zakayi babu labari" "Badar kenan, kina gidan mijinki ai bai kamata na kiraki nace zanyi aure ba. Dama Hajiya tace zata aika cards nasan zaki ji labari" Rayuwa kenan, mutumin da suke matukar son juna gashi yanzu akwai katanga mai karfi tsakaninsu. Tayi dan murmushi. Wayar ma sai da ta nemi izinin mijinta dama ta kira saboda kare hakkin aure. Zancen ba'a son ranta akayi auren ba tuni ya wuce da ta sami ciki. "Allah Ya sanya alkhairi na bugu inyi maka dama. Sai dai naji wani labari a gida da ya tada min hankali...." Katseta yayi wayar ta fara isarsa. Abokai da mutanen da bai ba sani ba duk sun ishe shi da irin wannan maganar. Ga kiran Asmau yana ta shiga call waiting. "Cewa Asmau tana da 'yar da ta haifa babu aure ko? Haka ne abu daya kawai zakiyi min shine adduar da kika yi ta Allah Ya sanya alkhairi ki cigaba da yi" Maganarsa batayi mata dadi ba "idan saboda rashin haihuwa ne don Allah ka nemi wata mai 'ya'yan. Me zakayi da wadda ta gama yawonta a gari?" Runtse ido yayi ransa na kara baci. Haka ce zata yi ta faruwa kenan ko bayan aurensu. Albakarcin zaman tare da son da yayi mata a baya ya hana shi fada mata maganar da zata dade tana mata ciwo a rai. "Kema kinsan bazanyi aure irin wannan ba. Ina son Asmau da zuciya daya. Anyway nagode da wayar taki. Ki gaida mijinki" Ya katse wayar Mami tace "kayi hakuri Yaya. Nasan bazai wuce irin maganar da mukayi ba ita ma shi tayi. Sai an sami mai zurfin tunani ne zai nemi jin ainihin labarin Asmau kafin ya yanke muku hukunci." "Gaskiya ne, Allah Ya kyauta. Babu mai iyawa mutane sai Ubangijin da Ya haliccemu. Komai kayi a wurin mutane baka iya ba a wurin wasu." Dakinsa ya tafi ya kira Asmaunsa yana bata hakurin rashin jinsa da tayi. Dayake tasan yana aiki tace babu damuwa. Sunyi hira wadda duk akan abinda ya shafi biki ce sannan ta kwanta. ***** Ranar Jumaa gidan Umma tun safe ya cika da jama'a duk da a katin an rubuta ba a gidan za'ayi kamun ba. Mutane sun rasa daga inda wasu ma suke zuwa. Abin mamaki sai ga Sagira matar Rabe da 'ya'yansu matan. Duk ta yamushe rayuwar kauye babu dadi. Umma batayi zaton zasu zo ba ganin da Asmau ta dawo an aika musu. Hajjo ce ma ta hana Asmaun zuwa Dakasoyen ta gaishe da Kawu Raben saboda shima ya dauke musu kafa. Gashi dai shine da laifi amma yafi kowa fushi. Su Anti Lami da Yaya Abu duk sun iso da safe da yaransu har na gidan miji. Abu yayi kyau ko babu komai dai dangi ba'a canza su. Lalle aka zauna yi mata ja da baki wanda aka bata lokaci wurin yinsa. Tasha zama kuwa don 'yan uwanta sun dage bazata cire da wuri ba sai ya fito sosai yadda za'a jima ana cin amarci. Ana idar da sallar jumaa aka fara wanka don gidan Umma, Mama da na Jafar duk babu masaka tsinke. Itama Asmau kafin a kira la'asar tayi wankanta mai kwalliya Najah tazo ya fara aikinta. Fuska ta dauka don Naja ba daga nan ba. Kwalliyar ta nutsuwa ce ba'ayi mugun fentin nan na foundation ba da fuskar mutum take canzawa gabadayanta. Ana gamawa ta tashi tayi sallah aka sake gyarawa sannan ta saka kaya. Idan ka ganta a lokacin bazaka ce Asmau mai wankin bandaki bace a asibitin Jos. Tayi kyau ba kadan ba. A lokacin yawancin matan dake gidan sun tafi venue din. Yaya Abu ce ta kira Zubaida akan lallai su taho da amarya da wuri mutane sun soma cika a wurin. Ita har mamaki take yi wasu daga ina suka zo. Wata mota ango Ishaq ya turo mai kyau ta daukar amarya zuwa wurin biki. Da suka isa ita da Walida da Zulaiha ne a motar. Safiyya tazo tace ta zauna domin ango yana hanya sai ya iso zata fito. Ta saki wani murmushin jindadi bayan Safiyya ta tafi. Zulaiha ta ce "Hmm Asmau amare na dan kuka rana irin ta yau sai fara'a kike yi." Allah Yasa dreban motar ya fita sai AC da aka ware musu. Walida tace "baki ga komai ba ita da Col. Ishaq nasu salon daban yake" Asmau tayi fari da ido kawai tana murmushi. Motar tasu mai tint ce ta waje ba'a ganinsu sun jiyo kida daga wurin bikin yana tashi ga mata suna ta shige da fice. Wurin cike yake da sojoji masu gadi. Da farko ma taron ba'ayi niyar yi da maza ba. Sai Mami ta roka akan cewa ango zai zo da abokansa suyi hoto da amarya ya tafi. Shima da kyar ya yarda da zuwan. Shemau ce ta fada mata kalar kayan da amarya zata saka suka yi gaggawar nemawa ango wanda zai dace. Bugu zuciyar Asmau ne ya karu da ta hango motar Jikamshinta. Wurin motoci bakwai ne suka shigo tare. Wai bikin da akace babu maza kenan. 'Yan kashe kwarkwarar ido da abokan arziki duk sun biyo shi. Saitin motar da take Dahiru da ya tuko motarsa ya daidaita tasu yadda zasu fito tare. Ya hakimce a baya yana waya. Sai da ya gama ya fito ko'ina ya dauki kamshi. Kofar inda take zaune yaje ya bude suka hada ido. Babu karya ya yarda yana son Matar Jikamshi. Duk abinda kake so kuwa dole kaga kyaunsa. Indai haka ne Jikamshi da Asmau sunyi kyau a yau ranar kamunsu. Wani hadadden lace ne peach a jikinta da ta samu tela yayi mata dinki na gani a fada. Doguwar riga ce amma tayi kyau sosai mai dogon hannu. Dankwalin rigar aka hada da wani yadi mai kyalkyali purple mara turowa akayi mata dauri. Sai tasa mayafi irin yadin aka makale mata shi daga tsakiyar

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});