Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 53

Chapter 53

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da wani ba" "Don Allah kayi hakuri" tace idonta na kawo ruwa. "Ki fada min ni dashi waye ya fara nuna miki so" "Kai ne" ta amsa masa jiki a sanyaye. Bata son bata masa rai ko kadan saboda yadda take sonsa. "Alhamdulillah, da ya rigani zan ci girma na bar masa ke don bazan iya tarayya da wani akanki ba. Ina da kishi mai zafi wanda ban taba sanin kaina dashi ba sai yau. Amma tunda na riga shi sai dai shi ya hakura. Ina sonki kuma bana jin zan iya hakura dake." Shiru tayi tana kallon kasa. Tun bayan rasuwar Abubakar ta cire rai da sake samun soyayyar wani da namiji sai gashi yanzu har mutum biyu ne suke sonta. Mutum biyun da take matukar son daya, dayan kuma take ganin girmansa. Duk su biyun kuma tana jin kunyar nuna musu bata sonsu a yadda take ganin ba karamin darajata suka yi ba da suke sonta da aure. Col Ishaq yana kallo yadda ta shiga rudani. Kamar yadda ya fada mata da ace Qasim ya rigashi to zai hakura ne indai ya tabbatar da gaske yake sonta. A yanzu kuwa yana da yakinin shi Asmau take so kuma ya riga saboda haka yana nan daram sai yaga abinda ya turewa buzu nadi. Shi kishin kara masa so da kaunarta yayi ma. "Kamar kwana nawa kike bukata na baki ki sallame shi" Ji karfin hali ta ayyana a ranta. A fili tace "bangane ba" "Kin gane, karin bayani kike nema dai. Bansan iya matakin da kuka kai ba ke dashi shiyasa zan baki lokaci kuyi rabuwar arziki. Shima don na fahimci kamar yana da halin kirki ne." "Ya kake so nayi? Kaima na fada maka babu zancen aure a raina shima kuma hakan na sanar dashi" "Idan babu zancen aure a ranki kin tanadi yadda zakiyi da soyayyata wadda yanzu ma na fara nuna miki ita. Idan bakiyi wasa ba nan gaba kadan saboda yadda zan rinka yakin neman sonki da kanki zaki ce gobe a daura mana aure" Dariya tayi, shi a komai sai ya saka wasa tace"kai Jikamshi" "Allah kuwa Asmau" shima ya mayar mata da murmushi. "Ni da ban taba cewa ina sonka ba. Amma kana da confidence a kaina" Kansa ya shafa yana kallonta. Baya gajiya da kallon Asmau ko kadan. "Asmau kina sona. Nima ina sonki. So bana bukatar sai kinyi ta maimaitawa da baki. Akwai lokacin da zaki rinka fada da kanki" Ita kam Jikamshi yana bata mamaki. Sai ya fadi magana ya kuma dake abinsa. "Ki shiga ciki bana son kina shakar kurar nan. Kada ki manta da abinda nace. Idan kin sallame shi zan turo iyayena a fara maganar aurenmu" Magana taso yi ya sanya yatsansa akan lebensa alamun tayi shiru. "Idan rokona zakiyi akan Qasim kada ki bata bakinki. Nan da sati biyu idan baki sanar dani yadda kuka yi ba ki zaki ga magabatana sunzo. Ki kula min da kanki da princess dina. Yau duk kin rikita min lissafi na kasa bata kulawa yadda ya kamata" "Ni babu ruwana." "Harda tsakinki. Sai da safe" "Allah Ya bamu alkhairi" Tana kallo ya shiga mota ya zauna sannan itama ta juya. "Matar Jikamshi" Cak ta tsaya amma bata juyo ba sai murmushi da take yi. "I love you" Hannuwa tasa ta rufe fuskarta cike da kunya tayi hanyar gida a kunyace. ****** Daurewa kawai Col. Ishaq yayi har suka karashe hirar cikin wasa. Da ya rage shi kadai yana tuki tunani yake kada iyayen Asmau su bawa Qasim ita saboda sunfi sanin shi sannan abokin Abubakar ne. Saurin kawar da tunanin yayi daga ransa. A zatonsa ya gama soyayya akan Badar sai gashi lokaci guda Asmau ta wargaza masa tunani. Yana zuwa gida dakin Hajiya ya wuce. Bayan sun dan taba hira ya sanar da ita zancen Asmau. Tayi mamaki sosai don bata taba hasko hakan ba. Bilkisu da tayi niyar fada mata kuma ranar tun a hanya yaja mata kunne. Shiru tayi na dan lokaci kafi tace "Kai yanzu kana tunanin sai ka aureta ne kawai zaka iya kyautata rayuwarta da ta Safina?" "Hajiya nifa ba don in kyautata musu kawai nake son aurenta ba. Ina sonta ne tsakani da Allah" Ko kunyar yace yana son mace baiyi a gabanta. Tayi iya kokarinta wurin nuna masa kunyar dan fari amma duk baya biye mata. Yanzu me ya kawo zancen soyayya a gabanta. "Bazan zama irin iyaye marasa karbar kaddara ba musamman da na san komai game da ita. Kai ba yaro bane da zan ce baka san abinda ya kamata ba. Amma ka jira nayi shawara da 'yan uwana dana mahaifinka. Kasan zancen duniya baya buya. Gara su sani tun kafin ayi auren sabo gudun gutsiri tsoma" Murmushi yayi ya nuna mata tsantsar farincikinsa. "Hajiya nagode da kika fahimce ni. Ina fata ko sun nuna rashin amincewa don Allah kada ki hanani aurenta don wallahi bakiji yadda nake jinta a zuciyata ba" Haj Lubabatu ta kawar da kanta gefe a kunyace. Ya cigaba da cewa "idan tayi murmushi ji nake kamar...." "Kai tashi ka bani wuri zancen ya isa haka" ta fada amma kafin ya tashi ita tayi gaba. Dariya yayi dama tsokanarta yaso yi. Sai da ya gama shirin bacci ya dauko wayarsa zai kira Asmau yaga missed calls da bakuwar number har uku. Ya kira numbar ga mamakinsa sai yaji muryar Qasim. Sun sake gaisawa yace ya karbi numbarsa a wurin Yassar ne don su rinka gaisawa. Hira suka dan taba cikin mutunta juna. Suna yin sallama ya kira Asmau. Ta dauka kafin tayi magana yace cikin muryar shagwaba "Matar Jikamshi kin cuce ni" Gyara zama tayi a dan tsorace." Me nayi kuma"? "Wannan dan sandan saurayin naki wallahi yana da mutumci. I feel guilty nace ki rabu dashi gashi har yana min waya." Ta dan murmusa "to ko na barshi kai ka janye" "Ba haka nake nufi ba fa. Kawai dai naji babu dadi ne. Da kin sani wani dan caburus kika nemo wanda zanji kwarin gwiwar yiwa rashin....." ya dan toshe baki "wai shekarunki nawa ne? Kinsan dole na kula da abinda zan fada a gabanki saboda kada na bata yarinya" "Nice ma yarinyar. Shekarata ashirin da takwas fa" "Kai, kai ,kai...kada azo a kamani ina soyayya da 'yar yarinya" Asmau sai dariya take yi tana juyi akan gado, Ainau daga gefe tace "love in Tokyo" Pillow ta jefeta dashi ta cigaba da dariyarta saboda yadda Jikamshi yake mata shagwaba yau "shiyasa nace ka hakura ka janye kawai ka barwa yaro" "Ai baki isa ba yarinya. Bayan duk kin gama kashe min jiki da wadannan idanuwan naki. Na dai fada miki ina tausayinsa ne amma bance ki tausaya masa ba. Ki gaggauta sallamarsa kada ya janyo zuciyarki da kirkinsa" "Jikamshi" Sai da ya gyara kwanciya ya amsa mata "mene ne?" "Babu komai, sunan kawai nake son fada" "Shi mai sunan ba kya son shi?" "Ina so" Da sauri ta tashi zaune da ta gane abinda ta fada. Ta rasa dalilin da yasa idan tana tare dashi take manta komai tayi ta sakin baki. Ko dai ta fara zama irinsa ne??? ***** Washegari Malam Musa ya zaunar da iyalinsa ya fada musu cewa nan da sati mai

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});