Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 91

Chapter 91

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

so sosai a jikinki. Kinga sai na rama a nan ba sai munyi nisa ba" Daga nan bai bari ta motsa ba bare ta gudu.... ***** Shi ya fara tashi wurin goma ya kalleta. Bacci take sosai kamar wata 'yar yarinya. Allah Sarki Asmau, duk wata matsalarta ta wuce a wurinsa. Yadda ta iya jajircewa akan aurensa duk da matsalarsa yasa yake jin sonta sosai a ransa. Zaiyi nasa kokarin sosai wurin kyautata mata. Duk wani gata da miji zaiyiwa mace shima zai kokarta. Baya son ko kadan suyi nadamar auren juna. Yadda take tunanin yayi mata alfarma shima hakan yake ji. A hankali ya fita daga dakin don kada motsinsa ya tasheta. Yasan ba karamar gajiya ta tara ba tun kafin a fara bikin. Ga ta biki ga rashin bacin kirki a nasa gidan. Kitchen ya shiga wanda ya cika store din da kayan abinci tun kafin a kawo gara. Sauran kananan abubuwa da mace ke bukata na kitchen ya bawa Safiyya kanwarsa kudi yace ta tabbatar idan an gama jere ta sayo su ta ajiye. Ai kuwa ta siyo su kwai, kayan miya da 'yan tarkacen da ba'a rasa ba duk ta ajiye a inda ya kamata tun jiya. Su Shemau ta tarar suna karasa aiki lokacin da ta kawo kayan. Ya duba ya sami abubuwan da yake bukata ya fito dasu. Addua yake kada Asmau ta tashi sai ya gama komai. Ya dade da koyon girki a wajen Hajiyarsu. Ko ta koreshi daga kitchen sai ya dawo yace tayata zaiyi. Ita tana haka saboda namiji ne kuma dan fari shi kuwa ko a jikinsa. Har babansu yace ta rabu dashi. Ga amfanin koyon girkin yazo. Da Asmau idonta biyu kila tayi masa dariya ko kuma ta hana shi. Wata hira da suka taba yi ta fada masa abinda tafi son ci da safe ya tuna. A lokacin dama tunaninsa yayi mata shi ranar farkon aurensu. Tana can tana baccin gajiya ya da fa masu indomie da attaruhu, albasa da caras yadda tace tana so. Ya dafa kwai ya yanka a gefe da cucumber sannan ya hada musu tea a cups ya zuba a tray. Shi kadai yake murmushi har yaje dakin. Tana nan inda ya barta. Ajiye tray din yayi ya zauna kusa da ita ya janyota jikinsa. Ta bude ido kenan zata yi magana ta kula da agogo. Shadaya harda rabi. Ta zaro ido tana kokarin tashi."Subhanallah haka nayi ta bacci, ka dade da tashi ko? Ko breakfast ban hada maka ba. Bansan wane irin bacci nayi ba yau" Duk ta damu ko kadan ba haka taso ba. Amare da take jin labari sun riga mazansu tashi sun hada musu abinci ita gashi rana ta fito tana bacci. Zaunar da ita ya sake yi "duk kin wani tada hankali kamar wadda tayi laifi. Bacci kuma ai dole kiyi, ko kin manta baki sami damar yi ba jiya" Asmau ta ji kunya, duk inda zai dauko maganar da zata kunyatata ya iya. Ta sake yunkurin tashi sai ta ga tray din abincin har tiriri yake, sai lokacin ta farga da kamshin dake tashi taji cikinta na kukan yunwa. Idonta ne ya ciko da kwalla da ta ga yadda ya tsara komai kamar ba hirarsu ne sati daya kafin biki. Fadawa tayi jikinsa "Jikamshina nagode" tana jin wani sabon sonsa a ranta. Wannan farincikin yake son gani daga gareta kuma ya samu. "Kije kiyi brush kada yayi sanyi. Idan kuma godiyar zaki yi zan baki goyon baya. Kinsan ana son yawan godiya" yana magana yana daga mata gira ta tashi da sauri tana dariya ta shige toilet. Kafin ta fito wayarsa ta soma kara ya dauka ganin maigadinsa ne. "Sir baki ne suka zo har mota biyu. Na bude musu?" Col. Ishaq yaji kamar ya fita ya kori ko su waye. Shi fa yana mamakin wannan dabiar ta hausanmu. Ayi komai na hidimar biki da mace wai amma gari na wayewa sai su zo ganin amarya. Ko ganin gulma kamar yadda yake kiran ziyarar. Ai dai a bari ko azahar ayi. Amma yanzu ko shabiyu batayi ba ace an zo gidan sababbin aure ai ba'a so zaman lafiya ba. Bare a lokaci irin wannan da ya gama tsara yadda zai kasance idan sunci abinci da amaryarsa. "Ina fata ba a gabansu ka kirani ba" "Eh Sir, ina daga ciki ne" Rai a bace yace "to ka fita kace wayata a kashe take kuma nayi umarni kada ka bude sai da izinina" Ya ajiye wayar da yaji Asmau zata fito. Akan gadon suka ci duk kunyarta ta ajiye a gefe suna bawa juna a baki. Yadda ya kyautata mata itama haka take kokarin yi masa. Shaf ya manta da batun baki sai da Asmau ta fita kitchen zata mayar da kwanukan Hajiya ta kira shi. Ko gaisuwarsa bata amsa ba ta fara fada akan lallai yasa a bude gate ga baki nan 'yan uwansu ne da wasu daga gidansu Asmau duk sun hadu a bakin gate maigadi yaki budewa. Ba'a son ransa ba yace to tare da bata hakuri. Da Asmau ta dawo tace masa zata je tayi wanka. "Nazo muyi tare?" Ta fito da manyan idanunta "rufa min asiri" "Nine sirrin naki Matar Jikamshi. Bakya bukatar rufe min komai. Kije kiyi amma idan kika dade zaki ganni" Ta fita shi kuma yayi waje daga shi sai dogon wando da jallabiya. Bazai fada mata da baki ba yasan rudewa zatayi ta fara komaina gurguje. Abinda baya so kenan shiyasa ya kyaleta ma tayi wankan. Bayan ya bawa maigadi umarnin ya bude musu ya bude kofar falon ya koma ciki. 'Yan uwansu ne na Jikamshi masu komawa a ranar sai na Asmau 'yan Wushishi. Sake fitowa yayi da bayan sun shigo an fara hayaniya ana ta gaisawa. Wasu suna ina amarya take. Ai suna ganinsa har 'yan uwan nasa kunya sosai ta kamasu domin kana ganinsa zaka san bai dade da tashi ba. Yayi murmushin keta ganin duk sun daburce da ganinsa a haka suka gaisa, manyan cikinsu ma sunji kunya. A ransa yace gobe ma ku sake zuwa kallon kwakwaf. Basarwa yayi yace "tana shiryawa ne bari na kirowata" Kafin ya karasa shigewa korido din ya soma jin suna kuskus ana cewa dama ba yanzu suka zo ba sai anjima. Dakin Asmau ya shiga tana kokarin zuge zip din riga. Tana ganinsa ta juya kada ya ga bayan ya shigo ya rungumeta ya zuge mata zip din yace "sarkin kunya kin gama shiryawa, muna da baki a falo" A rude tace "baki kuma, yaushe suka zo. Ban duba kitchen din ba ko akwai waniz , , zaki abu mai sanyi da zamu bawa baki" tunanin yadda zatayi ta soma. Dama ransa ya baci da zuwan bakin ganinta yanzu ya sa ya dan manta. Gashi yanzu duk an ruda masa mata. Ita ma bata gamawa sanin kan gidan ba an zo mata mutane sunfi goma. "Shiyasa tun dazu da suka zo nace kada a bude gate din" "Sun dade da zuwa? Meyasa kace kada a bude yanzu sai ace laifina ne" A zatonsa zata ji dadin yadda yayi bai san mu mata mun saba da irin wannan bakin na bayan kai amarya ba. Idan ba'ayi sa'a ba ma kawayenta ke

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});