Chapter 17
Chapter 17
bakinta don bata san maganar ta fito ba. Shi kuwa dariya ta bashi ma. Bata saba ganinsa yana nishadi kamar haka ba, sai take ganinsa kamar ba wanda ta sani ba. Duk ya canza. Ya kula duk bata da nutsuwa kuma shima dai bazai sake ba a falon gidansu inda ake ta shige da fice. "Ki koma gida anjima zan zo in sha Allah." Kanta a kasa tace to ta juya zata fita. A takure take dama kamar wadda tayiwa sarki karya. "Asmy..." sabon sunan da ya rada mata taji ya fada. A hankali ta juyo amma bata iya daga kai ta kalle shi ba. A tsaye yake shima "dama fuskarki nake son kara gani. Sai na shigo anjima". Bata iya yiwa kowa sallama ba ta fita da sauri. Ko wayarta bata nema ba wadda tana kallo yasa a aljihun wandonsa. Har taje gida ta kasa gaskata maganganun Abubakar. Wai ita ya kira Mrs A.A Matawalle. Murmushi ta saki saboda sunan yayi dadi. Kai tsaye daki ta shige ta tarar Shema'u ta dawo daga makaranta. Itama murna ta fara taya kanwarta ta sannan tace ina sabuwar wayar ta gani. Asmau ta danyi yake "Yaya Abubakar ne ya karba zai duba amma yace zai kawo min anjima." Shema'u tace to Allah Ya kaimu. Daga nan hira suka cigaba wadda duk akan shirye shiryen bikin Shema'un ne. Sai bayan sallar Isha Abubakar yazo. Dayake ranar babu karatun dare saboda Malam Hadi ya danyi tafiya. A falo ya same su suna cin tuwo ita da Aina'u a plate daya. Yana sallama Asmau ta tsame hannunta don yadda take jin kunyarsa yanzu ko kallon inda yake ta kasa. Binta yayi da ido yana murmushi har ta shige kitchen. Shema'u da Yassar suka yi masa sannu da zuwa ya tambayi ina Umma. Yassar ne ya kirata suka gaisa tana tambayarsa ya Ebonyi. Sun sha hira har yake fada mata bazai koma ba sai bayan bikin Shema'u. Makarantar secondary aka tura shi service kuma sun yi hutu. Asmau tunda ta shiga kitchen ta kasa fitowa. Yana ta kallon hanya yaji shiru. Gajiya yayi ya tashi yayi musu sallama sannan yace Shema'u tazo zaiyu mata magana. Wurin da Umma ke ajiye mota suka tsaya ya dan shafi fuska "nifa wurin Asmau nazo amma na kasa sanarwa Umma kamar yadda nayi niyya tun a gida." Dariya Shemau tayi cike da jindadi "Allah Yayi lokaci yayi. Mun dade muna jiran lokacin nan da zaku dena satar kallon juna ayi kowa ya sani". Ya dan daure fuska yana harararta "Ke nifa yayanki ne kike min dariya. Amma seriously ke da waye 'yan sa idon?" "Tabdi, Yaya Abubakar kowa fa ya gano ka tuntuni. Su Umma ma duk jira suke hasashensu ya zama gaskiya. Yanzu ma da ka kalli kofar kitchen sai Umma tayi murmushi." Kunya yaji sosai "kice kawai na dena zuwa gidan nan. Ga wayarta ki bata, ni yanzu kunyar ganin Umma nake yi ma." Shema'u dai dariya tayi ta masa da tsokana har ya tafi. Tana shiga gida ta bawa Asmau wayarta sannan ta sanar da Umma yadda suka yi da shi. Kasa boye farincikinta tayi saboda sun jima suna jiran hakan ita da Mama. Asmau ta kira ta bata izinin zata iya tsayawa da Abubakar tunda ko yanzu za'a iya aurar da ita a shekara shabakwai. Sannan ta ja mata kunne sosai game da kare mutumci duk da dai ta yaba da tarbiyar Abubakar. Asmau kamar ta shige kasa don kunya wai ita Umma ke yiwa nasihar fara zance. Bayan ta koma daki missed calls ta gani da numba an sa _Mine_. Duk tunaninta tasan batayi saving numbar kowa da wannan sunan ba. Tana kallon wayar aka sake bugowa ta dauka. Muryarsa taji mai dadin sauraro musamman idan yana karatu. Ya ce "My Asmy" A hankali tayi magana "Yaya Abubakar?" "Sunan da kika gani kenan da aka kira ki?" "A'a" ta amsa tana dan murmushi "Wane suna kika gani?" Lallai ma Yaya Abubakar so yake ta fadi sunan da ta gani yaji dadin cewa tayi rashin kunya. Shiru tayi har kusan minti biyu babu wanda yayi magana. Ya numfasa har tana jin sautin "idan na dameki ne bari na ajiye wayar." Da sauri ta ce ba damunta yayi ba. "To ki fadi sunan da kika gani don shi kadai zan rinka amsawa daga gareki idan har kin yarda nan gaba kadan ki zama matata." Wani irin dadi taji yana ratsa zuciyarta. Bata taba sanin soyayya ba sai akansa. Muryarta kamar mai rada yaji ta ja kalmar "Mine" Ji yayi kamar yafi kowa nishadi a wannan lokacin. Bai ja ta da hira sosai ba sai dai duk abinda ya fada mai tsayawa ne a rai. Da suka yi sallama wata hirarsu ta tuna da Walida inda take ce mata babu wanda ya kai ustazai wadanda suka koshi da boko kuma suka dauki koyarwar Al'Qurani da hadisi a matsayin jagoran rayuwarsu iya soyayya. Kafin tayi bacci yayi mata text ya kai biyar duk na kalamai masu ratsa zuciya. Cikin dan lokaci kowa ya san soyayyar Abubakar da Asmau. Mama ta kara nuna mata so tamkar 'yar cikinta. Duka gidajen biyu babu wanda alakarsu bata burge shi. Ya zauna a Kano har akayi bikin Shema'u da sati daya sannan ya koma Ebonyi. Waya kam shi da Asmau kullum ne sai sunyi. Soyayya suke yi mai tsafta saboda dukkansu sun fito daga gidan tarbiya. A can garin ma shine Amir din Muslim Students' Society (MSS) dinsu suna kiransa Young Ustaz. ***** Admission ya fito Asmau bata sami medicine ba sai pharmacy. Abubakar yace ta karba ta godewa Allah domin zabinSa a kodayaushe shine alkhairi. Haka kowa tayi registaration dinta tayi sa'a Walida ma shi aka bata saboda haka kullum suna tare. Yana dawowa Abdulhalim yayi aure Mama tace gidan nata duk ya daye saura su biyu shi da Umar. Shima aiki yake nema ido rufe saboda a fara maganar aurensa da Asmau. Baba yayi musu gini duk su uku mazan a wuri daya gate ne ya rabasu. Amma yace daga nan kuma mutum ya nemi aiki ko sana'a sannan a fara batun aure. Itama Umma a nata bangaren sai siyan kaya take tana ajiyewa kada biki ya tashi batayi tanadi sosai ba. Da bikin Shema'u dangin babansu na nesa sune suka bata gudummawa. Hajjo da 'ya'yanta da suke makusantansu babu abinda sukayi mata. Daurin aure dai Alh Rabe ne ya karbi sadaki...su Rabe an zama Alhaji sakamakon kujerar Makkah da shugabar kamfanin da yake aiki Haj Rufaida ta biya masa. Shiyasa wannan karon Umma ta kara dagewa don fita kunya. ABINDA AKE GUDU🙆🏽9 Batul Mamman💖 Mal Yahaya dakansa ya rinka yiwa Hajjo fada amma ta takura Bara'atu. Lokacin Shua'aibu yaje gyaran gidan da zasu koma a Zaria. Yana dawowa ya tarar da mahaifinsa a kwance shine suka kaishi asibiti shi da Rabe. Likita ya duba shi aka ce malaria ke damunsa. Magunguna kawai aka rubuta suka dawo gida. A tsakar gida Hajjo tayiwa mijinta shimfida suka kwantar dashi yana shan iska shi kuma Shu'aibu ya tafi siyan magani. Fitarsa keda wuya Rabe ya karasa kusa da Hajjo yace "Hajjo likitan fa yace basu gane kan cutar dake damun Baba ba. Idan bakiyi wani abu ba duk sai mayun nan sun cinye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103