Chapter 92
Chapter 92
zuwa jin ya aka kwana. Amarya mai bakin aku tayi ta bayani dalla dalla. Gani yayi duk ta damu da bakin da bata san ko su waye ba yace "nayi miki gwaninta shine kike bata rai. To kije wurinsu ina daki idan kun gama" Asmau taji wani iri. Maganarsa kadai ta sanar da ita ransa ya baci. Ya juya zai fita ta riko hannunsa "kayi hakuri Jikamshina" Ya danyi murmushi "babu komai akwai lemo a fridge kuma ina jin da cake sai ki basu" Fita yayi ya barta ta rasa yadda zatayi. Gashi yayi fushi sannan ga bakin da idan bata je ba zasu tafi da ita a baki. Haka ta yafa mayafi ta fita wurinsu. Su a takure ango ya basu kunya ita kuma ta kasa sakin jiki saboda kunyar an shanyasu a waje ga Jikamshinta yana fushi. Basu dade ba suka tafi ko irin leken gidan amarya basuyi ba tunda ansan yana gidan. Suna tafiya ta koma dakinta ta canja kays zuwa wasu riga da siket da suka fiddo da jikinta sosai. Tasha turare da kwalliya ta tafi bawa angonta hakuri. Zaune ta same shi akan wata doguwar kujera ta dakin ya gama shiryawa yana waya da alama Mami ce. Tunda Asmau ta shigo ya ganta da kwalliya da kamshin da take zubawa ya nemi fushinsa ya rasa. Hannu ya mika mata alamun ta karaso. Tana ji ya sallami Mami ya dubeta "apology accepted" Tace tana jindadi "tun kafin na bada hakurin" "Ganinki ya kori fushin amma ki sani bazan yarda da bakin nan ba. Sati biyu kawai aka bani a wurin aiki. Bazanyi sharing dinsu da bakin nan ba. Anjima zamu hada kaya gobe in sha Allah zamu je Yankari Game Reserve" Ta sunkuyar da kai ta kara bashi hakuri sannan tace "ko naje na fara hada kayan yanzu?" Ya ja hancinta "yanzu kuma ai lokacina ne ranki ya dade" ABINDA AKE GUDU🙆🏽57 Batul Mamman💖 Washegari garau ta tashi kamar ba ita ba. Sai a lokacin hankalin Col. Ishaq ya kwanta ya lallai wani satin ta huta har ta kara samun lafiya. Sun cigaba da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ya karbo mata form din Jamb suka cike tare sai jiran lokacin jarabawa. Bayan sati daya Walida ta kirata ta sanar da ita zata kawo mata ziyara da neman shawara. Dadi ya kama Asmau ta shiga dakin Jikamshinta ta fada masa ta same shi ya mike akan gado yana baccin gajiya ko uniform dinsa bai iya cirewa ba. Daga taje ta zuba masa abinci kafin yayi wanka sai bacci. Asmau ta tsaya tana kallonsa cike da tausayi. Babu abinda baya wadata su dashi ita da Amatullah. Ji tayi a ranta inama zata haifa masa da ko 'ya mai kama dashi. Yana da tsayi da girma kana ganinsa kaga soja. Bata gajiya da kallon mijinta abin alfaharinta, komai nasa yayi mata. Fuskarsa kullum bata rabo da yi mata murmushi, idan kaga ya hade rai to yana wurin aiki ne. Amma duk da haka mutanen dake karkashinsa suna yabonsa da kirki da iya jan mutane a jiki. Col. Ishaq mutum ne mai jama'a, a irin zamansu da kyautatawarsa gareta haihuwa ce kadai tasan zata yi ta faranta masa rai sosai. Hawaye taji ya zubo mata tayi saurin sharewa kada ya gani hankalinsa ya tashi. Wayarta ta saita a kansa ta kashe flash light ta fara daukarsa a hoto. Sai da ta gaji don kanta ta juya zata fita taji ya tade mata kafa ta fado a kansa. Da farko ta tsorata sai kuma ta fasa bayan taji yadda ya riketa a jikinsa. Ta dube shi idanunsa har lokacin da alamar bacci ya sake kwantar da kansa ya rufe ido. Tace "Tun yaushe ka tashi?" Bai bude idon ba yace "tun da kika shigo kina kare min kallo mana. Ko nayi miki kyau ne" Tayi murmushi tana shafa sajensa "kullum ma kyau kake min Jikamshina. Musamman idan kasa kayan nan kamar kada ka fita" Yaji dadin abinda ta fada. Kamar yadda mata ke son a yabe su haka maza suke so suma matansu su yaba musu. Wayarta ya karba ya daukesu selfie suna yiwa juna murmushi. Bayan ya dauka yace "Matar Jikamshi kinyi kuka ko" Asmau tayi saurin kai hannunta wurin idonta zata goge sauran hawayen da tayi lokacin da take tsaye yana bacci. "Abu ne ya shigar min ido fa" "Uhmm uhm Matar Jikamshi kada mu fara yiwa juna karya. Na kuma san halinki da saurin kuka. Fada min me kika saka a ranki." A nutse yake kallonta ta sake shige masa tana jin wani hawayen na kokarin zuba. "Kawai ina tunanin abinda zanyi maka ne na faranta maka rai sosai. Kayi min komai a rayuwa har bana jin akwai matar da tayi dacen abokin rayuwa kamar ni. Har kunyarka nakan ji a raina in ga kamar bana yi maka abin da ya dace" "Babu abinda nake so daga gareki da baki bani ba. Kin bani Asmau da duk abinda Asmau ta mallaka. Adduata kullum Allah Ya bamu zaman lafiya mai dorewa." Ta amsa da amin hawayen da take boyewa suka gangaro. Ba su suka fito ba sai da Amatullah ta dawo daga islamiyya lokacin an kusa kiran magariba. ***** Bayan ya tafi aiki da safe sannan Amatullah ta tafi makaranta ta gama gyaran gida ta dora abinci. Walida na son alala shiyasa da tayiwa Jikamshi nashi abincin ta gyara wake tayi musu alala mai cike da dafaffen kwai da ta yanka kanana da kayan hadi. Kafin ta iso ta gama komai da zatayi har da juice din kwakwa da ayaba. Sai da tayi wanka Walida ta iso suka zauna hira. A hirar ne suna cin abinci Walida take neman shawararta akan abokin Col. Ishaq wanda shina soja ne kuma likita a nan asibitin barrack dinsu. Sunansa Hussaini, yana da mace daya da yara hudu. Asmau dadi ya kamata tace "ashe dai da gaske yake, Walida ki amince ni dai a dan haduwarmu a fuskanci mutumin kirki ne kuma mai addini. Yazo gidannan tare da Jikamshina yayi min tambayoyi a kanki. Dama shiru nayi sai kinji daga bakinsa." Walida tace "wato ko kunyata ba kya ji kike cewa Jikamshinki" "Don ma kada kice abin yayi yawa ne na tsaya a nan. Kinsan yadda nake ji dashi kuwa. Hmmm Jikamshi mijin Matar Jikamshi" tana magana tana kashewa Walida ido don tsokana. Ai kuwa ta kai mata dundu ta kauce suka saka dariya. Walida tace "to ya batun matarsa? Kinsan yadda muke da Anti bana son harkar kishiya. Ko shekara batayi ba a gidanmu Abba ya saki Mama. Auren shekara tara ya iya yi mata saki uku lokaci guda." Asmau tana tausayin Walida ta wannan fannin. Bata tashi tasan soyayyar mahaifiya ba kamar yadda suka sani ita da nata 'yan uwan. Tsakaninta da babarta sai anyi hutu. Shima babanta baya bari ta dade "Walida ba duka aka zama daya ba. Munje gidansa suma sun zo mana nan. Ni dai ina ganin kamar tana da kirki gaskiya duk da idan aka ce kishiya yanzu sai tunaninmu ya sauya. Ki dage da adduar neman zabin Allah. Idan mijinki ne sai kiga mun sha biki cikin kwanciyar hankali. Kada ki bari tsoron abinda baki da masaniya akansa ya sakaki ki amincewa da shi. Baki san
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103