Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

lokacin da ya sami attack bashi da wani mataimaki sai ke kadai a wurin. Rashin taimakonsa kuskurene tunda yana cikin mawuyacin hali. Da ace akwai wani namijin to dama bai kamata ki taba shi ba. Komai na addininmu yana da sauki. Duk abinda ya zama lalura wajibi ka taimaki mutum koda kuwa baki sanshi ba. Ku tashi Allah Yayi muku albarka". Shi Abubakar har kunya yaji. Yarinya ta fishi hangen nesa. Can gefe suka koma a cikin falon wurin wasu kananan kujeru da dan tebur a tsakaninsu. Littafin ya karba yace ta dauko text book dinta na P.N Okeke Mama ce ta bisu da kallo har suka zauna sannan ta maida hankalinta ga Umma. "A gaskiya Umma ina yaba miki wurin kokari a tarbiyantar da yaran nan. A zamanin nan da kananan yara sun san meye mace ko namiji amma har a irin wannan yanayin Asmau bata manta da hudubarki ba. Allah Ya kara taimaka mana wurin basu tarbiya. Shiyasa nake jinki kamar kanwata ta jini wallahi." Murmushi kawai Umma tayi. Mama ta cigaba da magana " inama dai yaran nan su hada kansu? Wallahi ba karamin dadi zanji ba. Ji nayi Asmau ta kara shiga raina. Ni daga yau ma ta kwace matsayin auta Umar." Wannan karon dariya Umma tayi. "Anya wannan dan shagwabar zai yarda? Maganarki kuma akan ita da Abubakar ba tun yau ba nima nake sha'awar hakan. Allah Ya zaba mana abinda yafi alkhairi." A can gefe inda suke yin aikin kuwa ko yaya suka hada ido sai su sakarwa juna murmushi. Wannan murmushin sai da ya zame musu jiki. Ko karatun dare suka zo sai Abubakar yayi ta kallon Asmau har sai sun hada ido anyi murmushin nan. Ita yanzu kunyarsa take ji sosai. Shi kuma duk irin basarwar nan tasa da rashin kula mutane indai suka taru suna hira ko a gidan Mama ko gidan Umma to sai yasan yadda yayi Asmau tasa baki. ABINDA AKE GUDU🙆🏽14 Batul Mamman💖 Kwance tashi babu wuya a wurin Allah. Anyi bikin Suwaiba da Sadiya lokaci daya. Asmau kuma ana ta shirin fara WAEC da NECO. Ita kuma Shemau tana aji uku a jami'a sannan ansa bikinta wata hudu masu zuwa. Asmau tayi murna don lokacin ta gama jarabawa. Karatu take yi sosai saboda don cika burinta na zama likita. Har gidan su Abubakar yaje da laptop dinsa yayi mata registration din JAMB. Anan ne ya cike mata medicine a matsayin zabin farko sai pharmacy a zabi na biyu. Duk abinda ya shige mata gaba tana tambayarsa ya koya mata. Gab da fara jarabar tasu ne posting din su Abubakar ya fito an tura shi jihar Ebonyi bautar kasa. Da yaje fadawa Umma yana kula da yadda fuskar Asmau ta nuna rashin jindadi sosai. Shi kuwa hakan yayi masa don yanzu ya tabbatar ba shi kadai ne zuciyarsa ta kamu da sonta ba. Jira yake yi ta kammala makaranta sannan ya fada mata. Watansa biyu da tafiya watarana tana dawowa daga makaranta sun gama practical din food and nutrition yamma tayi sosai wani saurayi ya tareta a hanya. Tunda ta fito daga makaranta bayan sunyi sallama da Walida kawarta yake binta a baya. Tsoro ne ya cika mata zuciya bare da yayi mata sallama ya bukaci ta tsaya. Yana bayyana mata soyayyarsa tace yayi hakuri tana da mijin aure har ansa mata rana. Saurayin ya gamsu ya tafi. Ita kuwa a ranta gani takeyi kamar taci amanar Abubakar ne ma idan ta tsaya da wani duk da bai taba cewa yana sonta ba. Alhamdulillah sun gama jarabawarsu lafiya sai jiran sakamako. Ranar da ta gama tana dawowa gida Umma na kitchen ta kwala mata kira. Ko kayan makaranta bata cire ba taje amsa kiran. Umma na murmushi tace "Asmau yau an gama jarabawa ko? To ki dage da addu'a kamar yadda kullum nake yi muku. Allah Ya bada sa'a Yasa ku gama lafiya." "Amin Ummana". "Kije dakina akan gado duk abinda kika gani naki ne na tayin murnar gama exams. Sauran kyauta sai naga result mai kyau." Dadi ya kama Asmau tana ta godiya ta ruga dakin Umman. Kwalin waya ta gani akan gadon hannunta har yana rawa ta dauka tare da yin ihun murna. Daga kitchen Umma tace "Asmau babu hamdala sai ihu ko? Kin kyauta." Dena ihun tayi ta fara godiya ga Allah sannan ta fito falo wurinsu Jafar. Sun tayata murna Yassar yana rokonta ta rinka bashi yana yin game. Shema'u da Jafar kayansu baya tabuwa. Jafar ya bude kwalin harda sabon sim na mtn. To dama Umma yanzu ta kara samun matsayi don har mota ta siya. Masu abu da abinsu. Duk wanda ta sayawa waya dole yayi sim din mtn. Suna gama murnarsu ta saka hijab ta fadawa Umma zata je ta nunawa Mama. Umma tace "babu inda zaki sai kinyi wanka kin canja kaya. Kin yini da uniform kuma kice dasu zaki fita?" Komawa tayi ciki tayi wanka ta canja kaya ta. Tare da Aina'u da Yassar suka tafi. Umma ta girgiza kai kawai tana dariya. Da sallama ta shiga ganin Nasiba tayi a falon da danta Amir. Asmau ta karasa ta rungume Nasiba tana murna sannan ta karbi Amir. "Tun dazu nazo fa, naje munsha hira da Umma tace kina makaranta. To ya exams din?" Maimakon amsa wayar ta mikowa Nasiba bakin nan yaki rufuwa. Ta tayata murna suna duba wayar Mama ta fito "yau Idon kuka ce take ta murna haka kamar an baki takardar karatun likita." "Haba Mama na dena fa. Kinga wayar da Umma ta bani." "Masha Allah, Allah Ya tsare. A kula sosai don Allah banda yin abinda bai dace ba kinji ko. Ni zaki fara bawa numbar kuma" . Dariya suka yi Umar yazo shima yana nacin a bashi ya gani. Kamar daga sama aka ziro hannu aka karbe wayar a hannun Umar. Da sauri tabi hannun da kallo. Abubakar ne tsaye yana mata wannan murmushin. Yayi kyau wata uku da rabi da bata ganshi ba har kiba yayi. Ga gemu dan madaidaici ya tara shi. Fuskarsa sai tayi mata kyau. Nasiba ce tayi dan tarin gulma wanda yasa Asmau tayi firgigit ta dauke idonta daga kansa. Mama sai ta basar kamar bata gani ba ta tashi ta bar falon. "Bazaki gaisheni bane?" Ya fada yana zama kusa da yar uwarsa. Kunya ta kama Asmau tace "ina wuni?" "Tunda sai da na roka na yafe. Ni da na taho musamman saboda tayaki murnar gama makaranta ". Nasiba ta soma dariya ganin yadda Asmau tayi kamar ace kyat ta tashi a guje. Mikewa tayi "bari naje na fara shiri ana magriba Baban Amir yace zai zo daukana." Aina'u ta kinkimi Amir tabi bayanta. Yassar da Umar ne suka rage. Abubakar ya dan kallesu "baku da abinyi ne a ciki kuka tsaya a nan?" Ba shiri suka tashi suka bi bayan Nasiba. Itama Asmau tashin tayi zata bisu taji muryar Abubakar yana mata magana a hankali "not so fast Mrs A.A Matawalle. Zance zamuyi. Ko kinfi so nazo gida anjima?" A kidime take sosai. Tana dago kai ya kashe mata ido daya. Yau kuma me ya sami Yaya Abubakar tayi tambayar a zuciyarta. "Soyayyarki ce ta sameni Asmy. Kuma nayi missing dinki da yawa." Hannu tasa ta rufe

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});