Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 65

Chapter 65

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

don kunya. Kada ayi zaton ko Yassar saurayinta ne duk da kuwa hakan take fata. Amma bata riga ta faru ba. Yanzu kokarin daidaita Kawunta da yayarsa suke yi. Allah Yasa hankalinsu baya wajen. Asmau da Anti Bintu ne suka gansu. Anti Bintu sai ta tsaya wurin Col. Ishaq saboda dama tana son ganinsa. Sauri zatayi suyi magana kafin Hajiya ta fito don Alh Adamu dasu Umma sun dan tsaya hira da ita. Ita kuma Asmau ta karasa wurin su Bilkisu. Suna hangota suka tashi sai dai ta kula da hawayen da Bilkisu ke gogewa da sauri. Tsorota tayi ko Yassar yayi mata wani mugun abin. Tsaresu tayi da ido tana kallonsu daya bayan daya "Me kuke yi a nan tun dazu?" Yassar ya dan sosa kai yana murmushi "babu komai Ummin Amatullah" Tayi dan tsaki "Bilkisu fada min kinji. Me yayi miki kike kuka?" Itama murmushi tayi "Allah babu komai, abu ne ya shigar min ido" Ko kusa bata yarda dasu ba. Daga ganin yanayinsu tasan basu da gaskiya. "Tunda bazaku fada min ba bari na kira babanki, shi nasan zaku fada masa" Zata juya Yassar ya riko hannunta da sauri "don Allah kada ma ki fara. Bari su tafi wallahi zan fada miki duk abinda kike son ji. Suna kallo motocin su Ismail da Dahiru suka fita daga asibitin. Bilkisu tace "bari naje, Anti Asmau sai da safe." Asmau ta dan bata rai cikin wasa "bazan amsa ba sai naji bayani." Murmushi kawai Bilkisu tayi ta kama hanyar motar Col. Ishaq. ****** Tana karasawa taji Anti Bintu cikin tashin hankali tana cewa "wace irin magana ce wannan Ishaq? Haihuwa ta Allah ce. Yanzu saboda wannan zaka ce ka fasa. Wallahi baka ga yadda na shiga damuwa ba da naji zancen Qasim" Rabin hankalinsa yana kan Asmau da yake hangowa suna magana da Yassar. Ba a nan inda 'yarta ke kwance tana jinya yake so taji zancen ba. Bilkisu ya kalla babu fara'a a fuskarsa. "Kin gama kai gulmar? To kije ki fada masa nace kada ya kuskura ya fada mata komai yanzu" Hanjin cikinta har wani kullewa yayi don tsoro ta koma wurinsu da sauri sosai. Ya mayar da hankalinsa ga Anti Bintu. "Rashin haihuwa ba karamar matsala bace. Ke shaida ce ina sonta amma yaushe zan tauye mata hakkinta ta zauna dani babu haihuwa" "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Asmau tana ganin jarabawa kala kala a rayuwarta. Tunda ta dawo gida ban taba ganin farincikinta ba kamar idan tana tare da kai. Ishaq wallahi tana sonka. Kada kayi mata haka. Yarinyar nan taga taskun rayuwa. Yanzu kuma zata rasa masoyi" Anti Bintu tana magana ita kanta kamar zata yi kuka. Ji yayi zuciyarsa har wani zafi take masa. A jiya ya yanke shawarar ko me zai faru bazai rabu da ita ba. Amma magana daya tasa ya tuno da rashin dacewarsa da ita. ***** Kafin Bilkisu ta isa wurinsu Asmau tayo gaba. Yassar yayi mata alkawarin sai sun koma gida zai fada mata komai, ita duk tunaninta ma ko soyayya sukeyi a boye. Bata matsa masa ba tace shikenan. Cikin nutsuwa ta taho wurin da Jikamshi yake tsaye da Anti Bintu. Ita dai Anti Bintun tana ganinta ta bar wurin zuciyarta tana kara karaya. Bata san halin da Asmau zata shiga ba idan taji abinda Ishaq yake tafe dashi. Gashi lamari na haihuwa ba'a daukarsa da wasa. Ita bata isa tace dole ayi auren ba tunda da kansa ya fada mata aurensa na fari shekarunsu goma shadaya da matar. Gashi suna rabuwa ta haihu. Da zata bar wurin suka hada ido da Asmau tayi saurin sunkuyar da kai a kunyace. Shima ba dadewa zatayi a wurinsa ba saboda kada Hajiya ta fito. Yaji dadin ganinta amma yanayin da zuciyarsa take ciki ya hana ya bayyana mata duk kokarinsa na boyewa. Da murmushi a saman fuskarta ta gaishe shi. "Matar Jikamshi" "Uhmm" "Yau nafi sonki akan kullum, ji nake kamar yau na fara sonki ma" yadda yake furta kalamansa a hankali yasa taji wani dadi a ranta. Mukullin motar yake dan kadawa yace "baki amsa min ba." A zuciyarta tace zai fara sakata jin kunyar da ya saba. Kasa take kallo tace "to me zan ce?" "Au baki ma sani ba, to bari na fada miki tunda ni nake son jin amsar. Ina ji idan baki fadi abinda nake so ba bazan iya kaimu gida ba." jikinsa duk a sanyaye yake. Daga yau baya jin zai kara furta mata kalmar so. Kallo kuwa tamkar ya cinyeta da idonsa. Jin soyayyarta yake sabuwa a zuciyarsa. Dago kai tayi "don Allah ka dena fadin haka bana so" "Nine bakya so ko maganar da nayi" Kwabe masa fuska tayi tana shirin kuka yaji ta kara shiga ransa"kasan me nake nufi. Ka dena cewa bazaka iya zuwa gida ba" Yayi dariyar karfin hali "to bani amsar da ta dace" Rufe fuskarta tayi da mayafi sannan tace "I love you Jikamshina" da sauri ta juya zata gudu ya dakatar da ita ta tsaya amma bata juyo ba. "Matar Jikamshi ki rike mijinki da gaskiya kinji ko. Allah Ya albarkaci rayuwarki" Duk ya kashe mata jiki da kalamansa amma ko kadan bata kawo komai a ranta ba. Ita a zatonta shi yake nufi a matsayin mijin nata shiyasa tace "Amin" sannan ta shige cikin asibitin. Allah Ya taimaketa domin kuwa a hanya ta hadu da Umma da Mama sun rako Haj Lubabatu. Gashi babu damar canja hanya haka tayi mata sallama ta wuce su kuma suka rakata har mota. Har su Umma suka zo tafiya Anti Bintu bata ga wani sauyi a tare da Asmau ba. Wannan ya sa tayi tunanin Ishaq bai riga ya fada mata ba. Duk su biyun tausayi suke bata, zata saka su a addua don ita bata san wace shawara zata basu ba. ***** Bayan kwana biyu aka sallami Amatullah. Duk kwanakin da Mami tayi a Kano a gidan Col. Ishaq tayi su don kuwa da gaske Haj Lubabatu ta hanata kwana a gidanta. Ranar da zata tafi suka taru ita da kanneta suka sake bawa Hajiyan hakuri. Shi Col. Ishaq tuni ya ware dasu. Fushin bazai kaishi ko'ina ba yanzu tunda akwai gaskiya a maganarsu. Mami ta tafi akan duk shawarar da ya yanke su duka zasu bashi goyon baya. A wannan lokacin ya rage kiran Asmau. Idan ta kira sai taji wayar a kashe. Nambobinsa biyu gareta duk bata samunsa sosai sai idan shi ya kirata. Shima din hirarsa tafi yawa da Amatullah. Idan ta karbi wayar daga gaisuwa sai yace mata zaiyi aiki ko zai kwanta. Tun bata dauki abin komai ba har dai ta fara tunanin akwai wata a kasa. A bangaren Qasim ya matsa mata sosai da waya yanzu. Yazo sau daya ya koma bakin aikinsa. Nunawa yayi bai san da maganar Col. Ishaq ba. Ita kuma taki sakar masa jiki tana jira taji daga bakin Jikamshi tukunna. ***** Haka tayi sati daya duk abubuwa sun cakude mata. Jafar ya karbi takardunta na SSCE zai sake nema mata admission. Amatullah tunda taji sauki Abdulhalim ya zo wata litinin da safe ya tafi da ita makarantar da yaransa suke yi. Makaranta ce mai tsada sosai domin kuwa ana arabiya da boko tun bakwai da rabi

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});