Chapter 4
Chapter 4
tace "kiyi hakuri Asmau. Shima ba gaggawa yayi ba. Mu kuma da kike ganinmu a nan ba jinkiri muka yi ba. Duk mai rai yana da wa'adin da Allah Ya dibar masa na rayuwar duniya. Mutuwa nada daci amma babu abinda hakuri da tawakkali ya bari." Maganganun Umma suka sake saka mutanen dakin kuka. Asmau kuwa taki bude idon. Duhun da take gani ido rufe ya fiye mata akan hasken da babu Abubakar a cikinsa. Duk yadda aka rinka rarrashinta sam taki yarda ta bude idonta balle ta tashi zaune. Suna haka suka ji sallamar Haj Yalwa da Abdulhalim. Ita da Umma suna hada ido sai kuka. Suka rungume juna suna yi ana basu hakuri. Umma tace cikin kuka "Mama Yalwa me yasa kika fito? Allah Ya jikan Abubakar....Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Dakin ya sake rudewa da koke koke. Bayan sun dan nutsu ne Mama ke tambayar ya jikin Asmau. Umma ta dan tabe baki "tana jinmu tun dazu ta farfado amma taki bude ido. Mama Yalwa ni dai banso fitowarki yanzu ba. Mutane zasuyi ta cigiyarki a gida. Da zamu samu ta tashi muma duk gidan zamu taho yanzu." "Zamana a gidan bazai dawo dashi ba Umma. Komai na gani ji nake kamar karya ne Abubakar yana nan." Tashi Mama tayi ta koma gaban gadon da Asmau take kwance tana hawaye. A hankali Mama ta tayar da ita zaune ta rungumeta a jikinta tana shafa mata baya. Abdulhalim yana tsaye daga bakin kofa zuciyarsa cunkushe da bakinciki. Cikin nutsuwa Mama ta soma magana "Asmau kuka ba soyayya bane tsakaninki da Abubakar. Kiyi masa addua da fatan samun rahmar Mahaliccinmu. Da iliminki amma ace kin kasa karbar kaddara? Dukkanmu nan jiran lokaci muke yi. Ki daure ki tashi indai ba kina son ki nuna cewa kinfi karfin jarabta daga Allah ba." Jin haka Asmau ta bude idonunta da suka kumbura da kyar. Dai dai ta rinka kallon mutane kafin ta sake fashewa da wani kukan mai shiga rai aka shiga tayata. Babu mai bawa wani hakuri sai Abdulhalim. Shima da ya gaji fita kawai yayi daga dakin. Likita yazo ya sake duba Asmau ya tabbatar musu cewa zasu iya tafiya da ita gida. A haka suka tafi ko da suka iso gate din gidansu Abubakar da yake shine a farko kafin nasu wani kukan ta sake fashewa dashi. Mutanen da suka zo daurin aure sun koma zaman makoki. Duk a nan suka sauka suka shiga gidan. Gaban Asmau sai faduwa yake balle da taji ana cewa ga amaryar nan ta shigo. Mutane da dama suka taso ana kallonta. Kowa na fadin albarkacin bakinsa na dangane da tausayawa gareta. Bayan sun shiga gidan dakin Mama aka wuce da ita. Ko zama batayi ba Umma tace mata taje tayi alwala saboda batayi azahar da la'asar ba. Jiki kamar wadda bata da laka haka ta shiga bandakin jiri na dibarta ta dauro alwala tazo ta biya sallolin dake kanta. Tana sallar tana zubar da hawaye. Bayan ta idar ta dade tana kuka da addu'a. Sadiya ta hado mata tea mai zafi ta mika mata. Kai ta girgiza alamun bazata ta karba ba. Kusa da ita Sadiyan ta zauna " ki daure ki sha ko yaya ne sai kici abinci. Kowa da kika gani dauriya kawai yake yi Asmau." Nata hawayen ta share sannan ta dubi Shema'u tace "Anti Shema'u kisa baki ta sha ko kadan ne". Taruwa akayi ana lallabata tasha tea din amma taki har Umma da Mama suka dawo daga waje inda suka karbi gaisuwar wasu maza 'yan unguwar. Suma suka saka baki har Asmau ta karbi tea din. Bai fi rabin kofi tasha ba ta fara kwara amai saboda tun jiya rabonta da abinci. Haka ta rinka amai ta baki ta hanci abin tausayi. Ta galabaita sosai. Bayan ta gama aman Nasiba ta dagata zata shiga da ita bandaki ta gyara jikinta ta fadi kasa a sume. Nan da nan aka taru a kanta ana mata fifita. Aka shafa mata ruwa a fuska tare da sauke mata zip din rigarta don tasha iska amma duk da haka bata tashi ba. Mama tace aje a kirawo mata Baba a waje. Ita Umma gefe kawai ta koma tana kuka. Gani take yi kamar Asmaun ma ta cika. Shi da wasu suka shigo suka ga halin da Asmau ke ciki. Jafar aka kira da Abdulhalim suka sakata a mota aka kaita wani asibitin mafi kusa dasu. Su Mama suka biyosu a wata motar kowa bakinsa da addu'a. Bayan an bata gado wata likita da nurse suka zo suka tsaya a kanta ana ta kokarin ceto rayuwarta. Allurai kala kala kam tasha su. Likitar tace jininta ne ya hau ga kuma rashin kuzari a tare da ita. Gwajin jini ta umarci ayi mata don su gani ko akwai wani ciwon a tare da ita. Har wani likitan ne yazo suka taru ana ta abu daya sannan suka samu ta farfado. Su Umma sai godiya suke ga Allah. Mama na zaune a kusa da Asmau tana sake bata baki akan tayi hakuri kuma duk da ana mata karin ruwa ta daure taci abinci sai ga nurse din ta shigo. Shema'u ta tashi da kyar Anti Bintu tace " kema kina bukatar hutu tun dazu baki zauna ba. Kada kafarki ta kumbura". Murmushi Shema'u tayi sannan ta tambayi nurse din tana fata babu wata matsala a tare da Asmau. Nurse Ngozi ta washe baki cikin hausarta irin da inyamuran da suka zauna a Kano tace "babu wani masala sai abin murna...." ta mayar da kallonta ga Asmau "...congratulations ashe ciki ne yana baka wahala." Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci har maganar nurse Ngozi ta gama shiga kwakwalwarsu. ABINDA AKE GUDU ๐๐ฝ4 Batul Mamman๐ Kallon kallo suka fara yiwa juna. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin Asma'u ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki. Mama ce tayi karfin halin kallon Ngozi tace" 'yar jakar uba bakinki ne cikin ai, dama Hausa bata gama zama ba dole kiyi shirme. Bari likitan tazo da kanta muji daga bakinta. Kila ma ciwon ciki kike son cewa kika ce ciki zaki karasa tsorata mu." Nurse Ngozi tace "Madam ina jin Hausa sosai fa. Yarinyarki is pregnant zata haihu shine abinda nake nufi." Takardar hannunta Umma ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Shema'u ta karbi takardar suka hada kai ita da Nasiba da Anti Bintu suka karanta. Gabadayansu Asmau suka zubawa ido da tsantsar mamaki a fuskokinsu. Mama dake tsaye a gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar. Jafar ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan inda Abdulhalim yake tsaye tana masa bayanin magungunan da aka rubutawa Asmau. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Abdulhalim ya tambaye shi ko jikin Asma'un ne. Jafar yace "ai gara ace jikinta ne da abinda mahaukaciyar nurse dinnan ta rubuta. Wai ciki? Asma'u ke da ciki kamar a tatsuniya...." likitar ya kalla "...ki taso muje ki sake gwadata don kada ku karasa gawar da ba taku ba." A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103