Chapter 23
Chapter 23
na rabuwa. Suna mota ita da Abubakar babu wata hirar kirki don basu taba kadaicewa a mota haka ba na tafiya mai nisa. Hanyar cikin gari ya nufa ya kashe motar a gefen titi. Asmau ta kalle shi zata yi magana sai ta kasa ganin idanunsa sunyi wani iri kamar wanda yake cikin tashin hankali. A raunane yake dubanta har sai da tsigar jikinta ta tashi don tsoro da ya dora hannunsa a kan nata. "Asmau" Yaushe rabon da ya kirata da sunanta haka. Gabanta na dukan uku-uku ta amsa. "Idan na rokeki alfarma zaki yi min?" Ita fa Yaya Abubakar tsoro yake bata da yanayinsa na yau. "in sha Allahu idan baifi karfina ba". Gwauron numfashi ya ja. "Asmy ina cikin matsala kuma ke kadai ce zaki iya yi min maganinta. Ko sati ba'ayi ba da muka amince mun dena taba jikin juna.." Bugun zuciyarta ne ya karu tana ganin kamar ta fara fahimtar inda zancensa ya dosa. "Ni mutum ne mai yawan bukata, ina tsammanin baki san me hakan yake nufi ba." A ranta kuwa tace sai dai na fadawa wani. Rabe-raben mutane ta fannin sha'awa tuni ta san shi a posts din waya. Muryarsa wadda take rawa taji a kusa da ita. "Ina cikin tashin hankali da son kasancewa tare dake. Wallahi bazan iya kaimu Kano ba a yanayin da nake ji yanzu musamman da kike zaune kusa dani. Ki taimakeni ko sau daya ne na kawar da wannan masifaffen tunanin." Kofar motar ta kama a gigice hawaye na wanke mata fuska jin ya saka lock. Sanyin AC bai hanata gumi ba. "Yaya Abubakar ka rufa min asiri ka mayar dani gidan Anti Bintu. Duk ni na jawo wannan matsalar da na rinka saka kaya masu matse jiki ina zama kusa da kai. Sharrin shaidan ne da na zuciya don Allah kayi hakuri nan da wata hudu zamuyi aure fa". Magiyar da take masa jin muryarta yake kamar tana masa busa. Wannan wace irin masifa ce??? Shiyasa tun a da yake nisanta daga duk abinda zai jawo masa sha'awa tunda ya gane yanayinsa. Hawaye ne ya zubo a idonsa wanda bai san dalilinsu ba. "Ke kadai nake so kuma da ke kadai na amince Asmy. Idan baki amince ba wallahi nayi miki rantsuwa zan nemi wata. Bani da lafiya duk a dalilin sonki da son kusantarki. Ko kinsan satin nan ko sau daya banje wurin aiki ba saboda halin dana tsinci kaina a ciki". Kuka Asmau take yi sosai gashi tausayinsa ya mamaye zuciyarta. " Yaya kada mu aikata haram. Kuma idan ka rabani da abinda duk budurwa take takama dashi yaya zanyi?" Hannuwanta duka biyun ya rike. "Asmy kinsan dai nine mai aurenki ko? Kuma ni ba wai zanyi miki yadda zaki tashi daga budurwa bane. Akwai yadda zanyi babu wanda zai ce namiji ya kusanceki. Ki taimake ni. Har bincike nayi wasu malaman sunce kudin aure daidai yake da sadaki. Ko baki ga iyayenmu maza ke zuwa ba ayi a gaban shaidu. Al'ada ce kawai sake taruwar da ake yi a daura aure. Amma yanzu ma a haka ni da ke matsayin mata da miji muke." Shi da yake fada mata hakan ya tabbatar karya yake yi amma babu yadda ya iya da zuciyarsa. Roko da rarrashi haka ya rinka yiwa Asmau tana kuka haka ta amince saboda tausayin da ya bata da tsoron kada ya nemi wata. Wani hotel ya sama musu kuma da yake duk sunyi shigar mutunci babu mai cewa ba ma'auratan gaske bane. Haka ya karbi mukullin dakin zuciyarsa tana kwabarsa da abinda yake shirin aikatawa amma gangar jikinsa bazata iya hakuri ba. A kofar dakin da kyar Asmau ta shiga. Yana rufe kofar ta kara fashewa da kuka. Abubakar yayi nisa duk da yana tausayinta hakan bai hanashi biyan bukakarsa ba. Alkawarin da yayi mata na yin dabara kada ta rasa budurcinta tuni ya manta dashi. Sai da komai ya kammala yaji kamar tashin hankalin duniya duk ya kare a kansa. Gefen gado ya koma ya dafe kai ya rasa inda zaisa kansa. Asmau tana kwance sai sautin kukanta ke tashi. Ga ciwo ga bakinciki. Sun kusa awa daya sannan yayi wanka ya umarceta da itama tayi. Wannan masifa da yawa take...Ya Allah Ka tsare mana imaninmu. Haka suka fito babu wanda yake yiwa dan uwansa magana. Ya biya kudin hotel suka wuce Kano yana ta zabga gudu a hanya. A bakin gate din gidansu ya sauketa zuciyarsa tana kuna. Ya rasa me yake ji game da Asmau. Ko kayanta bai taimaka mata da dauka ba haka ta fito dasu ta shige gida fuska a kumbure. Su Umma sai murna suke yi ta dawo amma ganin yanayinta Umman ta tsorata tana tambayarta abinda ya faru. Asmau ta fashe da kuka ta rungume mahaifiyarta. Yau taci amanar addininta kuma taci amanar Umma. Taruwa suka yi a kanta Jafar ya taba jikinta. Zazzabi ne sosai a jikin hatta kanta ya dau zafi. Ya danyi murmushi "Umma wannan 'yar taki ta fiye shagwaba da raki. Daga zazzabi kuma sai kuka?" Sai a lokacin tayi dan murmushi ganin cewa idan ta cigaba da kukan zata tonawa kanta asiri. "Yaya Jafar ji nake kamar kan zai tsage biyu" Umma ta tasheta tsaye "Ki dena tsorata ni irin haka Asmau. Baki ji yadda gabana ya fadi ba. Muje ki dan watsa ruwa sai kici abinci kisha magani. Ina Abubakar din?" Har zuciyarta ta razana jin an ambaci sunansa. "Ya tafi gida amma yace zai shigo ku gaisa anjima". "Babu komai ai kun sha hanya ga rana. Allah Yasa ba kukan nan naki kika rinka yi masa ba saboda baki jindadi." ***** Har washegari Asmau tana kiran wayar Abubakar saboda bai zo ba kamar yadda tayi tsammani. Babu waya babu text. Nata kiran kuma yaki dauka. Hankalinta yayi matukar tashi. Yanzu idan ya fasa aurenta saboda abinda suka yi yaya zata yi da ranta. Shima a gida kwana yayi kuka. Idan yaga wayar Asmau ji yake kamar yasa ihu. Zuciyarsa ta kasa rabe masa haushinta yake ji don ta bashi kanta ko kuwa haushin kansa da ya tilasta mata. ABINDA AKE GUDU🙆🏽18 Batul Mamman💖 Bacci barawo ne ya sace Asmau ba don taso ba. Ta raba dare tana kuka wanda ya haddasa mata mugun ciwon kai ga jikinta da yayi tsami. Washegari wurin karfe takwas da rabi ta fito daga dakinsu zata shiga kitchen dora ruwan tea ta tarar Umma har ta dama kunu tana buga kosai. Gaishe da Umman tayi sannan ta yunkura zata karbi aikin ta karasa Umma tace ta bari ya jikin nata. Kafin ta amsa Umma ta dakatar da ita "Asmau ki fada min gaskiya meye yake damunki? Ji yadda fuskarki ta kumbura ga wata tafiya kina yi kamar me tatata". A dan tsorace Asmau tace "zamewa nayi a toilet da zanyi alwala." Umma ta bita da kallo na rashin gamsuwa. "To fuskar taki fa? Kinsan bana son boye-boye idan rigima kuka yi da Abubakar jiya ki fada min tun wuri ayiwa tufkar hanci." Murmushi Asmau ta kalalo "Umma lafiya kalau muke. Kaina ne har yanzu yake ciwo sosai kamar bansha magani ba". "Idan anyi breakfast sai Jafar ya kaiki asibiti tunda dai kin sha magani jiya bai warke ba gara kiga likita
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103