Chapter 11
Chapter 11
fara kokarin sakawa ta dan hada ido da yarinyar dake tsaye a wurin. Ga mamakinta murmushi sosai yarinyar tayi mata. Uwargida tayi dariya sosai "duk yaran gidan nan da kika gani babu wacce take yarda karuwanci ta fito yi sai babu ta sakata a gaba. Ni bazan matsa miki ba. Akwai daki na haya dubu goma duk wata. Idan kina so a jona injin gidan nan dake ki rinka samun wuta idan babu a gari duk sati zaki biya dari biyar. Ci, da sha da sutura kuma kowa ta kansa yake yi. Zabi ya rage naki. Zaki zauna ne ko zaki fita ki kwana a titi". Shiru Asmau tayi tana tunani. Yanzu idan ta fita ina ta nufa. Matar ta katse mata tunani " bana tilasta mace tayi sana'ar da bata so amma indai ba kina da jari ko wurin zuwa fa to nan ne gidan da kowace 'ya da bakincikin rayuwa ya korota zata kira gida." Bulayi yace "kuma gata da jikin sana'ar ba. Fatarta har wani sheki take yi tayi luwai-luwai. Ni da na matsa kusa da ita ma har kamshi naji tana yi shiyasa nace da shirinta ta fito." Dan murmushi Uwargida tayi sannan ta zaunar da Asmau a kusa da ita " ke amarya ce ko?" Ta fada tana daga gira. "Irinku yawanci mijin ne bakwa so sai ku gudu. Shiga duniya ba da ka ake yinsa ba. Dole ki fara ta wani wurin. Kamar yadda na fada miki ko wurin zama ki samu nan gaba idan kika shafa kika ji babu abinda zaki ci nasan zaki fara sana'ar da bata tsufa. A lokacin zan taimaka miki da kayan aiki wato maganin mata sannan na hadaki da kilayen(client). A tsarin gidan nan duk wadda tayi ciniki a gida ko a waje zata bani kaso goma a ciki. Sauran bayani dai sai kin shigo hannu. A lokacin kuma zan saka miki suna. Ni nan babu ruwana da sunan kowace yarinya na gaskiya." Yarinyar dake tsaye a gefe tayi tsaki "haba Mama tace ba abinda ya fito da ita ba kenan ko dole ne?" Bulayi ya kalleta yana dariyar shakiyanci "ustaziya Zubaida kenan, kina nan da halinki na korar mana alheri". Baki ta murguda masa Uwargida tace " yanzu ma fadan da nake mata kenan ya kamata ta ajiye girman kai ta rungumi sana'ar da na haifeta kuma na raineta a ciki shine ta fara min rashin kunya na bige shegen bakin." Asmau ta sake kallon yarinyar sai taji tana sonta. Murmushi tayi mata yarinyar ta mayar sannan Uwargida ta umarceta da ta nuna mata daki daya cikin wanda babu kowa. Babu yadda Asmau ta iya dole ne ta nemi muhalli kafin tasan yadda zata fara gudanar da rayuwa. Shiyasa ta bi bayan Zubaida. Wani daki ta bude duk yayi kura. Zubaida tace bari na kawo tsintsiya. Bata dade ba ta dawo da yake akwai wutar nepa ta kunna fitilar dakin. Sai da ta taya Asmau shara da goge kura suka karkade yamushasshiyar katifar dakin da babu zanin gado. Bayan sun gama Zubaida ta fita sai gata ta dawo da tuwo wanda aka fara ci da ruwa a kofi. Tana murmushi tace "Allah Yasa ki iya ci dazu na fara ci Mama ta fara damuna na barshi. Don girman Allah da Ya haliccemu kada kiyi karuwanci. Gidan nan har mace ta nemi mace anayi." Asmau ta karbi tuwon da murna taci tayiwa Zubaida godiya sannan ta kara tabbatar mata da cewa da zarar komai ya daidaita barin gidan ma zatayi. Zubaida tace "idan babu damuwa ki fada min abinda ya raboki da gidanku". Ajiyar zuciya Asmau tayi "in sha Allahu gobe zan fada miki tarihin rayuwata". Zubaida sai murna take. Har ta fita ta dawo da sauri "ina kara tuna miki kada kiyi sana'ar matan gidan nan. Mata da yawa da farko haka suke cewa sai an kwana biyu su fi kowa lalacewa. Ni ma ba don bani da wurin zuwa ba da tuni na bar gidan nan." A haka suka yi sallama. Da Zubaida ta koma dakinsu har ta kwanta addu'a take yi Allah Yasa bakuwar nan kada tayi halin matan gidan. Bata da wani ilimin addini amma tasan cewa sana'ar da ta tashi taga mahaifiyarta tanayi bata da kyau.. Washegari shayi da bredinta ta dauka zata fita daga dakinsu Uwargida ta kalleta tayi murmushi. "Zuby tawa kenan, da kinga bakuwa kin rinka rawar kafa kenan ke a dole sai kinsa ta koma gidan iyayenta. Rayuwar duniyar nan ta wuce tunaninki fa. Ki sani duk wadda kika gani a nan to abinda ya korota yafi nan muni." Zubaida ta gallawa Uwargida harara ta fita. Kai tsaye dakin Asmau ta wuce. 'Yan matan gidan suna ta mata dariya don sun saba ganin irin haka a wurinta idan taga bakuwa. Da sallama ta shiga dakin. Asmau na gyangyadi a zaune. Kyamar katifar yasa bata kwana a kai ba. Kusan kwana tayi tana koke-koke da addu'o'i. Cike da farincikin ganin Zubaida ta amsa mata sallama. Zubaida na zama ta mika mata abincin ta karba da godiya taci. Sannan ta tambayeta inda ake samun ruwa domin taimama tayi da asuba tayi sallah. "Meye kuma taimama?" Zubaida ta tambaya. Asmau tayi mata bayani. Zubaida ta gamsu sannan ta sanar da ita kowa a gidan siyan ruwa yake yi. Dole sai ta siye duk wani abin amfani sannan ta tanadi kudin hayarta domin anjima kadan Uwargida zata bukaci ta kawosu. Bayan duk ta gama jin bayanin gidan ne Zubaida tayi mata tuni akan alkawarinsu na jiya. Asmau tayi murmushi mai ciwo sannan ta fara sanar da Zubaida dalilin watsewar farincikinta. *FARKON LABARI* Alh Shu'abu Yahaya sunan mahaifinsu Asmau. Iyayensa duk 'yan Kano ne kuma a nan cikin Kanon suka tashi. Su biyar ne a gidansu shine na biyu. Babbar yayarsa suna kiranta Yaya Abu sai shi sannan mai binsa Rabe sai Lami da Garzali. Babansu mazan kawai yake sawa a makaranta. Saboda haka Shu'aibu yayi karatu har matakin digri inda ya karanci Agric Science harkar aikin gona. Shi mutum ne mai saukin kai da kirki shiyasa mahaifinsu yake ji dashi. Sauran 'yan uwansa kuwa kusan duk halin Hajjo mahaifiyarsu suka debo na fada da sa ido. Lokacin bautar kasa aka tura shi makaranta a wata karamar hukuma a jihar Niger mai suna Wushishi. A can ya hadu da Bara'atu tana ajin karshe na sakandire. Farkon haduwarsu duk da baya koyar da 'yan ajinsu soyayya ta kullu a tsakaninsu. Abu kamar wasa har lokacin komawarsa gida yayi inda yayi mata alkawarin turo iyayensa. Dama a hannun kawunta take ita da kanwarta Bintu marayu ne ko kadan basa jindadin zama da matar kawun. Da ya koma Kano ya sanar da iyayensa Hajjo ta dage indai tana da rai danta bazai auri banufiya ba. Duk 'yan Niger mayu ne a cewarta. Ita a son ranta ya auri 'yar kanwarta. Akayi ta jan zance ita da mahaifinsu shi kuma ya dage Shu'aibu sai ya auri wadda yake so. Rigima sosai akayi sai bayan wata biyu iyayensa suka je Wushishi. Lokacin Bara'atu har ta fitar da rai. Ba wani dogon lokaci aka saka bikin ba gashi ko aiki bai fara ba. Wurin hada lefe yasha wahala Bara'atu ta bashi kudi cikin kudin gadonta ya cika ya siya mata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103