Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 73

Chapter 73

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tuna cewa samu da rashi na Allah ne. Da kudi na bayar da haihuwa da wasunmu sun sayar da komai nasu don suji kukan jariri a gidajensu. Ki godewa Allah kina da wadda zaki kalla a matsayin tsatsonki. Ni bani da wannan kuma na yarda na karbi kaddarata. Ina fatan hakurin da nake da wanda zaki zo ki tayani muyi ya zama silar samun rahmarmu a wajen Allah" Da gaske Asmau take kuka. Abinda ake gudu ya riga ya faru. Allah Ya kara kare sauran 'yan uwa musulmi. Ji take duk duniya idan ba da Jikamshi ba bazata taba iya rayuwar aure da wani ba. Shi kanshi idonsa yayi ja amma sai ya daure yace "kinsan dai ba'a daura mana aure ba don Allah ki dena kukan nan. Nafi so ki tara shi sai ranar da idan kinyi zan daukeki na...." Da kukan nata da jikakkiyar fuska ta dago kanta tana murmushi tare da dora hannunta irin yadda yayi a lebenta "shhhhh Jikamshina kada ka karasa ko na gudu" Yayi murmushi "ina sane na turaki cikin motar don kada kice zaki gudu. Share hawayenki kinji Matar Jikamshi. Kada Umma ta hanani aurenki, kullum nazo sai kinyi kuka." Tissue din gaban motar ta zara tana goge hawayen yana fada mata wuraren da kwalli ya bata. Tace zata duba madubin motar yaki yarda. Haka ta goge suna kallon juna suna dariya. Sun danyi hira yake ce mata sunyi magana da Umma yana ganin nan da wata uku za'a saka musu rana. Umma tace akwai bikin Dijan Anti Bintu wata biyu masu zuwa wanda shima lokacin yaso ayi aurensu. Yasan kafin nan ya gama gyaran gidansa. "yanzu da Umma kayi zancen saka rana?" "Na lura kin mayar dani mara kunyan karshen zamani. To Ismail ne ya fada musu. Ni shiru nayi ina ta sunkuyar da kai irin yadda kike yi" Dariya take yi wanda hakan yake sanyaya masa zuciya. Yana jindadin ganin ya faranta mata. Sun fi awa daya a wurin batare da sun san lokaci ya wuce ba. Ismail ne ya fito da Amatullah a bayansa. Haka nan Allah Ya dora masa son yarinyar nan. Shi bai ki ba wallahi Asmau tace ta bar masa ita. Suna zuwa gaban motar Amatullah tace "Ummi kinga sabon Baba ya goyani." Col. Ishaq ya tashi tsaye ya sauko da ita daga bayan Ismail sannan ya dorata a cinyarsa. "Idan banyi da gaske ba naga alama zaka yi min kwacen 'ya" "Colonel ai na gama da kai. Ka taho nan sace zuciyar Umminta da dadadan kalamai ni kuma ina nawa yakin a kanta da kayan kwadayi. A takaice dai yanzu nine baban" Asmau ta rufe ido tace "Yaya Ismail kada muyi haka da kai" Jikamshi yace "gara ki kira Musaddiq yaya da wannan. Shifa bai san ya girma ba. 'ya'ya biyar amma idan yana barkwanci kamar mara iyali." "Kada ka zubar min da girma mana soja. Yanzu dai gaskiya Madam ta damu ban koma gida ba tun fitar safe. Ummin Amatullah taimaka ki sallame shi mu tafi. Don ma na fada mata Yayanta na rako zance yau da an hanani tuwon dare" Ta fuskanci da gaske Ismail mutum ne mai barkwanci. Jikamshi ya katse mata tunani da cewa "haka suke daga shi har matar tasa. Gidansu kamar gidan wasan yara" "Allah Sarki kace ina gaisheta" "Fada mata da kanki dai" Ismail ya ciro wayarsa ya kira Aisha matarsa. Da gaskiyar Jikamshi kuwa don da gaske Aisha tayi ta janta da hira da wasa kamar ta santa. Karshe tayi ta jaddada mata ta rike amanar yayansu. Ita dai Asmau sai dariya kawai. Bayan sun gama wayar sukayi sallama dasu. Jikamshi kamar kada ya tafi. Ba don dare yayi ba kuma dai yakamata Ismail ya tafi gida yau da Umma sai ta koreshi da kanta. A hanya ne ya dubi kaninsa yace "nagode Ismail da yadda kake yiwa Asmau da Amatullah " Idonsa na kan titi yace "Colonel nine da godiya da ka yafe min maganar da nayi maka rannan. Duk da bana ganinsa amma na tabbatar shaidan ne irin masu hada fada tsakanin 'yan uwa ya murde min harshe na fadi abinda banyi niyya ba" Murmushi dan uwan nasa yayi "zaka fara ko, kada ka damu komai ya wuce a wurina in sha Allah. Ka fadawa su Dahiru idan zasu sami lokaci karshen sati sai muje Jikamshi ayi magana dasu Kawu" ***** Ranar Juma'a da yawancin ma'aikata ke tashi da wuri Col. Ishaq da kannensa maza suka tafi garinsu, Jikamshi a Katsina garin Dikko...Katsinawa kunya gareku ba tsoro ba. Kafin tafiyarsu dama Hajiya ta riga ta fadawa Yayanta da kuma kanin mijinta komai game da Asmau a waya. Kamar yadda yayi tsammani bai sami goyon baya sosai daga garesu ba. Wani kawunsa ma cewa yayi indai saboda rashin haihuwa ne yasa zai auri karuwa, karuwar ma mai 'ya to akwai zawarawa a gari masu yara ya zaba a cikinsu don Allah Ya aura amma kada ya gurbata musu dangi. Su da suka je yin kwana biyu basu sami dawowa ba sai litinin. Col. Ishaq sai da ya taba rashin kunya aka sami daidaito tsakaninsa da Kawunan nasa da manyan Gwaggoninsu. Daga karshe ma dai harda wa'azi da nasiha ya hada. To anyi sa'a da yake ana ganin girmanshi gashi kuma da dan abin hannunsa sai suka gama fadansu suka amince zasu taho Kano nan da sati biyu. Kamar yadda ya saba ya hadasu da alkhairi kafin ya tafi. Wannan karon harda kari don kada su bashi kunya ma. ***** A bangaren su Asmau kuma washegarin da Jikamshi yaje gidansu Qasim yazo. Ya nuna mata ya janye batun aurensu kuma yana mata fatan alkairi a zamansu da Col. Ishaq. Taji kunya sosai tace "Yaya Qasim kayi hakuri da hukuncin da na yanke a matsayin zabin Allah. Bazan taba mantawa da abinda kayi mana ba. Duk da kaine babban abokin Yaya Abubakar amma hakan ba shine yake nufin sauran su gujemu ba. Tun ranar da ya rasu ban kara jin duriyar kowa ba sai taka. Nagode Allah Ya baka mace tagari kamilalliya." Yayi mata murmushi "babu wata godiya mata zaki nemo min kawai." Itama tayi murmshin ga dan hawayenta "to In sha Allahu zan nema maka kuwa" "Kada ki dauka wannan abin zai shafi zumuncinmu Asmau. I am always here for you. Ki daukeni dan uwanki wanda zaki iya fadawa matsalolinki. Shi kuma soja tunda yayi min fin karfi ki fada masa aure bazai yiwu ba sai ya kama kafa dani." "An gama ranka ya dade" ta fada zuciyarta wasai. Alhamdulillah dama bata so su rabu ana jin haushin juna. ABINDA AKE GUDU🙆🏽50 Batul Mamman💖 Tun daga wannan lokacin tsakanin Matar Jikamshi da Jikamshinta wata sabuwar soyayya ke tashi da shakuwa. Duk wani labarin rayuwarsu da basu sani ba a da yanzu sun fayyacewa juna. Komai nasu abin shaawa sannan suna soyayya a tsaftace. Irin hirar nan da zata jawo budurwa da saurayi su fara sakin layi har a kai ga jin sha'awar kusantar juna sun nesanta kansu da ita. Kuma duk da haka idan kaga yadda suke sai sun burgeka. Wannan ita ce soyayya ta gaskiya. Duk wata hira mai tado sha'awa sunanta batsa kuma tana cikin jerin abubuwan da suka kusanci zina indai ba ga ma'aurata ba

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});