Chapter 57
Chapter 57
daya ne sai ta tsani mahaifiyar da ta sha wahalar rayuwa don ta haifeta. Babu dan da yake son jin shi shege ne. Sannan ga soyayyar wani Allah Ya dora mata amma saboda abinda ya faru a baya idan tace zata bijire ma kallon mara kunya kuma mara godiyar Allah za'ayi mata. Allah Sarki Asmau da matan da suka sami kawunansu a yanayi shigen nata. Tuba da tawakkali shine kawai kwanciyar hankali garesu. Anti Bintu tana ta tunani har bacci ya kwasheta a zaune Asmau bata idar da sallah ba. Itama sai gabanin asuba ta soma baccin. Ana kiran assalatu ta tashi dama baiyi nisa ba. Ta shi Anti Bintu da 'yan matan da suka shigo dakin kwanciya tun tana sallah. Sai wurin bakwai na safe bacci mai nauyi ya dauketa. ***** A kitchen Umma ta rabawa kowa aikinsa na taron gobe. Gidan Mama zasuyi meatpie da doughnut. Nan kuma cake zasuyi da pepper chicken sai lemuka da za'a siyo. Har dakin Yassar taje ta bashi kudin abubuwan da zai siyo a fara aikin yace mata da zazzabi ya kwana. Yassar da bashi da kyuyar aike yau kirikiri ya nuna mata bazashi ba. Dama tun jiya ta kula yana wani cin magani ta rasa dalili. Bata san Col. Ishaq yake tayawa kishi ba tun kafin ya fara nasa. Dayake Shemau zata zo sai kawai ta kirata a waya ta fada mata abubuwan da zata taho dasu. Ta fito tana mitar tasan Yassar kalau yake Anti Bintu tayi dariya. "Indai Yassar ne ranar daurin auren ma yana iya kirkiro ciwo. Don baki san irin shakuwarsu da Ishaq bane." "Ke kuma naga alama abin yayi miki dadi. Ni duk a yaushe ya tara masoya a gidan nan ne ban sani ba?" "duk abinsa ai dole yaji kunyarki. Don baki ga yadda mukayi dashi a Zaria ba. Hatta babansu Dijah sun sha hira sosai. Tamkar 'yan uwansa haka ya dauke mu. Gashi yanzu kun zo kun raba" Umma ta rike haba tana kallon kanwarta. Da gaske Bintu ta zama 'yar kamfen "kun mayar dani wata boss dai. Gani kuke yi kamar bana son Asmau. Bari ayi auren ku gani idan suka fara zaman lafiya. Yau fa ko gaisheni bata fito tayi ba." Anti Bintu tace "bacci take yi, jiya kwana tayi tana sallah da kuka" Hajjo dake tsaye a bakin kofa tana musu dariya tace "ta kwana sallah kika ce, to ni dai babu ruwana Bara'atu da Garzali ne suka yanke shawarar. Allah Yasa dai bata ambaci sunana a adduar ba. Ko dai na tasheta na tambayeta ne. Kunsan addua ba abin wasa bace" Duk su biyun dariya suka yi. Daga falo suka ji shigowar Zubaida da Sabira. Har kitchen din suka zo aka gaisa suna yiwa Zubaiba fadan dalilin zuwanta tace "Umma jiya banyi bacci ba tunda ya fada min gobe za'a kawo kudin Asmau. Mu dan shiga ciki akwai wani sirri da nake tsammanin bata fada miki ba" Anti Bintu tace "fadi a nan kawai, ba zancen Ishaq bane" Zubaida tace "wannan sojan ko. Ashe kun sani, to meyasa za'a hadata da Qasim?" Hajjo tace "kinga matar auta, jeki ki bawa 'yar uwarki baki kawai. Maganar nan an gamata tun jiya. Allah Ya sanya mana alkhairi" Jikin Zubaida duk sai yayi sanyi. Mata nawa ta gani a gidan Uwargida wadanda suka ce auren dole ne ya fito dasu daga gidan iyayensu. Allah Yasa Asmau ta iya hakuri dai. Ko sau daya Asmau bata fito daga daki ba. Abinci ma Dijah ce ta kai mata. Amatullah da bata iya komai idan Umminta bata walwala itama a dakin ta zauna. Har su Shemau suka zo yara sun cika gidan amma taki fita sai nanikar jikin Asmau take yi. Col. Ishaq yayi ta kiranta ta daure ta dauka tace masa baki ne a gidan yau duk ya cika. Har su Anti Bintu sun zo. "To bazan takuraki ba kije kuyi hira zuwa dare sai muyi magana. Ki gaishe min da Yayata Bintu" Tana ajiye wayar sai kuka. Yanzu da tasan za'ayi mata katanga dashi tafi jin sonsa ma a zuciyarta. Duk bayan dan lokaci kadan sai tayi mata text mai cike da kalamai masu ratsa zuciya. Shemau tazo tayi ta rarrashinta akan ta hakura ta karbi wanda Allah Ya zaba mata. Gudun kada su dameta yasa ta dan sake tana amsa musu idan an sakota a hira. Sunyi aikinsu sun gama zuwa yamma. Washegari kawai ake jira mutanen Shanono su iso. A daren ranar Ainau da bata sami zuwa tayasu aiki ba ta kirata harda kukanta. Ta kira Umma tana rokon kada a hana yayarta wanda take so. Umma dai ta rasa yadda zata yi. Duk sun hade mata kai. Jafar ne ma bai nuna ga wanda ransa tafi so da Asmau ba. Uban gayya ASP Qasim shima sai dare ya kira Asmau. Kana jinsa kasan yana cikin farinciki yace "Asmau kinga ikon Allah ko. Ina sanar da su Baba maganarmu suka ce kawai azo ayi komai. Ina fatan hakan zai karan kwantar miki da hankali kisan cewa komai ya wuce." Zuciyarta har wani zafi take yi don bacin rai ta daure tace "babu komai Yaya Qasim, Allah Ya tabbatar mana da alkhairi" Yaji dadin furucinta "Amin Asmau, goben zanzo nima. Idan sum gama nasu sai mu fara tsara bikin. Sai da safe ko gimbiyata" Ta kakalo murmushi tayi "to sai da safe" ta ajiye wayar ido na cikowa da kwalla. ***** Washegari da wuri gidan ya cika kamar masu shirin biki. Yaya Abu da Anti Lami sun zo, Mama da 'ya'yanta mata harda matar Abdulhalim. Sai Aina'u da Shemau da Sabira. Falon aka share aka tura kujerun baya aka shinfida wani kafet din ko da wurin zaman zaiyi kadan. A bangaren maza ma akwai masu zuwa ta bangaren Hajjo da maigidanta sai Kawu Garzali da abokansa biyu. Ga mazansu Anti Lami da na Anti Bintu. Banda kuma gayyar Alh Adamu. So suke su nunawa dangin Qasim suna son 'yarsu kuma ita din 'yar dangi ce. Tun safe Asmau ta kashe wayarta don bata san me zata cewa Jikamshi ba idan ya kirata. Adduarta kada yazo ana tsakar taron. Yau ma a daki ta zauna sai dai 'yan uwanta su shigo tayata hira. ***** Ana la'asar mutanen Shanono suka iso gidan Alh Adamu. Daga nan suka dunguma zuwa gidansu Asmau. Mota biyu suka ciko da nasu 'yan uwan. Qasim dama ya rigasu zuwa ya sai zauna a cikin gidan idan taro ya watse zaije ganin Asmau gimbiyarsa. Kafin su iso Umma tace Asmau ta tafi gidan Jafar tare da wasu cikin 'yan matan tace kanta na ciwo bazata iya fita ba. Umma tayi murmushi kawai ta rabu da ita. Sauran suka tashi aka jera komai a falon sannan suka koma ciki suna hira a dakin Hajjo saboda yafi fadi. Asmau na kwance zazzabin dole ya rufeta taji hannuwan Amatullah sun rike mata wuya ta baya. Tun jiya taki sakewa itama. Idan ta korata tayi wasa bata dadewa take dawowa wurin Umminta. Murmushi tayi tana kokarin cire hannunwan don rikon ya danyi karfi "Ama sake min wuya mana" Jin tayi shiru yasa ta juyawa sosai. Amatullah ta gani tana kokarin numfashi bakinta a bude. "Subhanallah" ta fada a rude tana dagata. "Ama ki rufa min
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103