Chapter 1
Chapter 1
ABINDA AKE GUDU 🙆🏽 1 Batul Mamman💖 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Daki ne cike da 'yan mata sai hayaniya suke yi. Wasu suna saka kaya wanda ya kasance atampa ce ja mai adon baki, wasu kuwa kwalliya suke yi a gaban madubi. Wadanda basu sami wuri a gaban madubin ba da na jikin hodarsu suke amfani ana ta fentin fuska cikin nishadi. Suna wannan hirar da shewa wata mace da bazata wuce shekaru talatin ba ta shigo da katon cikinta ita ma irin atampar jikinsu ta saka tayi kwalliya daidai gwargwado cike da damuwa ta soma magana. " don Allah kuyi sauri ku fito ku ake ta jira. Umma sai fada take min babu amarya babu kawayenta. Kun dai san tayi ta kashedi akan African time". Wata cikinsu wadda da alama ta gama nata shirin tace "kiyi hakuri Anti Shema'u yanzu zamu fito". "Babu wani yanzu zaku fito. Ina Asma'un?" Ta fada tana dube dube. Can gefen gado ta hango kanwar tata ana rangada mata kwalliya irin ta amare tayi kyau sosai. Kusa dasu Shemau ta koma ta sake nanatawa mai kwalliyar tayi sauri ta gama a fito da amarya. Ita dai Asma'u har yayarta ta gama magana bata ce komai ba saboda kada ta bata kwalliyarta. Wannan rana ce mai matukar mahimmanci a rayuwarta. Ranar kamunta da mutumin da take ganin tamkar babu irinsa a duniya. Har Shema'u ta fara tafiya tayi saurin dawowa da sauri ta sake kai idonta gaban rigar jikin amarya. Daure fuska tayi " duk amaryar duniya idan ana bikinta rama takeyi saboda zulumin barin gida da sabuwar rayuwa banda ke Asmau. Dubi yadda rigar nan ta sake matse ki duk kirjinki ya fito ta sama". Hannu Asmau tasa ta rufe jikinta saboda yadda 'yan uwa da kawayenta na dakin suka maido da kallonsu gareta. Shemau ta cigaba da magana "ki tabbatar abinda zaki yafa ya rufe miki kirji don bani da amsar bawa Umma idan ta fara fada." Daga nan ta fice tana mamakin irin wannan jiki na kanwarta. Dama can ita mai jikin kiba ce.... ****** Farfajiyar gidan ta gama cika da mata inda aka kawata wani bangare da ado irin na gargajiya domin zaman amarya. Ga kujeru da tebura wurin yayi kyau sosai harda turaren wuta na tsinke da na garwashi aka kunna sai kamshi ke tashi. Mai gabatar da taron mace ce ta nemi kowa yayi shiru saboda amarya zata fito. Mai kida ya canza salon kidansa da wanda ya dace da amarya aka fara ita da kawayenta suka fito suna taku daidai. Sunyi matukar kyau da burge mutane da irin salon fitowarsu. Aka dauki tafi, masu hoto kuwa na camera da na waya suka fara aikinsu. Haka suka rinka tafiya har suka karasa inda zata zauna. Autarsu ce Aina'u 'yar kimanin shekaru sha uku a tsaye da mafici irin na kaba yayarta na zama ta soma yi mata fifita a hankali. Hakan ma ya kayatar da mutane. Hajiya Bara'atu dake zaune cikin 'yan uwanta da kawaye har 'yar kwalla sai da tayi. Gashi cikin ikon Allah karo na biyu kenan da zata aurar da daya daga cikin 'ya'yanta. A hankali tace " Allah Ka jikan Alhaji" bai rayu yaga auren 'ya'yansa ba bare yaga jikokin da suka fara tarawa. Daga nan fa aka soma shagalin biki inda aka bukaci dangin ango su fito domin kamun amarya. Suna tahowa Asma'u ta bawa Walida aminiyarta wayarta ta rada mata a kunne ta dauketa a hoto idan ana fesa mata turaren kamun. Walida tace "uhmm su Asmau an iya soyayya. Nasan sarai Abubakar zaki turawa". Asmau ta juya ido tana fari "ke kuwa an hana bawan Allah ganin iyalinsa dole na taimaka masa da hoto". Dariya duk suka yi sannan aka cigaba da biki. ****** Ana soma kiran sallar magriba aka gama taron shiyasa dama Haj Bara'atu ta rinka nanata musu banda African time. Sallah aka tafi a gabatar harda amarya wadda ta gaji sosai. Dakinta suka nufa ita da kawayenta suka yi tasu sallar. Tana idarwa aka fara yi mata tayin abinci, kafin a kawo ta dauki wayarta ta turawa Abubakar hotunan kamu. A lokacin yana tare da abokinsa Qasim. Shi dai Qasim gani yayi Abubukar ya dan matsa ya fara waya. Murmushi yayi don yasan da wa ake wayar. Hira suke yi sosai yana fada mata yadda tayi kyau da kuma rashin jindadinsa da aka hana shi zuwa wurin kamun. Karshen gado ta koma ta rungume waya suna ta hira. Tun ana cewa ta sauko ga abinci har suka gaji suka dena. Ba su suka gama wayar ba sai da ya fara jin kiran sallar isha daga masallacin gidansu wanda suma su Asma'u shi din suke ji. Sallama suka yi tare da alkawarin zai kirata anjima. Tana saukowa daga kan gadon ta dafe cikinta "yunwa nake ji kamar na kwana ban ci abinci ba" Walida ta dan harareta "abincin ai ba jiranki zaiyi Juliet. Ni nayi tsammanin a irin soyayyarki da Romeo din naki baku san yunwa ko kishiruwa ba idan kuna tare". "Nasan ba wani abu ke damunki ba sai tafiyar da rabin ranki Babangida yayi gashi ba kya samunsa a waya sosai" Asmau ta fada cikin tsokana ai kuwa Walida ta jefeta da pillow tana fada. Babangida yaron gidansu Walida ne irin almajiran nan marasa kunya gashi ya kware wurin kaiwa matar babansu gulmar duk abinda take yi shiyasa ta tsane shi. Har kusan daya na dare 'yan matan suka kai suna hira sannan bacci ya dauke su. Wasu akan gado wasu a katifun da aka shinfida a kasa. Cikin bacci Asma'u taji wayarta na kara ta dauka cikin magagi. Tana ganin sunan mai kiran ta wartsake. Cikin taushin murya yace " Asmy na tasheki daga bacci ko?" Sai a lokacin ta kula karfe hudu da kwata na dare sunfi wata daya yana tashinta a irin wannan lokacin dama. Ta dan shafa idanu "babu komai Yayana yau mun so mu makara ma". "To a tashi ayi a nemi kusanci da Allah. I love you Asmy." Murmushin da yake so a gareta tayi sannan tace "me too Yayana". Bayan ta ajiye wayar tashi tayi ta fita ta tafi bandaki ta dauro alwala. Nafila tazo ta fara yi sannan ta dukufa istigfari kamar yadda suka sabarwa kansu ita da Abubakar har aka kira assalatu. Sake kira yayi ya tabbatar idonta biyu sannan ya tafi masallaci ita kuma ta tashi 'yan matan dakin ta tayar da tata sallar. ***** Yau ta kama alhamis babu wani taro da za'ayi a gidan sai karfe bakwai da rabi da za'ayi dinner da daddare. Qasim yazo har gida ya sami Abubakar tare da takardar da aka bashi ta canjin wurin aiki da karin matsayi. Abin takaici ana bukatar lallai yaje ya gabatar da kansa a sabon ofishin da aka tura shi a Zamfara kafin litinin mai zuwa. Abubakar ya taya shi murna sai dai sunyi bakincikin bazai sami dinner da daurin auren abokin nasa ba. Abubakar duk ya shiga damuwa Qasim ya rinka kwantar masa da hankali. Abubakar yace "yanzu tunda ka zama ACP Qasim to sai ka nemo mana mata musha biki." Dariya Qasim yayi "wace mata zan nemo bayan kasan albashin dansanda har yanzu bai taka kara ya karya ba." "A dai rinka godewa Allah"
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103