Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 46

Chapter 46

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ke ce?" Ta fashe da kuka tana kallonsa tana tuna wasu lokuta a da. Yayi dan jiki kamar bashi ba. A da Abubakar ya fushi kumari. Gashi duk ya canja alamun yana da sukuni. Kusa da Umma ta zauna a kasa ta gaishe shi tana dan murmushi ga hawaye "Yaya Qasim ai bazan ganeka ba" Yau da Asmau namiji ce babu abinda zai hanashi rungumeta don ya nuna mata tsantsar farincikinsa da ya ganta. Jiya da ta tsaya a Shanono su Inna suka ce dare yayi ya bari gari ya waye ya karaso Kano ji yayi inama bai biya ya sanar dasu ba. Yau dai burinsa ya cika Asmy din Abubakar ta dawo gaban iyayenta. Amatullah ce ta shigo falon tana kira Asmau. Duk da ta sake da mutanen gidan amma haka halinta yake da an dan jima sai ta nemi Umminta. Tana ganinta kuwa zata kama wata sabgar. Gaban Qasim har faduwa yayi da ya ganta. Baya bukatar wani karin bayani ya tabbatar wannan 'yarsu ce wadda rabon haihuwarta ya jefa iyayenta da su kansu cikin rudani. Tashi yayi ya durkusa a gabanta yana shafa fuskarta, muryarsa na dan rawa yace "yaya sunanki"? Tayi masa murmushi irin wanda yake tunawa Asmau da Abubakar idan tayi shi "Safinatu Amatullah Abubakay" Rungumeta yayi kawai hawayen farinciki na fito masa. Muddin yana raye yayi alkawarin kula da ita har karshen rayuwarta. Yana shafa kanta yace "Safinatu nine babanki" Ta dago kanta tana kallon Asmau "Ummi ni babana biyu ne"? ABINDA AKE GUDU🙆🏽37 Batul Mamman💖 Tana gama wayar Ainau ta tambayeta ko waye tace baban Amatullah ne. Ainau ta kurawa 'yar uwarta ido "Yaya Asmau zaki iya yin sati a garin nan kuwa ko kawai mu bi Yaya Yassar mu koma Kano" "Kada ki damu Ainau, irin wannan abubuwan nasan ban fara ganin komai ba ma. Idan ya faru ne yake taba min zuciya na dan lokaci har nayi kuka. Dama abinda ake gudu kenan, ba wai yin a lokaci daya ba, abinda zai je ya dawo bayan kayi. Kinga rana daya a rayuwata ta canja akalar komai nawa." Kuka suke yi duk su biyun Ainau tana bata hakuri "Ku zan bawa hakuri ma da na janyo ake yiwa tarbiyar da Umma ta bamu kallon gazawa. Don Allah kada ku bari taji wannan labarin. Shima Yassar din zanyi masa magana" Anti Bintu tana bakin kofar tana jinsu. Tausayin Asmau ta kara ji ta koma wurin maigidanta. Alfarmar kada su fadawa Yayarta tazo nema sai gashi Asmau tayi wannan tunanin. Sun dauki lokaci a dakin suna magana kafin su dawo falo bisa umarnin Kawu Yusuf. Rokonsu yayi da suyi hakuri da halin tsufa irin na mahaifiyarsa kuma yana fata zasu sake a gidan bazasu takura kansu a daki ba. Sai da suka yi sallah aka zauna cin abinci. Babu wata hirar kirki sai hayaniyar Amatullah. Kowa jikinsa a sanyaye yake. Ganin haka Asmau ta rinka dauko hira duk don ta nuna musu bata tare da damuwa. Su Yassar sun dawo daga masallaci inda suka yi sallar la'asar yace zai kama hanyar komawa. Anti Bintu ta tsayar dashi ya jira a kawo sako da take son ya tafiwa da Umma dashi. Yana zaune a falon Col. Ishaq yayi masa waya yana tambayarsa kwatancen gidan da suke zai zo ganin Amatullah. Yassar ya tashi tsaye cike da mamaki, sannan ya kwatanta masa inda zaije ya jirashi sai yazo ya kawo shi gidan. Anti Bintu ta tambayeshi ko lafiya ya sanar da ita bakon da zasuyi. Murmushi tayi "anya 'yar yazo gani ko uwar 'yar" "Nima tunanin da nake yi kenan Anti. Mutumin ba karamin burgeni yake yi ba. Idan yace yana son Yaya Asmau ai ya gama min komai. Wallahi binsa zan rinka yi sau da kafa". "To sarkin zumudi, daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki" Anti Bintu ta fada amma itama tana fatan hakan ya tabbata. Dan ganin da tayi masa ranar da suka dawo da Asmau ta yaba dashi. "Bari kiga naje bakin layin kada yazo yayi ta jirana" "Ita yayar taku tasan da zuwansa?" "Kai bana jin ta sani, kyaleta kawai Anti kada ta bata lamarin. Ba karamin aikinta bane ta tura masa Amatullah taki zuwa su gaisa. Kuma ai kinga bai dace ba mutum yayi tafiya irin wannan saboda danka" Wannan karon dariya sosai ya bawa Anti Bintu. Lallai Yassar da yana da iko tuni zai bawa sojan nan auren yayarsa. Yana fita ta shiga ciki suna daki ana ta wanka saboda zafin gari. Ta tarar Asmau ta shirya cikin wata doguwar riga mara nauyi shudiya ta yafa karamin mayafi fari a kanta. Anti Bintu tace ta taso ta tayata hadawa bako abinci don duk 'yan matan gidan suna Islamiyya. Tashi tayi tabi bayanta ta bar Ainau da yaran. Da yake akwai sauran abincin rana salad kawai ta sake hadawa ita kuma Anti Bintu ta hada zobo mai sanyi. Tray din abincin ta dauka ta shiga falo, ko tsakiyarsa bata kai ba taji sallamar Yassar da ta Jikamshi. Sai dai murya ta biyun ce tafi daukar hankalinta har ta daga kai suka hada ido. Sanye yake cikin kayan aikinsa da hularsa rike a hannu. Yayi kyau sosai. _Innalillahi wa inna ilaihi rajiun_ ta fada saboda tsabar kaduwar da tayi hannuwanta suna rawa tana neman sakin tray din a kasa. Wani irin kallo ya bita dashi yana wani kashe ido. Sai kuma ya karasa gabanta ya karbi tray din da yake tangal-tangal ta kasa rike shi da kyau. Sai da ya ajiye shi a kan centre table din falon ya sake dagowa yana kallonta kamar wadda aka kafe a wurin yace "Duk murnar ganina ce haka tasa kika kasa motsi?" Juyawa tayi bayanta taga Anti Bintu tana murmushi,daga bakin kofa kuwa Yassar ne bakinsa ya kusa zuwa keya don dadi. Ji tayi kamar ta make shi. Mamakin ganinsa ta yi sosai har ta kasa hada wata kalma a bakinta. Shi kuwa ba karamin dadi yaji ba da ya ganta. "Kinyi tunanin wasa nake yi da nace zan zo? Gashi ko wurin zama baki bani ba sai aikin daukar miki tray daga shigowata" Da sauri Yassar ya nuna masa kujera. Anti Bintu ta karaso ta zauna suka gaisa amma har lokacin idonsa na kan Asmau da ta tsaya kawai tana kallonsa. Bata taba kawowa da gaske zai zo ba kamar yadda ya fada a wayar. Ji tayi ya sake shiga ranta har abin yana bata tsoro. "Yaya hanya? Yassar na shirin tafiya yace ka shigo gari" Sai sannan ya maida hankalinsa ga Anti Bintu yana magana da alamar damuwa a fuskarsa "Waya muka yi da Ummin Safina sai naji kamar tana kuka kuma taki fada min abinda ya sameta. Shine kawai nayi deciding na taho don ko na zauna bazan iya aikin ba" _Subhanallah_ ta fada a zuci. Shi kuwa me yasa yake haka ne. Baya jin komai idan ya fadi magana a gaban mutane. Kallonta Anti Bintu tayi sai taji kunya. Kada tayi tunanin ko ta fada masa abinda ya faru ne. In'inar karfi da yaji ce ta kamata "Uhmmm...dama...da.....lokacin...kai" ta rasa karyar da zata yi ma. Shi kuwa ya zuba mata ido kamar bai san da mutane a wurin ba. Anti Bintu tayi gyaran murya don ta kula hankalinsa yayi

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});