Chapter 55
Chapter 55
Idanu suka koma kan Umma. Daga yadda Alh Adamu yake magana ta tabbatar yana so su amince tunda har ya zo gidan da da kansa. Mutumin nan yayi musu gata fiye da tunanin mutane. Ta dauke shi tamkar dan uwanta bazata iya bijere masa ba balle kuma Asmau. "Nima dai bani da zabi sai abinda kuka yanke. Wannan aure idan ya yiwu ba karamin dago mata martaba zaiyi ba a idon jama'a sai dai muyi fatan alkhairi. Shi kuma Abubakar Allah Ya gafarta masa" ta kare da guntun hawaye. Da yana raye duk wannan abin bazai taso ba. Mama ma sai ta soma kuka duk kuma zukatansu suka raunana. Alh Adamu yace "zaku fara ko?" Da yaga sun nutsu ya ce "tsakani da Allah ni naso nasa Abdulhalim ya nemi aurenta domin kare martabarmu gabadaya. Sai na bari ta dan kara kwana biyu ashe rabon Qasim ce. Zan sanar dashi su zo jibin. Idan yaso sai mu kira dangi na kusa azo ayi komai da wuri. Iyalin Mal Musa sunyi mana abinda bazamu manta ba tunda suka bari dansu ya nemi auren tamu 'yar." Sunyi ta tattaunawa akan maganar karshe mazan suka yi shirin zuwa masallaci. Aka bar su Mama suna kara shawara akan kamar yaushe ya kamata asa auren idan dangin Qasin sun nemi asa rana da wuri. ABINDA AKE GUDU🙆🏽41 Batul Mamman💖 Asmau tana can gidan Zubaida suna hirarsu bata san wainar da ake toyawa a gidansu ba. A cikin hirar ne ta fada mata zancen Qasim da Col. Ishaq. Zubaida taji dadi sosai "kinga yadda Allah ke juya lamarinSa ko. Shawarar zan baki ki yarda kiyi aure amma ki zabi wanda zuciyarki tafi so. Ni shaida ce akan irin abinda Qasim yayi da kika bata to amma nafi danganta hakan da rike amanar Abubakar da yayi. Bansan gaskiyar lamari akan menene a zuciyarsa ba yanzu. Ma'ana soyayya ce ko tausayi. Shi kuwa sojan nan dole na yaba masa. Duka duka yaushe ya sanki amma yake sonki da aure" "Ba kya tunanin nan gaba matsala ta taso ko a kaina ko akan Amatullah" "Hmmm Asmau kenan, ke kike da goben da har kike tunanin matsala? Yadda Allah Ya daidaita miki lamura yanzu, idan har wani abin ya taso a gaba Shi din dai zai mana magani. Kada ki manta nima ba 'yar aure bace amma Allah Ya hadani daku gashi babu wanda ya taba yi mim gori. Auren ma Hajjo ce ta hada. Zamana nake lafiya na manta da kazantar da na taso cikinta. Yadda na hadu daku da yardar Allah itama zata hadu da mutane nagari a rayuwarta" Asmau ta sunkuyar da kanta kasa hawaye na taho mata. Duk matar da tayi zina ta gama cutar abinda ta haifa. Sai dai idan an hadu da mutane na kwarai. Kuma duk da haka haifewar itace tafi akan zubar da ciki wanda yake daidai da kisa idan an busawa jaririn rai. Mace sai ta sami rahmar Allah idan ta rungumi kaddararta ta bawa abinda ta haifa tarbiyar da ta dace da addininmu. "Ki kara hakuri da rayuwa Asmau. Haka Allah Ya tsara miki. Ke kika zama ishara ga masu hankali wadanda idan sunji labarinki zasu san cewa biyewa sharrin yanar gizo da son zuciya halaka ne. Uwa uba babu wani alkhairi da yake tattare da shiga groups din nan na whatsapp ko facebook masu yada alfasha." "Nagode Antina ta kaina. Allah Ya raba lafiya mu sha suna" Dadi Zubaida taji da taga Asmau ta dan sake. Amatullah tana tsakar gida suna wasa da yaran Zubaidan. "Tashi mu soya wainar fulawa" Asmau ta zaro ido "yaushe muka gama cin abinci?" Cikinta ta shafa "bani nake so ba kaninki ne ko kanwa" "To kala masa sharri saboda bashi da baki. Ina fulawar take na hada?" Ta fada tana tashi. Ranar dai sun wuni suna hira kuma taji dadin shawarar da Zubaida ta bata. Duniya kenan, Zubaida da ta tashi a matsayin 'yar magajiyar karuwai gashi Allah Ya sauya mata rayuwa. Sai bayan magariba Asmau tayi shirin tafiya. Dama Jafar yace zai dawo daukarta sai ya kira yace ayyuka sun masa yawa. Nan kuwa bata san suna can gidansu ana maganar aurenta bane. Zubaida ta sake yi mata tuni akan lallai kada ta bari dama ta kubuce mata. Ta amince tayi aure "Ni na kula sojan nan ba dai iya nuna kulawa ba. Zuwanki nan kunyi waya sau uku." Murmushin Asmau ya tabbatar mata da zarginta na cewa shi take so. Har kofar gida ta rakata suka tafi titi suka shiga adaidaita sahu ita da Amatullah suka tafi gida.. Abin mamaki tana zuwa ta tarar da Anti Bintu tazo da yaranta wai zasuyi weekend. Tayi murna sosai. Amatullah ma ta ganesu saboda haka ta saki jiki ana hira. Umma tace idan ta huta tazo dakin Hajjo tana son ganinta. Anti Bintu Asmau ta kalla tana dan murmushi, ko dai ta fadawa Umma zuwan Jikamshi Zaria ne. Karshenta maganar aure ce. Ta riga ta kudiri niyar bin shawarar Zubaida. Zata tsananta addua ta amince da Col. I M Jikamshi. ***** Ko kayanta bata cire ba da ta shiga daki Jikamshi ya kirata kamar yasan tunaninsa take yi a wannan lokacin. Daukar wayar tayi tare da yin sallama. Shima lokacin yana gida ya tasa laptop a gaba yana kallon wasu hotuna da ya dauki Amatullah. Yana son yarinyar nan, ko babu komai ta dauke shi uba sannan gashi tayi sanadiyar hadashi da Umminta. Safinansa akwai shiga rai. Sallamar Asmau ce ta katse masa tunani ya amsa mata cikin daddadar muryarsa. "Matar Jikamshi kun dawo gida lafiya?" "Lafiya kalau" "I miss you so much" "Duk wayar da muke yi tun safe?" Yayi yar dariya "yanzu ke hirar waya ta isheki. Ni nafi son na ganki a gabana. By the way lokacin da na baki fa yayi. Anyi sati daya ya kuka yi da Qasim?" Shiru tayi domin kuwa bata sami biyan bukata ba. Tayi kokarin nuna masa ya hakura da zancen aure sai ya rinka danganta abin da ko tana gudun aurensa saboda tunanin Abubakar ne. Karshe yace mata ta jira nan da lahadi komai zai zo karshe. Col Ishaq yace "ya kika yu shiru? Kada kice min bakiyi komai ba." Sautin muryarsa kamar baiji dadi ba tace "ka kara hakuri yace na jira zuwa ranar lahadi idan yazo kamai zai zo karshe" "Ban fahimceki ba, komai zaizo karshe kamar yaya?" Asmau kanta bata gane abinda Qasim yake nufi ba "nima dai haka yace min" Col. Ishaq ya tashi daga kashingidar da yayi "look Matar Jikamshi, ni mutum ne kaifi daya. Idan kina jin nauyin fada masa saboda kusancin families dinku ni zan fada masa da kaina. Tunda naga ya cigaba da yi min text da waya nasan bai san alakarmu ba. Kinga kashe wayar kawai bari na kira shi na fada masa Ishaq da Asmau suna son juna don Allah ka nemi wata" Bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba "yanzu don Allah sai ka fada masa haka"? "Kin dauka wasa nake yi, yara ne suke da lokacin wasa da soyayya." Tace "kayi hakuri zuwa lahadin please" Yadda take magana duk ya kashe masa jiki. Zai iya hakuri amma zuwa sunday kawai. Daga nan kuwa to sai dai ayita ta kare. Shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103