Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 30

Chapter 30

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

daga yanayin maganarsu ta kula a buge suke. Wanda ya danfi tsahon yayo kanta kamar zai doketa dayan yayi saurin rike masa hannu "Haba Annur, duba da kyau mahaukaciya ce. Tunda Allah Yasa bamu tabata ba kawai zo mu ware". Mai suna Annur ya ja tsaki "da ka barni na mareta. Haka kawai zata janyo mana makara a wurin party din. Sai an gama zabe fine chicks din" Ciwo ne ya sake kwasarta tayi kasa tana rike baya. Jajayen idanunta da suka rine don kuka ta daga tana kallonsu tace "don Allah ku taimaka min" Wanda ya hana a mareta yace "kai Annur it seems matar nan haihuwa zata yi". "Gaddafi bazan tsaya a wurin nan ba. Kaima kasan yanzu haka an fara nemanmu a gida. Allah Ya kawo wani amma ba mu ba. " Da sauri yaja hannun abokinsa suka shiga mota. Gaddafi ya leko da kansa ta taga yana kallon Asmau kwance a kasan gefen titi. Motoci basu da yawa saboda har lokacin goma na safe bata yi ba. Gashi titin fita gari ne. Annur ya fizgi motar da gudu Gaddafi yana rokonsa da su taimaka ko wane gari suka gani su sauketa a nan wani ya kaita asibiti. Tsaki da zagi Annur ya rinka yiwa abokinsa kafin ya juyo da motar suka dawo inda take. Ransa a bace yace Gaddafi ya shigo da ita. Kuma ya zauna a baya tare da ita saboda kada ta kai masa duka. Shi duk saurinsa ya isa party din abokinsa da za'ayi a Jos batare da sun sami matsala a hanya ba domin kuwa ko license na tuki basu dashi. Da sauri Gaddafi ya taimakawa Asmau ya shigar da ita motar. Ciwo ya fara tsananta a gareta sai gumi take yi. Annur ya soma yiwa Gaddafi magana da turanci "Tun farko da nasan haka zaka yi min da ban ce ka raka ni Jos dinnan ba. Amma babu komai zanyi maganinka. Hmmm yau 'yan matan Jos suna da manyan baki" ya karasa maganar yana wata shu'umar dariya. "Kayi hakuri Annur ni kaina bansan meyasa ta bani tausayi ba. Ji fa yadda take gumi ko magana bata iyawa. Allah Ya tsinewa wanda yayi mata cikin nan dai" Ciwon taji ya lafa mata ta kallesu tayi dan murmushi. Ga dukkan alamu Yassar zai girmesu duk su biyun. Ita ma turancin tayi musu wanda hakan yasa hankulansu dawowa gareta "Wanda yayi min ciki ya rasu fatana Allah Ya jikansa. Ku kuma ina yi muku fatan shiriya daga Allah kada ku fada mummunan hali nan gaba." Annur ya juyo kamar ba shine yake tuki ba yana kallonta da mamaki dan sauran mayen da yake duk ya tafi "wai dama ke ba mahaukaciya bace. Gaddafi kaga ka dauko mana masifa ko? Ke police ce ko 'yar mafiya?" Kasa bashi amsa tayi saboda ciwo. Yana maida kansa titi saura kadan ya bugawa wani. A haka ya cigaba da tukin Gaddafi yana yi mata sannu. Sun isa wani gari yayi kokarin tsayawa su sauketa sai ya kula da 'yan sanda a gefen wurin. Dolensa ya sake taka mota yana ta sharara gudu. Basu tsaya a ko'ina ba sai da suka shigo garin Jos. A wannan lokacin ba karamin tausayin Asmau duka su biyun suke ji ba. Wai dama hake ake nakudar gaske ba ta fim ba. Idan taji ciwo tana addua sai taji suna tayata suna yi tare. Idan ka matso kusa da motar sai ka zata duk su ukun suke nakudar, sai sharba gumi suke yi kamar babu AC a motar . Bakin gate din wani asibiti da yayi musu kama da na gwamnati suka tsaya. Sai da Annur ya taimakawa Gaddafi suka fitar da ita daga motar. Tsoronsu daya kada a kamasu ayi tunanin ko sato ta sukayi ko suna da alaka da ita. Cikin tsananin jin ciwo Asmau ta tambayi sunansu suka fada mata. "Bansan daga ina kuke ba amma ina muku fatan alkhairi da shiriya don nasan iyayenku ba rayuwar da suke yi muku fata ba kenan. A duk inda kuke ku rinka tunanin lahirarku. Nagode sosai." Daga haka ta lallaba ta karasa bakin gate din. Wannan karon sai da Gaddafi yayi da gaske Annur ya ja motar suka tafi. Kasa daga kafarta tayi taji kamar zata fadi wata mata mai uniform din masu shara da wanke bandaki ta tareta daga baya tana yi mata sannu. Daga nan bata san da yadda aka shigar da ita asibitin ba. Ko awa daya bata cika ba Allah Ya taimaketa ta haihu. Tana jin wannan kukan na jarirai taji gabadaya damuwarta ta gushe burinta kawai taga abinda ta haifa. Nurse din da ta karbi haihuwar tace mata kin sami 'ya mace. Asmau tayi murmushi tare da dago kai ta kalli kyautar da Allah Yayi mata tana hamdala. Gata da 'yar Abubakar sai dai babu shi kuma babu iyayensu. Kaddara ta riga fata a kansu. Ba don haka ba da yanzu iyayensu za'a mikawa jaririyar. A wani dan zani aka nade 'yar aka miko mata. Ta zuba ido tana kallonta. Sai kuma kuka ya kwace mata da ta tuna bata da wata hanyar kulawa da 'yar. Ko suturar da zata saka mata bata da ita. Wannan mai sharar tayi mata Allah Ya raya sannan ta fita daga dakin. Ba jimawa ta dawo da wasu tsofaffin riga da zani amma a wanke ta bawa Asmau fuskarta a sake. "Ga wannan akwai ruwa a bandaki ki gyara jikinki sai ki saka. Idan kin fito sai ki fadi wa za'a kirawo a danginki." Asmau kamar kada ta bata yarinyar haka take ji. A rayuwarta bata taba son wani kamar yadda take jin son jaririyarta ba. Tayi godiya ta karbi kayan ta wuce bandakin. Bata dade ba ta fito aka kaita dakin hutu. Wani likita yazo ya dubata yace babu wata matsala amma sai da safe zasu sallameta. Ya bata takardar magungunan da zata siya. Bayan fitarsa mai sharar ta kara dawowa wurinta ta sake tambayarta ina 'yan uwanta saboda a bakin gate ta ganta ita kadai. Ya kamata a sanar dasu ko don su kawo mata abinci da kayan baby. Asmau bata da amsar da ta wuce kuka. Matar sai ta kyaleta ta koma bakin aikinta. Ita kuma ta cigaba da kallon jaririyarta tana bacci. Ikon Allah, yarinyar kama take yi da Mama Yalwa. Asmau sai ta rantse duk 'ya'yan Mama babu mai kama da ita kamar wannan yarinyar. Dama duk sunfi kama da Alh Adamu. Da namiji ta haifa dama sunan Abubakar zata saka masa. Amma tunda mace ce zata saka sunan mahaifiyarsa kamar yadda suka yiwa juna alkawarin sai sun sakawa 'ya'yansu sunayen iyayensu. Da wannan tunanin ta danyi murmushi. Babbar matsalarta yanzu bata san ta ina zata fara ba? Bata da komai bata da kowa. Sannan bata san irin tarbar da za'ayi mata ba idan ta koma gidansu. Wannan tunanin ya isheta ga kudin asibiti duk da na gwamnati ne tasan ko yaya za'a bukaci ta biya kudin wani abin. Hakan ne yasa tana ganin duhun dare yayi ga cikinta kamar anyi mata yasa don yunwa ta kwance dankwalinta ta goya jaririyar da shi sannan ta zura hijab dinta tayi waje. Gara ta gudu tun kafin ace ta kawo kudin da tasan bata da su. Ta kusa karshen

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});