Chapter 15
Chapter 15
taka.( A labaranmu na soyayya muna yin wannan kuskuren duk mu saka cousins ko 'ya'yan riko sun gama tabe taben jikin juna duk da sunan 'yan uwan taka sannan daga baya mu kulla soyayya tsakaninsu). Aya ta ashirin da uku a suratun Nisa'i ta iyakance mana su waye muharramai. Kuma _An karbo daga Ma'qal ibn Yassar yace Manzo SAW yace: ya fiyewa dayanku a buga masa kusa a kansa da ya taba jikin macen da ba muharramarsa ba.At-Tabarani ya rawaito shi, Sheik Nasiruddeen Albani ya inganta shi a Sahih Jaami'."_ Wani kallon raini suka rinka binta dashi tunda dai ga hujja ta basu. Yaya Abu tace da Kamilu " Kai, daga yau babu ku duka babu wadannan 'ya'yan gwal din." Bara'atu dai kyalesu tayi ta wuce tana addua'ar kammala gininta su huta da wannan masifa. ABINDA AKE GUDU🙆🏽13 Batul Mamman💖 Tare suka koma gidan Kwamishina sai dai su Mama har sun wuce asibiti. Sai wuraren shadayan dare Mama ta kira Umma bayan taga missed calls dinta take sanar da ita an kwantar dasu asthma din Abubakar ce ta tashi. Gari na wayewa Shemau ta hada abincin safe harda mutanen asibiti. Ita da Umma suka tafi asibitin su Asmau kuma suka wuce makaranta. Sai bayan la'asar da zasu kai abincin dare duk da ana kaiwa daga nasu gidan Umma ta hada 'ya'yanta gabadaya suka tafi asibitin. Jikin Asmau a sanyaye suka shiga dakin saboda ba karamin rudewa tayi ba da ganin halin da Abubakar ya shiga. Bayan an gaisa kowa yayi masa sannu ya amsa banda na Asmau. Da farko ta zata baiji ba ta sake maimaitawa. Wannan karon harararta yayi amma ita kadai ta kula da hakan. Bata gane dalilinsa na yin hakan ba amma bata ji dadi ba har suka tafi bata sake magana ba. Sai da yamma aka sallame shi washegari. Nan ma da suka zo karatu yana falo ta sake yi masa sannu yaki amsawa har sai da Qasim yayi masa magana. "Abubakar ana yi maka sannu baka ji ba" Hamma yayi ya gyara kwanciya batare da ya amsawa Qasim ba. Da dan murmushi Qasim yace "jikin nasa da sauki . Ke ce Asmau ko?" Kanta a kasa saboda abinda Abubakar yayi mata tace "eh" tare da mikewa ta tafi masallaci. An shafe sama da wata biyu Abubakar baya amsa gaisuwar Asmau. Dama can ba wata hira suke yi ba. Abin yana matukar damunta sai dai ta kasa fadawa kowa. Ranar lahadi da yamma tana dakinsu Yassar ya shigo ya ganta tasa littafi a gaba tana kuka. Baice mata komai ba ya fita ya fadawa Umma. Tasowa tayi ta shigo dakin da kanta. "Me ya sami Idon kukana kike sana'ar a daki ke kadai" Littafinta ta mikowa Umma na Physics. Assignment ne kuma duk lissafi ko daya bata yi ba. "Tun dazu nake yi na kasa amsa ko daya. Kuma malamin duka yake yi." "To shine kike kuka kuma saboda kinfi kowa ruwan ido, uhmm? Kinga ni da yayyenki babu wanda yayi physics. Idan kuma kin amince na koya miki gobe kici kafi-zero shikenan" ta fada da dariyarta. Murmushi Asmau tayi tana sake duban littafin. Umma tace "kije Abubakar ya koya miki shine dan science a gidan Mama." "Umma ai gara naci zero din. Ni da ko gaisuwata baya amsawa idan naje nasan bazai kulani ba" "Asmau bana son karya. Baban nawa ne baya amsa gaisuwarki? Jiya da yazo ba ke nasa kika dafa masa indomie ba. Ko dai wani laifin kika yi masa?" "Kila kunyarki yaji amma da gaske tun kwanciyarsa a asibiti ya tsaneni. Kuma ni banyi masa komai ba". Umma ta dan kalli Asmau sannan ta fita. Abubakar yaron kirki ne kila Asmau tayi masa laifi ne ko kuma dai wani rashin fahimta suka samu. Ko ma dai meye bazata bari yayi nisan da zai shiga tsakaninsu iyaye ba. Wayarta ta dauka ta kirashi. Tayi sa'a yana gida tace yazo tana son ganinsa. ***** Dakin Mama yaje ya fada mata Umma na kiransa. Plate din da take shan kankana ta ture ta tashi. "Jirani muje tare jiya naji Aina'u tana ta tari. Tun dazu nake tunanin zuwa duba ta." Tare suka tafi suna 'yar hira a hanya. Umma taji dadin ganinsu su biyun. Sun dan taba hira ta kwalawa Asmau kira. Tana fitowa da taga Abubakar sai da gabanta ya fadi...ba dai Umma kiransa tayi akan abinda ta fada ba? A kasa ta zauna ta gaishe su. Umma ta lura tabbas bai amsa ba. Kuma bai dade da gama tsokanar Aina'u ba. Idon Umma akan Asmau tace "dazu da nace kije Abubakar ya koya miki assignment me kika ce min"? Cikinta har wani kullewa yayi ta daga kai suka hada ido ya harareta. Da sauri ta sauke kanta "Uhmm, uhmm, babu komai". Mama ta kallesu duk su biyun. Asmau a tsorace, Abubakar ya hade fuska. "Ni kun batar dani Umma, me ya faru?" Umma ta sanar da ita abinda Asmau ta fada da kuma wanda ta kula dashi a wurin. Duk su biyun Abubakar suka zubawa ido suna jiran amsarsa. Dariya suka bashi ya mike tsaye " ni bata yi min komai ba. Bari na koma gida dama aiki nake yi." Mama ta daure fuska "kaga abokan wasanka a nan ne, zauna ka fadi me ya hadaka da kanwarka. Ni bazan lamunce da gaba cikin 'ya'yana ba. Ku da su Asmau duk matsayinku daya a wurinmu." Ita dai Asmau sai satar kallonsa take yi a tsorace. "Mama kin tuna ranar da na sami attack har na kwanta a asibiti? Yarinyar nan fa tana cikin masallacin. Na kasa dauko inhaler a cikin aljihun wandona saboda yadda nake ji nayi ta nuna mata kuma ta gane wai sai ta fita kiranki. Da baki zo da wuri ba shikenan fa". Umma da Mama sai dariya shi kuwa da gaske yaji haushi ya dubi Asmau itama shi take kallo. "Da na mutu a lokacin idan ba fatalwa zan rinka yi miki ba." Wannan karon itama sai da tayi murmushi ganin ya dan saki fuska. Mama ta janyota jikinta "Me yasa baki bashi inhaler din ba Asmau?" Idonta ne ya cicciko da hawaye. Umma tace " oh ni Bara'atu yarinyar nan ko baure bazai nuna mata zuba ba. Ke baki da aiki sai na kuka daga tambayar fatar baki." Mama ce ta lallaba Asmau muryarta na rawa ta kalli Umma. "Ba cewa kika yi haramun bane mace ta taba namjin da ba muharraminta ba. Har a islamiyya duk ana fada mana. Da na taba shi nasan fada zaki yi min sannan a rubuta min zunubi shiyasa na kira Mama". A take Abubakar yaji wani irin yanayi game da Asmau. Shi kan shi yasan bai dace ace yana fushi da ita ba amma abinda ta fada yasa yaji ta sami wani matsayi a wurinsa. Ashe abinda tayi, tayi shi ne don bin umarnin addininta. A yadda yake matashi mai tsantseni wurin addini yana son mutane masu kiyayewa. Yanayin kallon da yake mata ya canza zuwa sakin fuska "dauko littafin muje na koya miki kinji kanwata Idon kuka." Sai da suka dara gabadaya sannan Umma tace "Asmau addinin musulunci yayi mana iyakokin da musulmin kwarai bai dace ya tsallakesu ba. To amma akwai sassauci akan abinda ya zama lalura. Kinga a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103