Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 98

Chapter 98

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na kujera ne" Hannu ta kai zata tureshi ya sureta gabadaya sai kan gadon yana fada mata irin yadda yayi kewarta. ****** Washegari da kyar ta iya tashi ta shirya cikin wani riga da zani na atampa. Jikamshi yana makale da ita a dakin kamar zata gudu. Motsi kadan sai ya hau shafa mata ciki. Ita kuwa idonta na kan agogo tana tunanin fita daga dakin su gamu da Hajiya. Kai hatta Bilkisu ma kunyarta take ji. Ganin duk ta damu yasa yaje ya duba Hajiya tana daki ya fadawa pAsmau. Da sauri ta fita taje falo ta zauna dama bata so kowa yaga fitowarta daga dakinsa. Da Hajiya ta fito tana kallon Asmau ta kula da bala'in kunyar dake tattare da ita. Shima ya fito lokacin banda murmushi da kallo da yake bin Asmau dashi babu abinda yake. Sunyi breakfast Asmau duk a takure gaban surukar da ta gama ganin rashin kunyarsu. Hajiya tace "idan kun gama sai ku tafi gida saboda Safina ko. Zan sa a nemo miki mai tayaki aiki idan ba'a samu ba sai Bilkisu ta dawo nan wurinku saboda ta taimaka miki" Suka yi shiru kawunansu a kasa. Zancen su tafi gidan ne yasa su jin kunya. Wato taga abin nasu ba mai karewa bane gara su koma gidansu. Zancen Bilkisu kuwa cewa yayi gara a samu mai aikin saboda baya son a bar Hajiya ita kadai. Bilkisun ce kawai a gabanta yanzu. Suna sallar azahar suka fito Hajiya ta zuba mata abinci wai ya ishesu har dare kada tayi girki. Sai godiya take da yiwa wannan dattijuwa addua da fatan alkhairi. Yaushe zata manta da ranar da suka fara haduwa wanda tun lokacin Haj Lubabatu take kyautata mata gashi bata kyamaci aurenta da danta ba. Tayi tunanin gida zasu wuce sai taga yayi hanyar Hotoro. Dadi kuwa ya kamata sai murna zata ga Umma. Lokacin da ya dena mata magana tana ta kewar mahaifiyarta amma ta kasa fada masa zata gida. Ya lura da murnarta har ya tsokaneta ko a nan ma zasu kwana ne su sake yiwa baby kani ko kanwa. Murmushi tayi, Jikamshi bashi da dama. Umma da Hajjo sunyi murna da zuwansu sosai. Sai da Umma ta lura da ramarta to a gaban idon suruki sai ta kasa tambayarta me yake damunta. Tsoronta kada ya zamana gori ake mata tasa abin a rai. Don kuwa bayan sun dawo daga Yankari sunje Jikamshi inda wasu cikin 'yan uwansa mata suka fada mata magana son ransu. Sun ji amsa kuwa daidai dasu daga bakin Jikamshin Asmau. Ranar tasha kuka sosai da kansa ya kira Umma yace ta tayashi rarrashinta. Ido irin na manya Hajjo tace "ya naga kina wani kyalli ne Asmau ga 'yar rama kinyi. Nasan dai kina tare da wannan sojan ba kewarmu kike ba" Col. Ishaq da Umma suka yi murmushi ita kuma Asmau ta fada kan Hajjo tana dariya. Tana fadawa ya tashi da sauri don ya manta Umman na wurin yace "wane irin ganganci ne haka don Allah kiyi hankali da jikinki" Kunya ta kamata da su Umma suka soma kallonta. Hajjo tace "Ishaq ko dai abinda nake zargi ne? Naki fada ne dai ko ba hakan bane na tayar muku da hankali" Asmau ta tashi ta fita daga dakin da gudu. Umma ma kunyar taji sai kace wata 'yar fari ta tashi ta bar dakin. Hajjo tace "Alhamdulillah kaga ikon Allah. Allah Ya kara hada kanku Ya kareku daga sharrin makiya da mahassada" idonta fal hawaye yana cewa amin tana addua. A dakin Umma Asmau ji tayi Umman ta shigo ta rungumeta. Hawayen farinciki take itama "Alhamdulillah ala kulli hal. Kinga yadda Allah Ya dubi zukatanku da taimakon da kuka yi niyar yiwa juna Ya baku abinda zai kara inganta zamanku. Amma dama ba cewa akayi bazai taba haihuwa ba?" Asmau tana nata hawayen ta labartawa Umma bayanin da yace likita yayi masa ba tare da ta fadi matsalar da suka fuskanta ba a dalilin cikin. Tasha addua a bakin Ummanta. Sannan tace duk abinda take so ta fada mata. Dole ne su taya Col. Ishaq tattalin abinda yafi so a rayuwarsa. A nan suka yi sallar laasar sannan suka wuce gida. Kulawa kam Asmau tana gani a wurin Jikamshinta sai godiyar Allah. ***** Tana zaune a dakin da suke girki duk hayaki ya bude ta taji sallama. Mai sallamar yayi ta yi ta tashi rai a bace ga bakincikin itacen yaki kamawa ga takaicin lokacin girkin na kurewa yanzu fitsararriyar yarinyar nan zata zo ta sakata a gaba da rashin kunya. Fuska a daure ta bude karamin gate din tana kallon mutanen su biyu. "Don jaraba kuyi ta sallama kamar kuna bin mutane bashi. Me kuke nema?" Daya cikinsu yace "ina Gidado?" Tana ta harare harare tace "kana magana da Zinaru ne uwar Gidado." Dayan ya bata wata takarda "gashi daga Hajiya Zulaiha lallai ku tashi daga gidan nan da sati biyu ko a hadaku da hukuma" Zinaru ta soma raba idanu. Abinda da ake gudu ya faru. Idan suka tashi ina zasu je. Yadda ta tsani rayuwar kauyensu ta dauko tilon danta ta gudo yanzu ana neman a mayar da ita duk tsahon shekarun nan. Sakin fuska tayi harda murmushi "Ku dena ambaton Haj Zulaiha nasan bazata koremu ba. Wasu ne dai suke neman shiga tsakaninmu. Hala baku da labari Gidado mijinta ne har yau. Ai ba rabuwa suka yi ba. Sabani ne irin na masoya" Wanda ya bata takardar yace "kinga ki bashi sakon nan. Lallai ne ya aiko mata da takardarta kuma ku bar gidan nan. Idan ba haka ba zaku ji sammaci daga kotu" Zinaru na kallo suka tafi tace "shegu masu karawa wuta fetur." Ciki ta koma ta tarar da Amarya tsaye a wurin girkin tana ta wani jijjiga jiki tana bata rai. Zinaru ta shigo ta dan rakube a gefen bango. Amarya tace "yanzu ko wutar baki hada ba bare ki dama min kunun. Idan cikin nan ya zube kwarankwatsa dubu sai na fadawa Baba ya karbe shagon da ya bawa Gidado. Ku haka kuke rayuwa ne shi malalaci ke kuma sai dai aci banza. Anjima kadan zani gida ni na gaji da wannan auren miji babu abinda ya iya sai bacci da shaye shaye" Gaban Zinaru ya fadi. Yanzu dan shagon da Baban Amarya ya basu Gidado ke kasa gwanjo a kasuwa idan ya ga damar fita idan suka rasa shi ai tasu ta kare. Tun yaushe suka cinye jarin kayan miyarta shiyasa bata fita sai aikin Amarya da dan cikinta. Tana dogon tunanin sai ga baban Amarya. Dama da wuya yayi kwana uku bai zo ba. Ita kadai ce 'yarsa yake ji da ita kamar rai. Zinaru tayi wuki wuki don bashi da mutumci ko kadan. Ko sallamarsa bata gama amsawa ba ya banko kai cikin gidan. Don abin kunya harda kai gwiwa kasa tana gaishe shi saboda ta girme shi ya amsa yana shan kamshi. "Ina shi yaron nan yake? Yau kwana biyu bai bude shago ba. Idan baya so ne sai na bawa wani ko na bayar haya" Amarya ta kwabe fuska "dama yaushe zai zo Baba. Bashi da aiki fa sai na shaye shaye tun jiya bai san inda kansa yake ba. Ga amai ya

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});