Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 94

Chapter 94

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

lokacin cikin kankanuwar murya tace *Alhamdulillah, I am pregnant*" Karfin adduar da yake a lokacin ta hana zuciyarsa bugawa. A hankali ya zame jikinsa daga nata cikin matukar kadawar zuciya ya kalleta. Murmushi take har lokacin hakan ya tabbatar masa ba karya take ba. Ta kula da kaduwarsa tace "nima ban gaskata ba sai da nayi PT dazu. Kaga ikon Allah ko Jikamshina" Bai iya cewa komai ba sai juya wa da yayi a sanyaye ya shiga toilet. Asmau tabi bayansa taji ya rufe da mukulli. Dama tasan wannan labarin ba karamin farinciki zai saka shi ba. Abu daya ne yazo kanta ko alwala zaiyi suyi nafila. Cikin sauri ta tafi nata dakin ta dauro alwala ta sako hijab ta dawo. Ko da ta shiga dakin toilet dinsa a bude yake amma baya nan. Falo taje da abin sallah biyu a hannu nan ma bata same shi ba. Tana lekawa ta taga ta hango yana fitar da motarsa daga gidan. Ta koma ta zauna da murmushi, wato ya tafi fadawa Hajiya. Gara da bai nemi ta raka shi ba ai da taji kunya. Shiru shiru har shadaya ta wuce bai dawo ba. Tana ta kiran wayarsa baya dauka sai daga baya ta ga wayar a daki. Hankalinta ya soma tashi amma bata son kiran Bilkisu ko Hajiya ayi zaton ta kasa hakuri daga miji ya fita. ****** Tuki yake bashi da wurin zuwa. Zuciyarsa ce take zafi har gumi yana karyo masa. Me yasa Asmau zata yi masa haka, yana da tabbacin tana son shi da zuciya daya. Amma waye ya fada mata lallai sai ta haihu zai cigaba da sonta. Ya dade da karbar kaddararsa me yasa ta aure shi idan bazata iya hakurin zama dashi ba. Waye ya bata wannan muguwar shawarar. Waye yayi sanadin rushewar farincinkin da yake bakin kokarinsa wurin ganin ya tabbata a rayuwar aurensu. Gefen titi yayi parking saboda baya ganin gabansa sosai. Zazzafan hawaye ne ya cika masa ido har yake ganin duhu. Ajiye girmansa yayi da mukaminsa yayi kuka, kuka na bakinciki da bacin rai. Kukan rasa mafita ga halin da abar sonsa ta saka shi a ciki. Sai da ya gaji da zaman ya rinka karanto addu'o'in neman sauki sannan ya koma gida. Asmau na zaune a falo a haka bacci ya dauketa. Zuciyarsa ta sake karaya da ya ganta rungume da abin sallah tana bacci ga Amatullah a kusa da ita. Dukawa yayi ya dauketa ya kaita nata dakin ya dawo ya tsaya yana kallon Asmau. Sai da ya daure zuciyarsa ya iya tabata ta bude ido a hankali. Magana taso yi ta kula da ja da kankacewar idanunsa. "Tashi kije ki kwanta" Bai bari tayi magana ba ya shige ya barta a wurin fuskarsa a daure cikin tsananin bacin rai. Yau da gobe tafi karfin wasa. Asmau ta fuskanci rayuwa irin wadda bata fatan wata mace ta gani. Yanayin da taga Jikamshinta ya sha bamban da abinda tayi tsammani. Wannan kadai ya bata amsar shirunsa da fitarsa daga gidan. _ZARGI_ irin wanda Allah Kadai Ya isa Ya wawarewa bawa. Sai dai abin mamaki gane hakan bai sata kuka ba. Ashe kuka wuri yake samu, ashe kuka rahma ne. Hannu tasa ta dafe kirjinta da taji yayi kamar an daure shi tamau ta kashe fitila da tv ta tafi daki. Duhu ta gani alamun ya kwanta sai ta koma nata dakin ta sako kayan bacci ta dawo. Tana kwanciya ashe a kansa ne saboda ya raba gadon ba kamar yadda ya saba ba. Yau a tsakiya ya kwanta. Ji tayi yana kokarin matsawa tayi saurin tashi tana bashi hakuri amma bai amsa mata ba. Bata yi fushin ta bar masa dakinsa ba ta koma gefen gadon ta kwanta. Sai karfe takwas saura mintuna ta tashi a makare. Wayam ta ga baya dakin. Ta fita da sauri motarsa bata cikin gidan. Jikinta yayi sanyi ta koma tayi sallah da ya saba tashinta idan zashi masallaci. Ta shiga dakin Amatullah ta tarar bata nan ga kayan baccinta a kan gado. Dan murmushi tayi ko babu komai bai dena kyautatawa 'yarta ba. Haka Asmau ta yini ranar da kuncin zuciya. Duk bayan lokaci sai ta duba wayarta ko ya kira ko text amma babu ko daya. Haka ta ke zaunawa ta tsara masa kalamai masu ratsa zuciya ta tura masa. Idan ya gani a take yake gogewa. Sai yanzu yake nadamar auren Asmau yana mai nanatawa kansa tambaya daya *cikin jikinta na waye?*. ***** Sati guda suka yi baya mata magana kuma baya shiga sabgarta. Ita kuma tayi alkawarin bazata takura shiba har Allah Ya sauketa lafiya. Daurewa take tana nunawa kamar babu abinda ya faru ta cigaba da yin abubuwan kyautata masa ko da bazai kula ba. Walida ta kirata taji yaya murnarsa da ta fada masa tana da ciki ta shirga mata karya don ta rufawa mijinta da kanta asiri. ABINDA AKE GUDU🙆🏽58 Batul Mamman💖 A daddafe take iya yin komai. Cikin da alama mai laulayi ne domin bata son warin komai ga yawan tashin zuciya. Rashin wadataccen abinci yasa ko aman yazo sai dai tayi wahalar banza babu komai a cikinta. Cikin dan lokaci ta fada. Babu wanda ta iya fadawa damuwarta sai Allah. Kullum sallah take da karatu tana mai tsananta addua da neman mafita. Idan ta damu da yawa ta kira Umma suyi hira taji sauki a ranta. A nasa bangaren Col. Ishaq ba karamin jigata yayi ba da rashin Asmau. Sonta yana nan a ransa amma yana kyamar halin da ta jefa su a jiki. Har yau ya rasa matakin da zai dauka bayan fita harkarta da yayi. Gidan yayi musu zafi duk su biyun. Gado daya suke kwana ya juya mata baya. Haka zata yi bacci tana kallon bayansa tana hawaye. Ranar asabar lokacin sun dauki sati uku a wannan yanayin tana fitowa daga kitchen shi kuma zai shiga daukan cup ya hada tea. Kallon kallo suke yiwa juna ta matsa ta bashi hanya. Yana shiga ya bugo kofar da kafarsa ashe hannunta na wurin kofar ta matse. Ciwo taji har tafin kafarta tayi kara cikin zafin nama ya bude kofar. Hannun ta rike sosai tana fitar da hawaye ta kasa tsayuwa wuri daya don azaba. Mantawa yayi da fushinsa da komai ya kama yatsun nata biyu da yaga ta rike ya shigar da ita kitchen ya sakar mata ruwa. Idonta a rufe tana kuka a hankali. Ciwon bai dameta ba kamar yadda Jikamshinta ya canja mata. Har zuciyarsa yake jin kukan tana bashi tausayi sosai. Ya soma hura mata yatsun amma yana gani har sun fara kumbura. Fuskarta yake kallo itama yau bata kawar da nata idon ba ta zuba masa ido. Yadda ta rame shima haka ya rame. Yana rike da hannun ya kai yatsun nata bakinsa ya saka a ciki. Kallonsa kawai take tana kara sonsa duk da halin da suke ciki a lokacin. Kusan minti uku yatsunta na bakinsa sannan ya cire yace "kinji sauki ko nasa miki kankara" Yaushe rabon da yayi mata magana. Ita da jin muryarsa sai dai idan waya yake. Girgiza kai tayi ta janye hannunta ta tafi. Wani iri yaji, yunwar ma ta fita a kansa sai rudani na rashin sanin yadda zaiyi da Asmau. Dakinta ya

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});