Chapter 95
Chapter 95
bita ya sameta zaune a kasa a kuryar gado tana kuka a hankali. Bai ce mata komai ba ya bude inda take ajiye mayafai ya dauko mata wani kato mai kauri. Tayar da ita yayi tsaya ya yafa mata sannan ya riko hannunta suka fito falo ya dauki mukullin motarsa. Cigaba yayi da jan hannunta har gaban mota. Ya bude mata ta shiga ta zauna sannan ya cewa Mal Sabo idan ya dauko Amatullah ya kaita gidan Ismail. Sai ta kula ya mikawa Mal Sabon wata karamar jaka wadda take tunanin kayan Amatullah ne a ciki. Da ya zauna ya tayar da motar Ismail din ya kira ya fada masa za'a kawo Safina kila ta kwana. Shi kuwa sai murna yace dama yana gida. ***** Barrack dinsu suka je bangaren asibiti. Ita dai binsa take a baya har suka shiga ciki. Wani office ya shiga ya barta a reception. Ba dadewa ya fito yace ta shigo. Hussaini ne a ciki sanye da kayan sojoji amma ya dora coat din likitoci. "Ranki ya dade sai ki zauna a waje kuma? Sir kasan fa ita ce mai hadani da Walida ya kamata ka tayani kamfen" Duk su biyun ya kula babu wanda dan guntun wasansa ya bawa dariya. Shima sai ya ci serious ya koma mazauninsa. Yasan yau abokin nasa a matsayin shugabansa ya shigo. Col. Ishaq ya kamo hannunta da ya matse wanda yatsun sun kumbura faratan kuma sunyi jawur alamar taruwar jini daya har ya fashe ta saman farcen "Doctor a duba mata hannun nan bana so ya zama babban ciwo" Hussaini ya kallo hannun sai ya dauki waya ya kira nurse aka zo suka tafi da Asmau yace ayi mata dressing. Bayan sun fita yace "ai yadda na ganku ne har naji tsoro ko anyi fadan masoya ashe amarya ciwo taji" "Kaga ba batun wasa ina so duk wani test da akeyi a gano ciki kayi mata please" Hussaini ya mike da sauri "Sir ciki??? Iko sai Allah, bashi da abokin tarayya. Lallai Allah maji rokon bayi." Col Ishaq yayi masa wani irin kallo "me kake nufi ne? Kafi kowa sanin matsalata yanzu na fada maka zancen ciki kuma kana murna" "Wannan ai abin farinciki ne da murna. Bari na fada musu ayi test din Allah Yasa akwai. Kai da kaina zanyi mata ma" Ran Col. Ishaq ya soma baci yace "Hussaini bana son wasa. Kada ka manta banda dangina bani da wani amini sama da kai. Kai kadai na fadawa komai game da Asmau kafin na aureta. Sauran a gari suka ji idan har sun sani. After all these years aure kasa da shekara ko wata shida bamuyi ba tace min tana da ciki" muryarsa tayi rauni sosai dauriya ce kawai yake. Zama Hussaini yayi a kujerar da take kallon ta Col. Ishaq hankakinsa a tashe. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Kada kace min zarginta kake yi. Col. Ishaq Jikamshi waye ya fada maka bazaka taba haihuwa ba? Na tabbatar ba ni bane" Maganar ta fara daure masa kai yace "ku likitoci kun iya boyewa mutane zahirin abu sai kuyi ta rufa rufa don kada ku tsorata patient. Ka gwadani ka kuma hadani da likitocin da lalurata ta shafe su. Kowanne sai ya cemin lokaci ne baiyi ba. wane magani ne ban sha ba. Sai gashi Badar ta haihu daga yin aure. Wannan ya tabbatar min ni nake da matsalar. Nine bana haihuwa " Hussaini ya jima yana kallon abokinsa kafin yayi magana "idan ni ko wasu a nan zamu boye maka idan bazaka taba haihuwa ba, asibitocin da kaje a kasashen waje kasan bazasu yi maka karya ba. Babu wanda ya kai bature baro baro. Sai ya fada maka nan da lokaci kaza zaka mutu. Duk wani sakamakonka kana bani copy na ajiye. Babu inda akace bazaka taba haihuwa ba. Dukkansu suna cewa ko dai akwai matsala a mahaifar Badariyya ko kuma wani dalili dai ya hana cikin samuwa amma ba rashin lafiya gareku ba." Col. Ishaq ji yayi ya fara jin zafi. Me Hussaini yake nufi. Wai zai iya haihuwa???. Hussaini ya cigaba "idan wasu zasu boye maka ni bazan bari kayi ta kashe kudi kamar baka san zafin nema ba akan haihuwa alhalin nasan bazaka samu ba. Garin yaya ka yankewa kanka wannan shawarar har kake zargin matarka. Allah Sarki shiyasa naga ta kasa magana da kuka shigo. Bani da masaniya game da Asmau bayan abinda ka fada min amma bana jin zata aikata wannan mummunan aikin gareka. Kada ka manta taga rayuwa a dalilin kuskuren farko. Wallahi ni ka kara tsoratani akan zina. Idan har zaka zargeta duk son da kake mata lallai har a nade duniya fentin zina bazai taba barin Asmau ba. Ya Allah Ka nesantamu daga wannan bala'i " Jikin Col. Ishaq ya gama sanyi kam yanzu. A lokacin da Asmau tayi masa albishir da samun karuwa a lokacin tarihin rayuwarta ta baya ya dawo masa har yake tunanin ko a garuruwan da ta zauna ta cigaba da mugun aiki. Tashi yayi da sauri Hussaini ya dakatar dashi "ka jira nayi mata gwaji a tabbatar" Zama yayi amma jinsa yake a kan kaya. So yake ya ga Matar Jikamshi a jikin Jikamshinta. Wani irin sonta yake ji na daban yana ratsa shi. Gabadaya yaji ya tsani kansa da zuciyarsa da ta raya masa wannan mummunan zargi.. Tana zaune an saka mata bandeji a yatsun Hussaini ya shigo dakin da suke. Nurse ya bawa umarni ta debi jininta nan da nan ya karba ya tafi lab dinsu. Da kansa yayi gwajin har sau biyu ya tabbatar babu karya Asmau tana da ciki. Dawowa yayi yayi mata tambayoyi wanda tana amsawa tana hawaye. Yaji tausayinta sosai sannan suka koma office dinsa. Ko da suka shiga kunya ce ta kama Col. Ishaq ya kasa yi mata magana. Hussaini yana murmushi yace "congrats Sir, uwargida tana da ciki wata na uku kenan. Zan bata appointment idan tazo sai a bata maganunguna ayi scanning domin ganin lafiyar baby. Allah Ya inganta Ya raba lafiya." Col. Ishaq kamar yayi me don murna. Yana cewa Amin ita kuwa Asmau ta fita daga office din saboda kukan da yazo mata. A bakin mota ya sameta bayan Hussaini ya nanata masa lallai yayi kokarin shawo kanta saboda yayi mata laifi. Sun shiga mota sun zauna bata ko kalli inda yake ba. Shiru suka yi yaja motar sai gidan Hajiya. Ta goge idonta sannan tabi bayansa suka shiga ciki. Hajiyan na daki tana kashingide ya shiga da sallama. Ta tashi zaune tana amsawa. Asmau ta tsaya a bakin kofa kawai sai ji tayi ya kama hannunta ya ja har gaban gadon Hajiya. Kunya kuwa daga ita har Hajiyan. Zama yayi a kusa da ita a kasa sai ta fashe da kuka Hajiya tace "lafiyarku kuwa, me kayi mata" Baya son kukan Asmau haka kuma baya son bacin ranta wanda shine ya haddasa mata. Kansa a sunkuye yace "Hajiya daga asibiti muke yanzu, tana da ciki wata biyu" *Alhamdulillah....* Hajiya ta fada sai kawai ta rungumo Asmau jikinta. Abin mamaki kuka ta saka Asmau na tayata. "Waye yace babu Allah? Allah sarkin dukkan mai sarauta. Ubangijin Annabi Adamu tsira da AmincinKa ya kara tabbata ga Annabi Muhammadu SAW. Ban taba fitar da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103