Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 34

Chapter 34

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jiya makociyarmu ce tasha zuwa cetona idan yana dukana. Zinaru kuwa ta tsaneni ta tsani yarana. Burinta danta ya auri wata mai arzikin ya rabu dani. Bata taba masa fada akan abinda yake yi. Tun kafin na haihu nayi yaji sai dai daga bakin kofa Abba ya koroni. Ina cigaba da hakuri ne kawai saboda idan auren ya mutu ba karamar kunya zanji ba sannan gidanmu basa sona. Babu wani dangina da ya taba zuwa gidan nan." Asmau taji tausayin Zulaiha sosai. "Lallai kema kinga rayuwa wadda ta zama izina ga sauran mata. Soyayya da kiyayya duk idan suka yi yawa halaka ne. Allah Ya karemu daga sharrin son zuciya" "Amin" Zulaiha ta amsa tana tashi "kinga aikin da nake yi dashi nake ciyar da gidan nan kuma nasa su Humaira a makaranta. In dai zaki iya zaman amana damu sai mu zauna tare mu rufawa juna asiri". Asmau tayi mata godiya sosai. Zata zauna a gidan amma dole ta nemi aiki saboda kula da Amatullah da kuma abinda zasu ci don bazata zamewa Zulaiha karin nauyi ba. ***** Daga masallci Qasim ya taho Kano. Ya hade cikin kayansa na 'yan sanda kana ganinsa kasan babu wasa. Da ace da wuri ya sami labarin wadda taga Asmau tun a jiyan zai taho. Hajjo da Garzali su ma da sassafe suka shirya zasu fita. Alh Rabe ya tambaya ina zasu je ne, jiya har ya dawo basa nan. Hajjo tace "tafiya ce ta kama mu zuwa Azare, an sami wadda ta ga jikata Asmau." Karara fuskarsa ta nuna bacin rai ya juya ga kaninsa "yanzu kai Garzali idan Hajjo ta makance da son wadanda basu damu da ita ba sai ka biye mata? Bara'atu da iyalinta har wata tsiya ne da za'a damu dasu. Wane irin raini ne bata kawo miki ba Hajjo?" "Wai Alhaji menene matsalarka dasu? Ni tunda nake ban taba ganin abin batanci da sukayi mana ba sai ma wanda muka yi musu" cewar Garzali yana kara karya hularsa. Cikin kuka Hajjo tace "ba laifinka bane Rabe. Ni na bada kofa har ka sami damar takasu ina kallo ban hana ba. Kuma da kake cewa su ba wata tsiya bane to a wurina sun wuce komai. Iyalin dana ne. Dana Shu'aibu wanda kake bi ba. Kuma ka sani daga tafiyar nan in Allah Ya yarda zamu tashi mu basu gidansu. Ka fara nema mana gida kafin mu dawo". Daga haka ta fita Garzali yana take mata baya. Aka Rabe da shiga tashin hankali. Kafin goma na safe sun gama shiri aka kama hanyar Azare. Mota biyu suka yi, daya Abdulhalim ne da Umma, Mama da Hajjo. Dayar kuma ta Qasim tare suke da Jafar , Kawu Garzali da Zubaida wadda jikinta yayi sanyi. Tsoronta bai wuce kada suje su barta a wurin Mamanta ba. Ita ta rinka yi musu kwatance har suka isa gidan. Addua suke yi Allah Yasa su dace a sameta. Zubaida suka saka a gaba sai dai Umma ta kula yarinyar da gaske bata kaunar shiga gidan. Hajjo tace su bata hanya. Ta shiga da sallama sauran na bayanta. Ai tunda matan gidan suka ga bakin dake shigowa tare da Zubaida kallo ya dawo garesu. Na cikin daki ma fitowa suke yi. Qasim ne karshen shigowa kafin kace meye wannan mata marasa suturar arziki sai gudu suke yi suna rufe kofa. Dan sanda a gidansu a irin wannan lokacin ba abin arziki bane. Gashi ya hade rai, kyakkyawar fuskarsa kamar bashi bane Qasim mai barkwanci da yawan wasa. Wata ta tsegumtawa Uwargida zuwansu Zubaida sai gata ta fito da daurin kirji kanta babu dankwali. Da dan sauri ta taho inda Zubaida ke rabe a gefen Umma. "Zuby ina kika shiga tun jiya ake nemanki. Ziza tace min ta ganki da jaka." Ta bi su Umma da kallo "wadan nan fa?" Mama ce ta bata amsa "mu iyayen Asmau ne. Yarinyar da tazo gidan nan da ciki. Ki fada mana inda take".. Uwargida tayi dariya "amma Zuby baki da hankali. Yarinya ta fito yawon bariki shine kika je har gidansu. To nima nan bansan inda take ba. Munyi da ita zata zubar da cikin ta fara sana'a sai kuma ta bar gidan. Ai da 'Yar Dabas na gidan nan ba karamin kudi zata kawo ba". Tassss taji saukar wani wawan mari da ya gigita ta har bakinta ya fashe. Idonsa a rufe da bacin rai Qasim yace 'Yar Dabas din uwarki. Kin tara 'ya'yan mutane kina bata musu rayuwa. Wallahi idan baki fito da Asmau ba kulleki zanyi sai naga wanda ya tsaya miki." Umma, Mama har ma da Hajjo sai kuka Kawu Garzali na basu hakuri. Abdulhalim ya rike hannun Qasim da yake shirin sake sauke shi a jikin Uwargida. Ransa ya gama baci. Ina zai ga Asmau shine tambayar da yake yiwa kansa. Zuciyarsa ta gama bashi lallai akwai hannunsa a lalacewar rayuwarta da ta amininsa. Ya zama dole a gareshi ya nemota ya aureta. Umma na kuka tana rokon Uwargida ta taimaka ta fada musu inda Asmau taje. Uwargida ta rike kumatunta da yau zafi ga yaran gidanta suna kallo "tunda kika bari danki ya mareni bana fatan ku ganta. Indai karuwanci kuke tsoro ina nan ko da boka ko dan bori sai 'yarku ta zama magajiya...." Wannan karon shaketa Qasim yayi har sai da Zubaida tayi kansu duk yadda ta tsani mamanta kuwa. Su Mama suka ce ya saketa yaki. Kawu Garzali da Abdulhalim sunyi iya kokarinsu yaki sakinta. Da taji shaka ne ta nuna dakin da kayan Asmau suke. Da gudu Umma ta shiga dakin. Zuciyarta ta kara tsinkewa da taga jakar Asmau. Ga kayanta a ciki sai wari sukeyi saboda datti da dadewa. Haka Umma ta rungumi kayan tana kuka. Jafar ne ya shigo da sauri yace a cikin mutanen da ya tsaya nunawa hoton Asmau yana cigiya wani yace ya santa tana sayar da magani a kemis. Basu tsaya wata wata ba suka yi hanyar fita harda Zubaida. Uwargida tace "Zuby idan kika sake kika fita daga gidan nan kada ki sake dawowa. Ki nemi wata uwar ba dai ni ba. Ke a haka kina tunanin akwai namijin da zai aureki idan aka ji wacece ta haifeki." Turus Zubaida ta tsaya tana hawaye. Tana tsoron fita tunda bata san matsayinta a wurinsu Umma ba. Dukkansu tsayawa suka yi Hajjo ta koma ta kamo hannun Zubaida tana murmushi hakoranta da suka rine da goro suka fito. "Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah." Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta." Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti. Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce dai shikenan." Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});