Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da goro suka fito. "Mu zamu zame miki dangi kinji. Yadda muke fata da adduar kada Asmau ta fada wannan mummumar harkar bazamu barki a gidan nan ba indai zaki bimu. Miji kuma kinyi kin gama da yardar Allah." Ta kalli su Umma "duk da dai sa'ar 'yarku ce amma ga kanwa nayi muku. Idan har ta amince Garzali zai aureta." Bacin ransu a wannan lokacin ya juye zuwa farinciki. Zubaida ta sunkuyar da kanta kasa don kunya. Garzali da bai san da zancen ba kansa yaji dadi. Lokaci yayi da ya kamata ya kintsa rayuwarsa yayi maya saiti. Umma da Mama sai hamdala suke. Umma tace "Zubaida tayi iyaye da miji in ce dai shikenan." Daga haka suka fita suka bar Uwargida a tsaye ta rasa bakin magana. Sau daya Zubaida ta waigo ta kalleta daga nan tabi sababbin danginta da ta samu sanadiyar kyautatawa Asmau. ***** Da fitarsu basu zame ko ina ba sai kemis din Sada tare da wanda yace ya santa. Kemis din a rufe yake sai dai sun sami wanda yasan gidansa. Suka dunguma sai gidan Sada. Umma da Mama ne kan gaba suka shiga da sallama. Rashida suka gani a tsakar gida tana kuka ga Sada yana bata hakuri sai Yaya Tagwai a gefe tana masifa. "Nayi muku gwaninta na kori wannan annobar shine bazaki dena kuka ba ko Rashida. Allah Kadai Yasan daga ina wannan Asama'un take. Ta zauna ta fada muku karya da gaskiya kun hau kun zauna." Sada yace "Yaya Tagwai ko tunanin halin da yarinyar nan zata fada bakya yi. Ga ciki ga rashin kudi...." Umma tayi caraf tace " ba dai kuma kun koreta ba. Wayyo Allah na" Kawai sai ta fashe da wani kukan mai ban tausayi wanda ya janyo shigowar sauran mazan. Yaya Tagwai ta kallesu a dakile "ku kuma daga ina?" Mama tayi mata bayani, Yaya Tagwai ta dubi irin suturarsu tabbas babu tsiya a tare dasu. Ga Umma tana ta kuka ko ba'a fada ba tasan ita ce mahaifiyar Asmau. Rashida ta tashi tana kuka tana fada musu abinda ya faru da Asmau. Hajjo ta goge hawaye da gefen zani tace "amma wannan tsohuwa baki kyauta mana ba." Yaya Tagwai tace "haba haba ko makaho yasan kin fini tsufa" Hajjo taja tsaki "wallahi kinfini tsufa. Ji bakinki fa hakora bazasu fi goma ba" Sada ya kallesu, ana fama da tashin hankali amma da tsufansu suke fadan shekaru. Qasim ya harari Yaya Tagwai ta kama bakinta tayi shiru don ya bata tsoro "jiyan da kuka duba babu wanda yace ya ganta?" Sada yace fada masa ance bus ta shiga. Yayi musu bayanin irib bus din suna zuwa kauyukan gaban Azare har zuwa Jos ne. ABINDA AKE GUDU🙆🏽27 Batul Mamman💖 Qasim yayi alkawarin zuwa neman Asmau daga kauyen farko har Jos din. A sanyaye suka koma gidan Sada wadanda suke ganin sun zame musu 'yan uwa sakamakon kyautatawar da suka yiwa Asmau. Duka kayanta Rashida ta hada musu harda na jariran. Umma dai tasha kuka har ta gode Allah. Su Anti Binta, Shema'u da 'ya'yan Mama su Suwaiba duk sunyi ta kira su ji yaya ake ciki. Da zasu tafi har bakin mota Rashida da Sada suka yi musu rakiya aka karbi numbar wayar juna. Qasim ya cika alkawari wurin binciken Asmau sai dai babu wani abin arziki da ya samu duk da haka bai hakura ba. Duk inda yaji alamar anga mace da ta bata sai ya duba ko za'a dace. ***** Humaira babbar 'yar Zulaiha ke zaune gaban Asmau tana jira ta gama sakawa Amatullah kaya a goya mata ita. Zulaiha tace "Asmau kada ki goya mata ita kin santa da rawar kai. Tsorona daya kada garin rashin nutsuwa su fadi shiyasa idan tace na goya mata nake hanawa". "Umma da gaske zan nutsu bazan yar da ita ba. Ni da har girki nake yi miki amma sai ki hana ni goyo". Asmau ta dauko zani cikin wanda Zulaiha ta bata "tashi kinji babbar Yaya na goya miki ita. Ai nasan ko bakin kofar gidan bazaki je ba a nan zaku zauna" Duk yadda Zulaiha taso hanawa haka akayi goyon Humaira ta fita tsakar gida tana murmushin jindadi. Asmau ta sauke ajiyar zuciya. Watansu uku a gidan nan lokaci yayi da ya kamata ta fara neman aikin yi ko don ta ragewa Zulaiha nauyi. Ga Zinaru kullum tayi zancen kudin haya sai Zulaiha tace mijin Asmau ne ba'a samunsa ko da a waya. Gori kala kala take sha akan abincin da suke bata wanda ba danta ke nema ba. Gyara zama tayi yadda zata rinka hango Humaira da kyau sannan tace da Zulaiha "Nasan kina kokari sosai tun zuwana Allah Kadai zai baki lada. Amma ya kamata na nemi aiki. Saboda Amatullah dai nasan babu gidan da zasu daukeni kuma gashi bani da wata takardar makaranta. Shine nayi tunanin ko zan sami irin naki sai nayi". Zulaiha ta katse ta "haba Asmau, yarinyar nan har nawa take da zaki fara neman aiki? Ki bari ta kara kwari. Ni zamanmu dake duk wahalar da zan sha ban dauketa komai ba. Na dade ina rayuwar kunci da rashin makusanci kafin zuwanki." "Duk da haka gara nayi aikin ko don na taimaka miki. Ki duba fa tunda nazo su Muhsin basu taba zuwa makaranta ba saboda rashin kudi." Zulaiha tasan gaskiya Asmau ke fada sai dai kuma tana tunanin kankantar Amatullah. Shawara suka yanke washegari da taje aiki ta sami makociyarsu wadda tayi mata hanya. Da taimakon matar nan Allah Yasa Asmau ta sami aikin itama. Yanayin aikin nasu da wuya suje tare. Juya musu akeyi idan wasu suka yi na safe wasu sai suyi da yamma. Hakan yayi musu dadi kodayaushe akwai mai zama da yaran a gida. Asmau sai ta goya Amatullah ta tafi aikinta tunda bata isa a fara barinta a gida ba. Da yake yarinyar akwai dariya ga dan jiki sai tayi saurin shiga ran sauran ma'aikatan. Idan Asmau zata wanke bandaki sai a rike mata ita taje tayi aikin. Tunda ita mace ce mai ilimi sai ya zamto tafi sauran mayar da hankali wurin tsaftace duk inda ta gyara. Albashinta na farko kaya ta siyawa Amatullah har kala biyar da Ali autan Zulaiha. Sauran kudin kuwa kayan abinci ta siyo musu. Zulaiha sai godiya take yi mata har tayi mamaki ita da ake ta dawainiya da ita. Zamansu haka yayi ta tafiya cikin lumana da taimakon juna. A hankali likitoci da dama suka san Asmau saboda tsaftarta zance har wajen Chief Medical Director (shugaban asibiti). Da yaji yadda ake yabonta da son cigabanta tunda har turanci ta iya sosai ya canja mata aiki daga shara zuwa bada kati. Ba karamar murna sukayi ba saboda albashi ya karu. Ko kadan babu hassada tsakaninta da Zulaiha. Karshe ma aka mayar da ita bangaren bada sakamako idan anyiwa mutum gwaji a asibitin. Dan ihsani kuwa daga nurses da likitoci tana samu sosai a dalilin Amatullah. Bata da wata matsala a lokacin sai Gidado da Zinaru. Daga ita har Zulaiha basa jindadin zama dasu. Kudin hayar daki kuwa taki bawa Zinaru a hannunta kamar yadda take ta naci. Su Humaira aka mayar makaranta. Shi kuma Gidado baya shakka ko a gaban Zulaiha baya iya boye son da

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});