Chapter 80
Chapter 80
Col. Ishaq ba irin wanda zaiyiwa tsiya bane da ya sha tsokana. Yana komawa dakin Anti Bintu tace "Allah sarki bawan Allah, ya tafi kuwa?" "Ya ce komai dare zai jira a gama" Umma ta dan sha kunu "kaje kace ina wurin ka kasa fadin sakon, haba yayi hakuri mana. Nan da kwana hudu za'a fara bikin sai ya ganta. Kema da laifinki da baki fada masa lokutan da kuke farawa ba" Asmau ta rufe ido kawai. Ba karamin kewarsa take yi ba ita kanta. Gashi tasan abubuwa sunyi masa yawa tunda bikin ya matso amma kullum kokarinsa ya ganta ko yaji dadi. Sai ake rashin sa'a idan yazo an fara shafe shafe ko turara mata jiki. Da daga ita sai Massouda ne kawai yadda suke wasa da matar ficewa zatayi ba'a sani ba. Amma kullum ba'a rasa babba da take jin kunya. Har Yassar ya juya Hajjo ta dakatar dashi. Tace a goge jikin ta fita "gyaran nan ai saboda shi ake yi ko. Kwana nawa kullum yazo amsa daya ai babu dadi, sai kun sa ta fita a ransa. Ko dai ku barta ta fita ko kuma naje na kawo shi har dakin nan muga karshen gyara" Umma kunya ta kamata ta fice daga dakin su Anti Bintu suna dariya. Auduga ake tsomawa cikin ruwan wani humra mai bala'in kamshi ana goge mata jiki. Sai da aka gama tas ta zura dogon hijab akan rigar jikinta ta fita don ko kwalliya an hanata sai ranar kamu. ***** Tayi zaton yana waje sai ta ganshi a falo yana waya ga Yassar da Amatullah suma suna zaune. Cikin nutsuwa ta shigo falon Yassar ya dauki Amatullah a wuyansa suka fice. Col. Ishaq ko sallama baiyi ba a wayar ya kashe yana kallonta. Ya ciri tuta a iya kallo mai kashe mata jiki. Ashe ita ma tayi missing dinsa sosai. Sai yanzu da ta ganshi taji sauki a ranta. Ko hoda babu a fuskarta kuma iya abinda yake iya gani kenan amma tayi masa kyau. Ga wani kamshi mai sanyi da bai san da yadda zai fasalta shi ba yana fitowa daga jikinta. Kujeru biyu ne tsakanin wadda ta zauna da tashi ta gaishe shi amma da kai ya iya amsawa babu magana. Shirun nasa ya dameta tace "Jikamshina yaya, ko kayi fushi ne?" Yayi sassanyar ajiyar zuciya "Matar Jikamshi harda muryarki ma gyarata ake yi? Tunanin nawa zan karawa matar da take gyara min ke nake. I just love the way you look. Matsalata daya ce hanani ganinki da ake yi" Tayi murmushi "to kayi hakuri kaji _Jikamshina_ . "Na fada miki idan zan tafi ki dena kirana da sunan nan amma kinki ji ko?" Wani kalar tausayi yake mata tayi dariya sannan ta fara magana da shagwaba "haba Jikamshina yanzu fa na fito. Ko rabin ganinka banyi ba kake zancen tafiya" "Kina wasa dani yarinyar nan. Nace ki dena kin cigaba. Kada kice banyi warning dinki ba dai. Bari na tafi, da na sani ban matsa sai na ganki ba yau" Gabanta taji ya fadi ko dai yayi fushi da gaske ne. Tana ganin ya tashi itama ta mike tsaye jiki a sanyaye tace "Me yasa kace haka" Kallon da yake mata na ido cikin ido ne yasa tayi saurin kawar da kanta. Rage muryarsa yayi yadda itama bata jinsa sosai batare da ya bar kallonta ba yace "zan fada miki nan gaba. I love you. Sai da safe" Kasa amsa masa tayi tana kallonsa ya fita. Ta koma ciki duk tana jin babu dadi. To me tayi masa haka da ko minti shabiyar batayi ba da fitowa ya tafi. Ko dai yayi fushi ne da gaske? Bazata iya jurewa hakan ba kwanaki kadan kafin aurensu. Dakinsu ta koma ta dauko wayarta zata tura masa text don bata son kira yana tuki. Hakuri zata bashi idan ma tayi laifi ne. Tana dauko wayar ta ga sakonni a whatsap dinta. Idan ba 'yan gidansu dasu Rashidan Azare ba babu wanda take chatting dashi sai Jikamshinta. Budewa tayi zata tura masa text sai taga nashi ne a sama alamun yanzu ya turo sakon. _Allah Ya kaimu ranar aurenmu Matar Jikamshi. Ranar zaki san irin matsayin da Allah Ya baki a zuciyar Ishaq. Kada ki fassara tafiyata da komai, idan na dade tare dake *kamshin matar jikamshi zaiyiwa jikamshinta illah* Ji nayi kamar na tafi dake._ Asmau ta karanta sakon yafi a kirga tana murmushi ita kadai. Ko a yanzu ace zaiyi mata kishiya ta tabbatar zuciyarta zata iya bugawa. Duk wannan kalaman nasa da iya nuna kulawa ace ya nunawa wata matar bata san inda kishi zaiyi da ita ba. Adduar son kai tayi a zuciyarta. Allah Yasa Jikamshi nata ne ita kadai.... ***** Washegari da azahar sai ga Zulaiha a Kano ita da su Humaira, Muhsin da sauran 'ya'yanta. A bakin kofa suka rungume juna suna tsalle kamar wasu yara ita da Asmau. Yara na murnar ganin Amatullah. Gida mai dadi ba Zulaiha ba hatta yaranta sun dan murmure. Kayan jikinsu kuwa ya isa ya fada maka cewa babanta wani ne. Don ko gidan Mama da Asmau take yiwa kallon arziki sosai bai kai na mahaifin Zulaiha ba. Kaddara da rabon 'ya'ya ya kaita auren Gidado. Dreba mahaifinta yasa ya kawosu tare da kanwarta itama sunanta Asmau suna kiranta Ma'u. A tsarin bikin ranar Juma'a za'ayi Kamu da walima wanda gidan amarya ne suka dauki nauyi. Washegari asabar a daura aure sannan bayan magriba ayi Sword Crossing sai kuma ranar lahadi ayi yini a kai amarya. Yadda su Shemau suka ci burin kawata kamun ayi biki mai kayatarwa wasu mata suka dauko masu shirya biki da duk wani abu na bikin kamar abinci da harkar decoration. Ya da kanwa ne Aisha da Zainab Maiturare. Tunda suka ji sunan ango har ragin kudi suka yi musu sun ce ai su kannensa ne wannan biki na yayansu ne saboda haka zasu zage damtse wurin yin abinda za'a yaba. Rashida tazo itama da yaranta da kanwarta Harira. Yaya Tagwai ma ba'a barta a baya ba. Da ta shigo gidan harda kukata tana bawa Asmau hakuri da bata tausaya mata ba ta koreta. Sai a lokacin suka daidaita da Hajjo. Mutanen Wushishi da amarya Dijah wadda ta kafawa mijinta naci duk sun zo. Gida kam yayi albarka don ya cika da 'yan uwa da abokan arziki. Asmau gidan Jafar ta koma ita da Zulaiha. Rashida tana tare da Zubaida a nata gidan inda take kula da Uwargida. Sai bayan biki zasu je Jikamshi. Sabira ce ta kai Asmau wani salon aka gyara mata kai gashin nan yana ta kyalli sannan aka gyara kafa da hannu. Ta kalli Sabira tace "yanzu banda iyayi har hannu ma ana gyara shi. Na zata sai masu saka farce ake yiwa" "Ummin Amatullah yanzu gyara ai ko'ina ake yiwa. Matan da ake cewa suna kwacen miji a waje ba wata tsiya suka fimu ba sai gyaran da rashin kunya. Mu kuma Hausawa komai sai mu ce Allah Ya sauwake nayi kaza bayan kuma gidan mijinki kike" "Kuma fa gaskiya ne, shiyasa naga Yaya Jafar indai abu ya shafeki wallahi baya kyashi ko kadan. Ashe gyara ne da sauran sirrikan da zanzo ki bani. Muma Allah Yasa mu dace" Suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103