Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 32

Chapter 32

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka yi masa kadan. Allah Sarki wannan jaririya ko kayan sakawa bata dashi. Ta gama ta nado mata ita a zani ta bata sannan aka kawo mata dafadukan taliya 'yar hausa harda yaji da ruwa. Asmau ta zauna ta narki abincin nan tana yi tana godiya. Sai da ta koshi sannan Zulaiha ta tambayeta sunanta da kuma abinda ya fito da ita. A nan Asmau ta soma kuka. Tana yi tana bawa Zulaiha labarinta mai cike da ban tausayi da gargadi ga sauran mutane. Sosai Zulaiha ta tausaya mata. Tace " Tun da na ganki haka nan Allah Yasa naji ina son na taimaka miki. Kinga nima ba wani abu gareni ba. Ganinki da nayi sai ya tuna min da tawa rayuwar shiyasa na zabi na taimakeki ko Allah zai kawo min sassauci a cikin kuncin da nake ciki. Kinga dare yayi ki kwanta zuwa gobe zaki san nawa labarin. Allah Yasa ki sami ruwan nono da wuri kafin hakurin 'yar tamu ya soma karewa ta fara kuka". Murmushi Asmau tayi tana kallon fuskar 'yarta ta hasken kyandir. Sun tashi Zulaiha zata nuna mata dakin da zata kwanta don gidan akwai dakuna suka ji an shigo falon. Wata dattijuwa ce rike da wani mutum yana ta tangal tangal kamar zai fadi. Daga bakin kofa ta tsaya tana jifan Zulaiha da harara "yau kuma wani sabon iskancin ne ya tashi kina jina ina fama da Gidado bazaki zo ki taimaka mu kaishi daki ba?" Idonta ne ya sauka akan Asmau ta daure fuska "Wannan kuma fa, daga ina?" Zulaiha tana saka hannuwan mutumin a kafadarta tace " 'yar haya na samo dazu a asibiti. Zata karbi hayar daki daya a gidan nan, kinga kudin ko cefane sai mu kara dashi". "Cefanen banza, ni zan rinka karba ina karawa a jari na." Asmau ta dan duka ta gaishe da matar ko kallonta bata yi ba ta fara tambayar ina abincinta. Shi kuwa mutumin da Zulaiha ke ja surutai yake marasa kan gado. Da suka zo wucewa ta gabanta wani irin wari yake fitarwa. A falon ta jira Zulaiha ta kaishi daki sannan ta nuna mata wurin da zata kwana. Tana kwance rungume da 'yarta tana jin wannan dattijuwa tana masifar anyi kaza anyi kaza ba daidai ba. Can kuma taji mutumin wanda ta tabbatar mijin Zulaiha ne ya soma zage zage bata bashi abincinsa ba zata kashe shi da yunwa. Har Asmau tayi bacci babu abinda take ji yana fitowa daga bakin Zulaiha sai "kuyi hakuri". ***** A can Kano kuwa lokacin da Yassar ya shigo ciki rike da hannun Hajjo sai da gaban Umma ya fadi. Aina'u tayi saurin labewa a bayan Umma a tunaninta daukarsu tazo yi. Hankalin Umma ya bar Zubaida ya koma wurin Hajjo. Cikin sanyin jiki ta gaisheta sai dai sabanin da sai taji Hajjon ta amsa cikin kuka. Har inda Umma ke tsaye taje ta kama hannuwanta tana hawaye "Bara'atu nasan ke mai hakuri ce da kawaici. Ki dubi girman Allah ki yafewa wannan tsohuwar banzar hakkinku da ta dauka." Umma ta saki baki cike da mamaki. Me kunnenta yake jiye mata ne? Hajjo ta cigaba da magana tana kuka "nayi nadamar abinda nayi miki tsahon shekarun nan. Ni kaina bansan dalilin yin hakan ba. Bakiyi min komai ba na dora miki tsana da tsangwama." "Alhamdulillah" Umma ta fada a fili itama da nata hawayen. Hajjo ta cigaba da rokon gafara Umma tace ai zuwanta kadai yasa komai ya wuce. Hajjo ta mika hannu "zo nan autar Bara'atu. Taho wurin kakarki kinji 'yar albarka. Jafaru baka ce komai ba. Ku yafeni ko don darajar babanku" A darare Aina'u ta matsa jikin Hajjo. Garzali ma a kunyace ya gaishe da Umma ta amsa bakinta yaki rufuwa don murna. Jafar ma murna yake yi sai dai hankalinsa yafi karkata ga Zubaida dake tsaye tana kare musu kallo. Sai da aka dan sami nutsuwa a falon sannan Jafar yace "Umma bakuwar nan fa tana jiranki" Hakuri Umma ta bata ko wurin zama basu bata ba suna farincikin fara daidaituwar al'amuran danginsu. Aina'u ta kawowa Zubaida lemo da abinci tana ci suna kallonta. Jira suke yi ta gama ta fada musu abinda ta sani game da Asmau. Da ta gama ne Umma ta fada mata Asmau tayi wata bakwai rabonta da gida. Zubaida ta dan cije lebe fuskarta ta nuna rashin jindadi "nayi tunanin gida da dawo da na koma aka ce min bata nan. To ina ta tafi?" Hajjo tace "kinga yarinya, bayani zakiyi mana yadda zamu fahimceki sosai. A ina kika ga Asmau'un?" Zubaida ta fada musu komai game da zamansu da Asma'u. Umma da Hajjo sai kuka jin Asmau ta zauna a gidan karuwai. Tace hatta yadda ta sami cikin duk ta fada min. Umma ta share hawaye "Ta fada miki sunan wanda yayi mata cikin?" "Eh tace sunansa Abubakar". Umma ta toshe bakinta da hannu tana wani kukan. Dama Qasim ya tabbatar musu cikin Abubakar ne amma basu bawa wacce abin ya shafa damar bayani ba. Yassar ta nuna "tashi maza kaje ka kira Mama Yalwa. Ka fada mata bakuwa ce tazo daga Azare wadda tasan Asmau". Ba'a dade ba sai ga Mama suka zauna Zubaida ta fada musu duk labarin da Asmau ta bata na waya da yadda al'amarin ya cigaba. Falon sai salati suke yi ana jimamin wannan abu. Ace tarbiyar shekara da shekaru wasu can da basa kishin addini suyi ta fito da samfurin yada alfasha salo salo suna turawa 'ya'yan musulmi. Hajjo tace "to shi shegen giruf (group) din aje a tarwatsa mana kowa ya huta. Haka kawai an janyowa marainiya fadawa mummunar rayuwa. Kada na kaiku da nisa ko mu da babu waya a zamaninmu waye ya koya mana yadda ake yi tsakanin mata da miji. Gashi mun rayu dasu cikin kwanciyar hankali mutuwa ce ta raba. Duk wannan shaidancin kuma da ake yadawa ai bai hana mutuwar auren yara kanana ba." Mama da batasan yadda akayi Hajjo ke nuna damuwarta akan Asmau ba tace " ai group din a waya ake bude shi. Ni abinda ya fi damuna bai wuce yadda zakiga yara da matan aure a dauki waya tun safe har dare ki rasa me ake gani. To ashe duk harkar lalacewa ce duk da dai ana samun karuwa ta wani fannin. Yaranmu da sunyi waya sai kiga basu da lokacin komai sai nata." Zama sukayi ana ta mayar da zance kowa na tofa nasa. Kawu Garzali a fusace yace "ita wacece wannan Walidar ne? Tayi fatan kada mu hadu don wallahi sai nayi mata rauni. Kawaye da abokan banza sunfi saurin lalata tarbiya. Ni ba daga abokin bane muka kare a haka." Ya dubi Jafar da Yassar " yanzu kuna da uba saboda haka duk yaron da na gani baiyi min ba kafin na kore shi ta kanku zan fara". Umma tayi murmushin jindadi. Duk da tasan Garzalin kansa baya sahun mutanen kirki amma dai taji dadin kulawarsa ga 'ya'yan dan uwansa. "Walida kawar Asmau ce tun primary. Kuma itama nata mahaifin yana kokari. Don ranar da abin ya faru kafin mu dawo daga asibiti yazo ya dauketa." Hajjo taja tsaki wanda har Zubaida da Aina'u sai da suka yi dariya "anyi ta baya ta rago. Shi da

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});