Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 103

Chapter 103

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 777 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bata taba ganin wani abu daga gare shi da zai sa taji ya ware Amatullah saboda ba tasa bace ko kuma yanayin haihuwarta. Shiyasa a kullum bata gajiya wurin saka shi a adduarta. Abdallah na da wata uku Yassar ya dawo daga short service dinsa ya dage shi fa aure yake so. Ga ginin da Umma take yi masa da saura amma haka ya hada har da nasa 'yan kudin kafin aiki ya kankama. Bilkisu ta kunno shi sosai akan maganar aure kuma ya zama irinta. Dama zama dasu Jikamshi sai an koyi hali. Iyaye dai sunyi murna kuma an saka rana. Bikin Walida ma ya tashi su Asmau sunyi rawar gani. Sai da aka gama ta fara shirin makaranta an gama komai. Jikamshi ya cika alkawari bai hanata ba. Yarinya ta samu suke tafiya tare tana rike mata Abdallah idan zata shiga aji. Yana da wata tara amma da girmansa ga kamaninsa da babansa kamar yayi kaki. A haka ne wata rana ta tashi da safe da amai ko makaranta ta kasa zuwa. Gwajin farko ta gane ciki ne. Murna a wurin Col. Ishaq kamar cikin farko. Yayi ta tattalin matarsa. Dole ta yaye Abdallah ga karatu. A haka tayi ta fama har ta haifi 'yarta mace wannan karon a asibiti. Yarinya taci sunan Hajiya wato Lubabatu amma suna kiranta Amaturrahman. *Bayan shekara uku* Asmau ce tsaye a kofar dakin yaranta suna bacci. Amatullah da Amaturrahman akan gado suna rungume da juna. Shakuwarsu har ta baci. Saboda Amatullah bata iya fadin sunan kanwarta sosai itama idan an tambayeta sunanta sai tace Amatuyyahman. Duk yadda mutum yaso gyarawa sai tace ba haka Yaya take fada ba. Abdallah yana kwance a kan nasa gadon ga kayan wasa sun baza. Hannuwan Jikamshinta taji ya rungumeta ta baya tare da dora kansa a kafadarta. A daidai kunnenta yake magana "Tunanin me kike yi Matar Jikamshi?" Kwantowa ta sake yi a jikinsa tace "ina godiya ga Allah akan ni'imarSa gareni." Hannunta yaja suka tafi dakinsa ya tura kofar da kafa. Yana juyowa yaga tana hawaye. "Allah nagode Maka baki da aiki sai kuka. Ni kaina daga haduwarmu zuwa yanzu sau nawa kina sani kukan nan. Yau kuma me ya faru?" "Ina tsoron ranar da yaran nan zasu tsaneni. Gara gara ma su Abdallah amma Amatullah sai taji ina ma bani bace mahaifiyarta. Me zan fada musu a lokacin da suka kara wayo mutane suka sanar da su mamansu ta taba ciki a waje? Ya zanyi da Amatullah idan ta tuhumeni da gurbata mata asali? Idan suka kyamaceni yaya zanyi da rayuwata?" Kuka take yi da gaske. Kwantar da ita Jikamshi yayi ya kwanta kusa da ita kanta yana kan kirjinsa. "Daga ranar da kika ji rasuwar Abubakar da batun cikinki kin taba tunanin zaki kara samun nutsuwa a rayuwarki?" "A'a" "To a yanzu Allah Ya kyautata miki rayuwa ko kuwa?" "Ya kyautata min" "Ina so ki sani cewa tunanin gaban da baki gani ba babu alkhairi a ciki. *Abinda ake gudu* ya riga ya faru. Adduarmu shine Allah Ya kara karemu daga sharrin shaidan da mukarrabansa. Yara kuma da kike tunani bazasu taba guje miki ba da izinin Allah. Ke dai kiyi iya yinki wurin basu tarbiya da nuna musu so irin na uwa, sauran kuma mu barwa Allah. A karshe Matar Jikamshi, Asma'un Ishaq ina mai kara shaida miki idan duniya zata gujeki in sha Allah bazan taba rabuwa dake ba. Kece Ishaq, Ishaq kuma Asmau. I love you with all my being" Kara rungumeshi tayi sosai tana hawayen farinciki "I love you too Jikamshina. Allah Ya barmu tare" Suka ce Amin a tare. ***************** *ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH* Ina godiya ga Allah da Ya bani ikon gama wannan labari. Ina fata Allah Yasa mu amfana da abinda yake cikinsa wanda yake daidai. Kuskuren dake ciki Allah Ya yafe min Ya kawar da hankulanmu daga aiki dashi. Allah Ya karemu daga abinda ake gudu. Godiya mai tarin yawa gareku masoya wannan labari. Hakika kun cancanci yabo domin kun bani kwarin gwiwa sosai. Bazan kama suna ba domin kuwa kuna da yawa kada nayi abinda ake gudu na manta da wasu. Allah Ya saka muku da alkhairi. *Gaisuwa gareku* matan 1.Batul Mamman novel grp 2. Yan uwa na Fikrah writers association. 3. Taskira 4. Rufaida Omar fans 5. Maryam Ameen novels 6. Tafeesu novels 7. RAZ novella 8. Zauren Biebee Isah 9. Feenat Jaafar novels 10. Mss MJay novels 11. Hausa novels only 12. Hausa novels xallah 13. Zauren karatu 14. Fairytopia novels 15. Rash kardam novels 16. Queen Meemi fans 18. Fati Ali novels 19. N,N $ Z novels Da wadanda ban saka ba duk ina godiya da mika sakon gaisuwa.

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});