Chapter 39
Chapter 39
bayan magriba da zazzabi mai zafi jikinta sai rawa yake yi. Lokacin Asmau tana kan abin sallah tana karatu taji fadowar Amatullah daga kan katifarsu. Sauri tayi taje ta dagata taji jikinta yayi mugun zafi. Hankalinta ya tashi ta rasa me zata yi mata. Da kuka ta fito da ita a kafada ta tafi dakin Zulaiha wadda bata dade da dawowa gidan ba. Har tana jin muryar Ali yana fada mata Zinaru ta zane Amatullah. Ko sallama bata yi ba ta shiga "Zulaiha taimakeni don Allah Amatullah zata mutu." Zulaiha ta bar kokarin cire kayan aikinta ta karbi Amatullah tana salati. Kwantar da ita tayi akan katifa tana ta karkarwa. Asmau ji take inama ciwon ya dawo gareta. Ta matsa jikin bango ta jingina tana jira kawai ace mata ta cika. Amina ce ta shigo Zulaiha tace ta samo mata ruwa mai kyau a roba da sauri. Asmau na kallo ta tubewa Amatulla kayanta duk da sanyin da take ji da aka kawo ruwan ta cire dankwalin kanta ta rinka guga mata ruwa a jikinta. Kukan Asmau kai kace Amatullah ta rasu. Zulaiha tana bata hakuri. Da taji zafin ya dan ragu tace bari ta cire kayanta su tafi asibiti. Asmau ta dauki Amatullah ta goyata suka fita. Yaran gidan duk jikinsu yayi sanyi. Kafin su karasa asibitin da suke aiki numfashin Amatullah har wani sama yake yi. A asibitin emergency suka wuce likita da nurses suka karbeta. Ana ta gwaje gwaje Asmau tana kuka kamar ranta zai fita. Likitan ya fito ya bata takardar magani sannan yace zazzabi ne mai zafi da kuma alamun pneumonia(ciwon nemoniya ko sanyi da yake kama kirjin yara). Hankali a tashe Zulaiha ta karbi takardar da kudin magani a hannun Asmau ta tafi ita kuma ta shiga dakin da aka mayar da Amatullah. Idonta a bude sai dai ta fada kamar ta dade babu lafiya. Tana ganin Asmau abinda ya fara fitowa daga bakinta shine "Ummi ni waye Babana ne? Zinayu tace Baba Gidado ba babana bane." Wani kukan ne yazo wa Asmau. Yana daga cikin _abinda ake gudu_ ki haifi yaro kafin aure ya tambayeka mahaifinsa ki rasa amsar bayarwa. Tun farkon haihuwarta take fargabar irin wannan lokacin. Ta tabbatar idan Amatullah ta kara girma abin sai yafi haka. Cike da nadama take tunanin da tana gidansu Yaya Jafar, Yassar , Yaya Abdulhalim da Umar duk bazasu bar 'yarta tayi maraici ba. Allah Sarki Abubakar ta fada a ranta. Yau ga sakamakon rashin hakuri ta kusantar zina wanda ya janyo musu fadawa ga yinta. Shekara biyar da faruwar abin amma babu ranar da zata wayi gari bata tuna da wannan yinin ba. Hawaye ta share ta kirkiro murmushin dole "Ama babanki yana aljannah kinji ko. In sha Allah yana can yana jiranmu. Kullum kika yi sallah kice Ya Allah Ka yafewa babana Kasa shi a aljannah." Ta zauna a kan gadon Amatullah tayi pillow da cinyarta."Ummi yaushe zamu je aljannah wurin babana? Ni yau nake son zuwa na fada masa Zinayu ta dokeni. Sai ya yama min ko." Asmau tace "zamu je watarana kinji. Amma ba yau ba don Allah. Sai kin girma kin zama babbar malamar addini kin tara yara da yawa". Amatullah tayi dariyar jindadi "idan munje shine zai kaini school. Ya siya min jaka mai kyau irin da takalmi. Har kayan sallah fa." Kula tayi da hawayen da Asmau take yi tace "Ummi ki dena kuka zai siya miki kema. Sai mu tafi namu gidan ko?" "Uhm" kadai ta iya cewa hankalinta yana wani wurin. Yaya zata yi da Amatullah yarinya mai dan karen wayo. Nan gaba kadan tasan zata sake tayar da zancen. A haka Zulaiha tazo ta same su. An bawa Amatullah maganinta da allurai sannan Zulaiha ta koma gida dauko musu kayan kwana. Cikin dan lokaci labari ya karade asbitin 'yar Asmau bata da lafiya. Ma aikata da yawa suka rinka zo duba ta. Sai da sawu ya dan dauke wata likita tazo tana yiwa Asmau fadan irin dukan da take yiwa Amatullah wanda take tunanin harda shi da kukan da tayi ya sa mata zazzabi. Asmau ta tabbatar mata ba ita tayi dukan ba. Likita tace to dai ta kiyaye don babu mai kular mata da 'ya kamar ita kanta. Sannan dole a kula da hanata shiga sanyi da kura don tana ganin alamun asthma gareta ba pneumonia ba. Sake tsorata Asmau tayi. Tabbas Abubakar yana da asthma ba abin mamaki bane idan 'yarsa tayi. Amma irin halin da taga yana shiga ga kashe kudi wanda bata dasu sosai ya tayar mata da hankali. Kwanansu uku sannan aka sallamesu. Kullum Zulaiha da su Humaira indai ba aiki ba ko su suna makaranta a nan suke zama sai dare su koma gida. Asmau kuwa taci alwashin bazata sake yarda da Zinaru ta taba lafiyar gudan jininta ba. ***** Zinaru ce zaune a gaban wata kawarta da suke kasa kaya a kasuwa take fada mata irin maganganun da Asmau ta fada mata ranar da ta zane Amatullah "Wato Kande maganganun sun kona min rai. Yarinya kamar wannan ina ta kawar da kai duk da bana son zamanta damu sai da ta kaini bango. Kuma ina ji lokuta da dama tana ziga shegiyar nan Zulaiha akan ta rabu da Gidado. Ni yanzu idan auren ya mutu ai ta tona min asiri. Ina zamuje mu zauna. Gashi dan banzan yaron har yau bai san ya girma ba. Daga shaye shaye sai neman mata ya iya." Kande ta tabe baki "tun farko ke kika yi sake. Ke da kike da jari a hannu. Gidado ai *farar haihuwa* ne. Kina kalli ya rasa matar aure sai Zulaiha ga 'ya'yan masu kudi a gari. Kinsan mu da rauni akan mai kyau. Idan da hali kisa ya saketa ita kuma bakuwar ku koreta ya auro sabuwa 'yar masu kudi". "Kin kawo shawara Kande. Amma babbar matsalar shine gidan nan nata ne. Ga yara har shida don bala'i haihuwa kamar zomo. Don ma Allah Ya takaita mana ta tsaya. Babbar fa zatayi shahudu yanzu. Kinsan auren kuruciya suka yi." "Duk wannan ba matsala bane. Ke dai ki samu yaron nan ya dau saiti ya gyara kansa. Da kanki zaki bani labari. Kin sanni da shige shige sai na tayaku neman mai maiko." Tafawa suka yi sannan kowacce ta cigaba da ihun azo a sayi kayanta. ***** Kwanaki hudu a tsakani wurin karfe tara na dare Asmau ta fito zata je bandaki taji Zinaru tana ambaton sunanta. Tsayawa tayi taji abinda za'a ce tayi. Daga cikin dakin Zinaru ke cewa Gidado "dole ne ka rabu da Zulaiha hakan ne kawai zai sa Asamau ta bar gidan nan. Zulaiha ma da dabara zaka saketa yadda zamu tsira da gidan nan. Ka santa da son 'ya'ya sai ka ce mata ka saketa amma tare da yaran zamu tafi. Nasan idan taji haka zata bar maka gidan ita ta fita. Kande ta riga ta samo mana 'yar wani kusa a gwamnati da zaka yi auren jari da ita." Gidado cikin muryar wanda giya bata gama sakinsa ba yace "amma Zinaru idan muka yi haka kamar bamu kyautawa Zulaiha ba. Kuma Asmaun nan na fada miki ita ma sonta nake yi." "Sakarai mara lissafi, Asama'un me. Ana maka zancen 'yar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103