Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 77

Chapter 77

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da kunyar ne? Ana shirin tafiya kin kasa hakuri kin fito ki ganni" Asmau ta rasa me zata ce sai bude baki kawai da tayi cikin mamaki. Shine fa yayi mata waya yana magiyar ta zo ya ganta. Dariya yake mata don yasan ya kureta "rufe bakin kada ya makale a haka" Ta dan juya ido "gara ya makale kowa ya huta" "Tuba nake Matar Jikamshi, shi bakin nan naki da kike gani ba karamin mahimmanci gareshi ba. Idan ya makale an cuce ni." Ta soma dariya ganin yadda ya kara marairaice fuska "meye amfanin bakin banda cin tuwo. Idan ya zauna a haka kaga na dena shan wahalar bude shi" Yace "da gaske kina so na fada miki kadan daga cikin mahimmancin bakin Matar Jikamshi" Wani jan zancen yake yana kallonta kasa kasa. Ko baa fada ba tasan ko me zai fada karshenta sai taji kunya shiyasa ta saka hannuwanta biyu ta toshe kunnenta tana ja da baya. "Ka barshi kawai na yafe. Wani ilimin ba sai na sani ba" Yayi murmushi mai kyau "kaji min yarinya. To ba abinda kike tunani zan ce ba. Shiyasa nace kinfi karfina dama" Sosai Asmau taji kunya ta koma ciki da sauri tana jiyo dariyarsa. Yanzu da suka shiga motocinsu zasu tafi ji yake ina ma motarsu daya. Ko yaya suka juya su kama juna suna kallon junansu. ***** A titin Zaria road suka hadu da Abdulhalim da Qasim a motar Qasim din. Daga nan suka mika sai Azare. Tun fitowarsu Zubaida ana ta hira a mota amma jikinta yayi mugun sanyi. Ba don Umma tayi mata nasiha sosai ba ita ko kadan bata son tuna asalinta. Yanzu duk mutanen nan kowa sai ya ga a irin kazantar da ta tashi. Addua take Allah Yasa kada su je su tarar da irin tsofaffin yan tashan nan da basa tsoron Allah masu zuwa wajen Uwargida a dakin. Sai su zo suce wai banda tsufa ya fara zuwar mata duk tafi yaranta iya aiki. Wani sa'in ma idan taji kudi sosai komai kuruciyar mutum bata jin komai take bashi dama. Koda yake ina wata kunya ga mace irin wannan. Motarsu ce a gaba Zubaida tayiwa Jafar kwatance. Su Asmau ma jiki ya mutu suka dena hirar saboda ganin yadda yanayinta ya canja. Asmau tana zancen zuci tace kada Allah Ya kawo ranar da Amatullah zata kyamaceta irin yadda Zubaida take yi a yanzu. Gidan yana nan yadda yake ko fenti ba'a canja ba. 'Yan bakin kasuwa suna kallon abin mamaki. Motoci irin wadannan a kofar gidan Uwargida. Kuma gashi harda mata bare ace wasu kadangarun barikin ne suka zo neman 'yan matan gidan. Asmau da Zubaida aka rasa me fara shiga. Ita Zubaida ma hawaye take yi har Kawu Garzali ya gani. Da sauri yazo ya karbi baby dinta mai suna Shuaibu suna kiransa Aiman sannan ya rike hannunta suka fara shiga. Zuciyar Asmau ta tsinke, yanzu haka Jikamshi zai shiga gidannan. Allah Yasa kada shi ko Hajiya wani yace a fasa auren. Zuga guda suka shiga da sallamarsu. Matan a gaba maza a bayansu. Kaya ne tarkace kala kala a tsakar gidan. Wasu matan na wanki wasu suna girki. Kowacce da sabgar gabanta. Kadan a ciki Asmau ta gane. Duk barin abinda suke yo suka yi kallo ya dawo kan baki. Daga kofar dakin Uwargida Bulayi ya fito. Mutumin da ya fara kawota gidan nan. Dama can a dattijo ta san shi. Yanzu kuwa tsufa ya kara bayyana a tattare dashi. Yana kokarin zura takalmansa ne idonsa ya sauka akan Zubaida. Fuskarsa ba karamin mamaki ta nuna ba yace "Zuby???" Ranta a dagule yake dama ta harare shi "Zubyn uwarka" a duniya yana cikin mutanen da ta tsana. Duk yarinyar da aka kawo gidan sai yayi amfani da ita kafin kasuwarta ta bude. Maimakon ta ga bacin rai a fuskarsa sai ya washe baki cike da fara'a yace "Shegiya ita ce kuwa, kina nan da bakinki kamar reza" Cikin dakin ya koma da sauri har yana tuntube. Suna jin muryarsa yana kiran Uwargida tazo ga Zuby ta dawo. Zubaida ta ji muryar mahaifiyarta tana cewa "Bulayi kada kayi min wasan da zai tayar min da hawan jini" "Yasin da gaske nake, bari na kamaki muje wajen" Kunya ta kara kama Zubaida, yanzu haka zasu fito hannu da hannu kamar wasu mata da miji a gaban mutanen nan masu daraja a idonta. Dukkansu kallon kofar suke zasu ga wannan Uwargidan ga wadanda basu taba ganinta ba. Bulayi ne ya fara fitowa hannunsa rike da sanda yana cewa "yi hankali da matattakalar kofar" Rike da sanda ta fito wacce Bulayi ya daga mata daga waje yana mata jagora. Tana nan da tsayinta fuskar nan tayi wani irin dabbara dabbara saboda mayukan bleaching da taji a baya. Sanye take da tubarau baki wuluk irin na makafi. Tana mika hannu cikin iska alamar lalube tace "Zuby kina ina?" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Zubaida bata san lokacin da ta saki hannun Kawu Garzali ba ta tafi wurin babarta tana kuka "Mama makancewa kika yi? Wayyo Allah na, kinga ni fa jikokinki na kawo miki nayi aure. 'Ya'yana hudu. Mama ki bude ido ki gansu don Allah" Uwargida tayi dan murmushi tana rungume da 'yarta. Hawaye ya zubo mata tana ta shafa fuskar Zubaida tace "Ashe zamu gana kafin na mutu Zubaida. Allah nagode Maka. Ina yaran? Wane dan albarkan ne ya rufa min asiri ya aureki? Kinga yadda Allah Ya mayar dani ko. Karyar karuwanci ta kare bani da wani mataimaki sai Allah sai Bulayi da bai gujeni ba" Zubaida ta kalle shi sai taji kunyar zagin da tayi masa. A yadda taga mahaifiyarta ta kara tsufa da yankwanewa sai ta godewa Allah da Umma ta dage lallai sai tazo. Bulayi ne yace "Uwargida tare da baki take fa. Ina jin surukanta ne mu shiga daga ciki ko kuma ina zuwa dai" dakin ya koma ya dauko tabarmi gudu uku. Kamar hadin baki Qasim da Col. Ishaq suka ki zama. In da sabo tsayuwa ba komai bace wurin soja da dan sanda. Sai akayi dace kyamarsu tazo daya basa son zama a tabarmar da ta fito daga dakin matar. Sauran dai sun zauna sannan Zubaida ta fara yi mata bayanin kowa. Yaranta kuwa sai da Uwargida tabi tana shafasu tana binsu da kiss a fuska. Manyan biyu mace da namiji dai kyankyaminsu suke. Tana yi suna gogewa duk ta yaba musu yawu. Da Zubaida tace tare suke da Asmau Uwargida ta mika hannu zata kamata. Balayi yace "Yar dabas kin canja Yasin. Jikinki duk ya murje kinyi fresh. Dama naso naga kama to kuma sai naga ta yanzu tafi ta da kyau da daukar ido." Wani mugun kallo Col. Ishaq ya sakar masa wanda ya girgiza har hanjin cikinsa. Ba arziki yayi shiru. Asmau ta dan matsa gaba Uwargida ta kama hannunta. "Nayi sanadiyar lalacewar 'ya'yan mutane da yawa Yar dabas, iyayenki har nan sun zo nemanki. Nagodewa Allah da baki kama sa'a kamar yadda naso ba. Hakkin wadancan shegun kadai ya isheni. Ni shaida ce akanki har kika bar gidannan namiji bai taba zuwa kofar dakinki ba. Ke kam kinji dadi 'yan uwa basu kyamaceki ba har Allah Yasa rayuwarki ta koma kan layi. Me kika

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});