Chapter 96
Chapter 96
rai da zaka ga jininka ba Ishaq. Allah Ya amsa min, Allah nagode. Sai dai bawa yaga jinkiri wanda komai daren dadewa zamu kwashi ladan hakurinmu a duniya ko a lahira. Allah Yayi miki albarka Ya raba lafiya" Duk duniya babu matan da yake so sama da Hajiyarsa da matarsa. Yau Hajiya harda kiran sunansa don murna. Gasu a gabansa suna kuka. Hajiya ta dago kan Asmau tana kallo "ba abin kuka bane Asmau. Ki godewa Allah" Col. Ishaq yace "Hajiya nayi mata laifi. Ko kallonta na kasa yi shiyasa na kawota wurinki" Ai kuwa yasha harara a wurin Haj Lubabatu. "Asmau me yayi miki? A wannan yanayin har zaka bata mata rai" Muryarta har ta dashe da kuka tace "ba laifinsa bane Hajiya. Laifina ne, kuskurena ne, da ban biyewa zuciyata da shaidan ba hakan bazata faru ba" "Don Allah kuyi min bayani. Me kayi mata nace?" Asmau ce ta kuma yin magana don ya kasa dago kansa "bakin fentin da nayiwa kaina bazai taba wankuwa ba ko me zanyi a duniya. Allah ne kadai shaida akan tuban bayinSa. Ban taba yi muku karya ba wallahi sau daya tsautsayi ya fada min. Da banyi cikin shege ba...." Toshe mata baki yayi da hannu ya hanata karasa magana a gaban Hajiyarsa yana kokarin rungumeta. Hawaye ne da baisan daga ina ba suke zarya a kumatunsa. Hajiya da kanta ta sa hannu ta janye Asmau ranta yayi masifar baci. Ita rashin kunyar tasa ma yau bata gani ba. Cikin fushi tace "hala cewa kayi ba cikinka bane?" Bazaiyi mata karya ba ya gyada kai. Kowa a gaban mahaifiyarsa yaro ne. Tsawa tayi masa sosai abinda ya bawa Asmau tsoro. "Shekarunka da iliminka sun tashi a banza. Kuma ka bani kunya ashe son da kake ikirarin yi mata yana da iyaka. Idan bata yafe maka ba zargin nan kasan cewa zaka hadu da fushin.... " Asmau ta kara fashewa da kuka ganin yadda mijinta abin sonta yake hawaye kamar karamin yaro ana yi masa fada bayan bashi da laifi "A'a Hajiya kiyi hakuri wallahi ba laifinsa bane. Laifina ne da na zubar da mutuncina a waje." Ta juya tana kallonsa shima ita yake kallo "ni nace ban yafe maka bane da ka kawo kanka kara, ko fushi banyi da kai ba. Don Allah ka dena kuka Jikamshina" "Da gaske kin yafe min Matar Jikamshi?" Ya fada yana dago hannu zai share mata hawaye. Ta gyada kai tana murmushi. Haj Lubabatu taji dadi sosai, wannan so da suke yiwa juna daga Allah ne. Gani tayi za'a fara rashin kunya a gabanta kamar sun manta tana wurin Col. Ishaq ya gama matsowa kusa da Asmau sai tayi gyaran murya ta sake hade rai. "Dan bamu wuri zanyi mata magana" Sai da ta maimaita ya tashi ya fita daga shi har Asmau suna kallon juna. Bayan ya fita Hajiya tace "Asmau kafin nace komai ina rokonki alfarma don Allah kada Haj Bara'atu taji zancen nan. Ko kadan bazata ji dadi ba. Sannan ina so ki kara hakuri da kaddara. Kamar yadda kika fada duk matar da ta taba aikata kuskure har wani namijin ya kusanceta to wallahi har abada lokaci zuwa lokaci akwai sanda zargi ko yaya zai darsu a zuciyar wadanda suke tare da ita. Zaki ga kinyi abin bajinta da burgewa amma karshe tuhumarki za'ayi. Kada ki rabe dayan biyun yaron nan yana sonki. Kiyi hakuri da halin da zakiyi ta tsintar kanki a ciki saboda abinda ya faru a baya" Murmushi Asmau tayi "ko kadan banji haushinsa ba. Kukana nadama ce akan abinda nayi a baya. Na tabbatar ba don haka ba Allah kadai Yasan farincikin da zaiyi tun farko. Da wata yake aure wadda bata da tabo irin nawa zaiji dadi mara misaltuwa. Ni kuwa dole ne yaji tsoron ko ba nasa bane musamman da ya gama yarda bazai haihu ba" Hajiya tace "shi kadai ya yankewa kansa wannan hukuncin babu ruwan likitoci. Badariyya ta haihu saboda rabonta na can shima gashi Allah Ya bashi nashi. Allah Yayi muku albarka." Ta kallo kofa "Sai ka shigo tunda ka koyi labe kaima" Asmau ta kallo wurin kofa sai gashi Jikamshinta ya shigo. Ko tun yaushe yake wurin bata sani ba. Maganganunsu da Hajiya sun kara sashi jin bai kyautawa Asmau ba. Dole yayi kokari wurin mantar da ita kuncin da ya dasa mata. Hajiya tace "sai ka tafi gida ita a nan zata kwana. Asmau me zan dafa miki?" Asmau tace "Hajiya don Allah ki zauna bana jin yunwa" "Dole kici abinci duk kin rame. Kai kuma me kake jira ka tafi mana." Asmau na kallo ko motsi yaki yi. Hajiya ta fita daga dakin don take takensa rashin kunyar da ta rasa inda suka gado ta yake neman yi. Kitchen ta tafi tana tunanin me zata dafawa Asmau taci. Baiwar Allah duk ta rame. Shima kuma ya fada kamar bashi ba. Yana dena jin takun Hajiya ya daga Asmau yana juyi da ita "I love you so much Matar Jikamshi. Ki yafe min kinji" Zata yi dariya saboda yau zuciyarta a wanke take yace "kada kiyi dariya ko so kike Hajiya taji tace baki da kunya" "Kai da ka daukeni a tsakar dakinta ai ka fini rashin kunyar" Ya sauketa "bari nayi miki a hankali saboda baby na. Amma fa idan Hajiya bata bari mun tafi gidanmu ba to za'ayiwa babyn nan kani ko kanwa a gidanta" Murmushi tayi na jindadi Jikamshinta ya dawo. Shi kuma ya janyota yana bin fuskarta da kiss ko ta ina. ABINDA AKE GUDU🙆🏽59 Batul Mamman💖 Jin taku kamar na Hajiya yasa Col. Ishaq ya sauke Asmau. Gani yake kamar a da can ba sonta yake ba saboda yadda yake jinta a ransa yanzu. Ita din ma shi take kallo cike da so. Bata da abinda zata saka masa dashi face addua da kuma tsantsar kulawa irin wadda ta dace da miji. A haka suna wannan kallon kallon da murmushi a fuskokinsu Hajiya ta karaso dakin tace ya wuce gida ya daukowa Asmau kaya kamar na sati daya. Ramarta tayi yawa tana so ta zauna har ta mayar da jikinta. A take murmushin dake fuskar Col. Ishaq ya bace. Asmau ta gimtse dariya don da gaske ya bata rai. Hajiya ta saka shi a gaba suka fita tare. Bata kyale shi ba sai da taga ya shiga motarsa ya tayar. Suna fita Asmau ta kwashe da dariya. Tsakaninta da Allah itama tana kewar mijinta. Amma yanayinsa ne yasa tayi dariya don tasan akwai rigima a gaba. Yana iya cewa me yasa da Hajiya tace zata kwana bata nuna bata so ba. Har ya isa gida tunanin yadda zaiyi da Hajiyarsa yake. Ko don bata san yaushe rabonsa da su yiwa juna kallon kirki bane shi da Asmau. Yau da ta kasance ranar farinciki sosai garesu, sun shirya ga kuma babbar kyauta shine zata hanasu celebrating. Shawarar da yasan zata fishshe shi ya yanke sannan ya koma gidan. ***** Tuwon masara Haj Lubabatu tayi da miyar kuka wadda taji naman rago da wake. Tana yi zuciyarta fes ciki da farinciki. Ba karamin tausayin Ishaq take ba gashi dama ance mahakurci mawadaci. Ta san irin yadda rashin haihuwa ya dame shi sosai. A dalilin hakan babu irin bacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103