Chapter 48
Chapter 48
da ita a zuciyarsa. Har mamakin kansa yake yi. Bai yarda sonta yake yi har haka ba sai bayan 'yar hirarsu ta dazu. Yana son muryarta, kunyarta, yanayinta....ya dan shafa kansa yana murmushi ya tura mata da text "Asmau Ummin Safina ki shirya, don Jikamshi da gaske yake. Kiran wayarki kuma yanzu na fara. Gudnyt" ***** Hannunta har rawa ya soma bayan ta karanta text din. Wani abu taji ya ratsa jikinta gabadaya don dadi. Bayan Abubakar bata taba tunanin sake jin wani abu makamancin wannan akan kowane da namiji ba sai akan Col I.M Jikamshi. Sai dai kuma wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa. Yaudarar kai ne ma ta yarda wani abu yayi nisa tsakaninsu. Tafi kowa sanin ko ita wacece, bata cikin mata da zasu sami rabon aure a wannan duniyar. Dadin dadawa Jikamshi ba karamin mutum bane. Yana da wata kima ta daban a idonta, sam bazata so suyi rabuwa mara dadi ba. Gara tun ba'a soma ba kada a fara. Tana wannan tunanin ne bacci ya kwasheta. Washegari Umma ke fada mata su fara shiri nan da kwana biyu zasu tafi Zaria da Aina'u. Sati daya zasu yi daga nan zata zo ta same su su wuce Wushishi. Jin zata je Zaria wurin Anti Bintu yasa ta farinciki har ta dan manta da tunanin da ta kwana ta tashi dashi. Shirye shirye suke yi daga ita har Aina'u sun hada kayansu da komai. Yassar ne zai kaisu ya dawo washegari. Da yamma ne ta tafi gidan Jafar saboda yace yana son ganinta tace ya bari zata zo da kanta. A gida ta bar Amatullah tana bacci. Sun dan taba hira da Sabira ta tashi ta basu wuri. Ba wani dogon abu bane maganar karatu yayi mata wanda yace sunyi shawara ne da Shemau zasu hada kudi su biya mata ta koma makaranta. Kuka take yi sosai kamar yasan abinda take son yi kenan. "Yaya Jafar Allah Ya saka da alkhairi. Nagode sosai, nima abinda yake raina kenan don bana son nayi ta zaman haka." "Kada ki damu Asmau. Ina so ki manta da rayuwar baya kiyi kokarin gina rayuwa mai kyau daga yanzu. Kada ki manta ko ke wacece a duk inda kike. A yanzu da kika dawo gida inda mutane suka sanki suka san labarin rayuwarki ki zauna da shiri na fuskantar kalubale kala kala. Dole duk inda kika shiga kiji maganganu marasa dadi daga bakin mutane daban daban. Abinda nake bukata daga gareki bai wuce ki toshe kunnuwanki ba. Komai yayi farko yana da karshe. Ki mayarda dukkan lamarinki ga Allah sai kiga kinyi nasara." Tayi murmushin takaici "hakane, kuma nagode da shawararka. Dole ne nayi hakuri da dukkan abinda mutane zasu ce game dani da Amatullah. Irin labarinmu dai da wuya yake zama tarihi. Duk wanda ya sanmu duk sanda muka hadu sai sun tuna. Wannan kaddara har jikoki idan da rabo nasan za'a goranta musu wata rana" ta kare maganar da kuka. Tausayin kanwarsa yaji sosai. Ya dade da sanin cewa illar zina tana bibiyar mutum duk inda yaje. Musamman idan akwai haihuwa tsakani. Fatanmu kawai Allah Ya tsare mana imaninmu Ya karemu daga fadawa sharrin shaidan da mukarrabansa. "Ki tsarkake zuciyarki Asmau, daga nan ki barwa Allah komai. Rayuwa ce kowa da irin tasa. Babban abin dubawa dama shine tuba da komawa ga Allah. Idan kika yi haka to babu ruwanki da zancen mutane. Duk wanda ya fiye bibiyar kuskuren dan uwansa don tonon asiri to Allah na kallonsa kuma Shine Yasan yadda zaiyi da bayinSa." Godiya ta sake yi masa har ta kira Shemau tace zata je har gida tayi mata godiya. Dan uwa rabin jiki inji bahaushe...banga mai kamarka ba. Abinda suka aikata ita da Abubakar ba su kadai yake bi ba domin kuwa tasan za'a nuna iyayensu da 'yan uwansu idan dalili ya kawo suma a goranta musu. Kai zina laifi ce mai muni, kazanta ce mai kaskantar da mai daraja. Ya Allah Kasa mufi karfin zukatanmu. Masu neman aure maza da mata Allah Ka basu abokan rayuwa nagari. Mu kuma Ka bamu zaman lafiya da wadanda Ka hadamu dasu. ***** ASP Qasim zaune gaban mahaifiyarsa ya gabatar mata da zancen Asmau wanda ta dade da sanin kudurinsa akai. "Baba ni bazan hanaka aurenta ba. Babanku ma yace ya amince da auren. Abu daya nake so da kai shine ka tuna dukkan abubuwan da suka faru. Naso kwarai kayi aure kafin yanzu ta yadda ko ka auri Asmaun zaka hadata da wata matar" "Inna kenan, kina gudun ita kadai ta kasance surika a gareki saboda tana da 'ya kafin tayi aure?" "Dan nan yau da gobe sai Allah. Mutane da bakinsu bazasu fasa surutu ba" "Amma Inna nasha fada miki ina gudun zamansu da kishiya yaki dadi saboda gori. Da bata dawo ba kamar yadda kika bukata a shekarar nan zan nemi aure. Ku cigaba da yi mana addua." Ta kada kai "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi. Haj Yalwa tace zata zo dasu su gaishe da Malam. Allah Ya kiyaye hanya" Qasim ya tashi ya leka dakin mahaifinsa har lokacin bacci yake yi. Shiryawa yayi cikin wani yadi mara nauyi ruwan toka yayi kyau sosai ya kama hanyar Kano daga Shanono. Ana magariba ya iso. Gidan Mama ya fara zuwa suka gaisa sannan ya kira Asmau ya fada mata zai zo idan an idar da sallar isha. Umma taje ta sanarwa. "Allah Sarki Qasim, gaskiya ya rike amana. Ji yadda yake kokarin kula daku duk da ba a garin nan yake aiki ba. Allah Ya biya shi da mafificin alkhairi." Asmau ta amsa da amin tana gyara goyon Husna da tayi. Suna cikin hira Qasim yayi sallama Umma tayi masa izini ya shigo. Cike da ladabi ya gaisheta ta amsa fuska a sake. Daga nan ta tashi ta bar falon ta koma dakin Hajjo. A nan ta sanar da Amatullah zuwan Qasim daya baban nata ta fito gaishe shi. Qasim ya ajiye kofin lemon dake hannunsa yana maida hankalinsa Asmau. "Asmau magana nazo muyi, ina fata zaki saurare kuma ki fahimceni." "Ina jinka Yaya Qasim" "Asmau kinsan irin shakuwa da abotar dake tsakanina da marigayi Abubakar" Ta gyada kai tana tuno masoyin da bazata taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. "Duk abinda ya gudana a rayuwarku na sani na kuma san nima akwai sa hannuna a ciki. Bazan gaji da rokon gafararki ba saboda ance karfe daya baya amo. Kamar yadda kawa ta ribaceki haka nima nayiwa Abubakar, ga kuma sakamakon hakan duniya ta gani. Asmau tun kafin ki dawo na yanke shawarar aurenki ko a wane yanayi na sameki. Cikin ikon Allah yanzu na tsinci kaina da tsananin kaunarki" A razane ta dago kai ta kalleshi ta mayar da kanta kasa. Yayi sassanyar dariya "Nasan dole kiyi mamaki sai dai kuma ki sani burina ba wai na maye gurbin Abubakar bane. Ina so ki bani dama a matsayin masoyi na sami kaunarki na kuma zama uba ga 'yata Amatullah." Wannan shine ana wata ga wata. Ita fa ko kadan bata son maganar aure ma yanzu. Qasim wani babban jigo ne a rayuwarta saboda yadda ya damu da lamarinta da na Amatullah. Ya rike amanar Abubakar ba da wasa ba. "Yaya Qasim bani da abinda zance maka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103