Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 66

Chapter 66

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai hudu da rabi ake tashin yara. Ga karatun Qur'ani ba kama hannun yaro. Ita dai Asmau sai son barka. Kowa na kokarin kyautata musu. Shemau taso ace a makarantar da nata yaran suke zuwa aka saka Amatullah. Da yake saura sati daya hutun makaranta gwaji kawai aka yi mata suka bata aji, kayan makaranta da litattafai. Karatu sai an dawo zata fara sosai. Abdulhalim ya biya kudin komai. Alh Adamu ya kara masa kudi don kada ya shiga matsi tunda yana da nasa yaran. Amma yaki karba Amatullah 'yarsa ce baya bukatar taimakon kowa. Da ya dawo da ita gida kuwa an sha labarin sabuwar makaranta. Tana ta zuba zance akwai lilo da wurin computer irinta Uncle Yassar. Hajjo da Umma kadai ke amsa mata. Asmau na rike da waya a hannu tana ta kiran Jikamshi ta kasa samu. Bata jima da ajiye wayar Qasim ba yace mata iyayensa suna so a sake basu ranar da zasu dawo. Umma ce ta lura da yadda take ta tsaki ga waya a hannu tana ta dannawa. "Asmau wa kike nema ne haka? Kinsan dai wani lokacin network sai yaki dadi amma duk kinsa abin a ranki sai tsaki kike faman yi." Amatullah tayi caraf tace "kuma ni ta hana ni yi, wai tsaka ce yake yi" Ran Asmau yayi mugun baci ta kai mata duka ta sameta a gefen fuska "ban hanaki idan manya na magana ki saka baki ba. Tashi ki bar wurin nan kafin na kara miki" Kuka sosai Amatullah take yi don har dankunnenta sai da yayi tsalle. Umma da Hajjo har suna rige rigen janyota jikinsu. Umma itama ta harzuka tace "wane irin rashin hankali ne wannan Asmau. Daga tayi magana sai duka." Hajjo tace "kuma dukan ma a fuska, tayi kuskure don ba'a so a koyawa yara saka baki a zancen manya. Amma ya zaki mata hukunci irin wannan. Ji yadda dankunne ya karce ta" Suna kokarin jan Amatullah amma taki tsayawa. Da Hajjo ta saketa jikin Asmaun ta koma tana kuka "Ummi kiyi hakuyi na dena" Kuka Asmau ta saka, tasan bata kyauta ba don fushinta ta saukewa Amatullah. Ga zuciyarta dama ta gama rauni. Bata samun Jikamshi shima baya kira sosai sannan Qasim yana jiran amsarta na ranar da zasu dawo. Amatullah ta sake cewa "Ummina kin hakuya?" Cikin kuka ta rungumeta sosai a jikinta "na hakura Ama" "To ki dena kuka nima na dena"Amatullah ta fada tana share hawayenta. Wannan ya kara karyarwa Asmau zuciya ta cigaba da kukanta bilhaqqi. Umma da Hajjo suka tsaya kallon ikon Allah. Sai da tayi mai isarta ta dauki Amatullah suka shiga ciki. Suna tafiya Hajjo ta rike baki "Bara'atu anya yarinyar nan bata da mutanen boye? 'yan kwanakin nan na lura tana cikin damuwa. Wannan kukan ma da biyu ko uku ma zance take yinsa." "Nima haka nagani, bari naje naji ko menene" ***** Dariyarsu Umma ta fara ji Asmau tana bin Amatullah tana cewa zata shafa mata dettol a wurin da dankunne ya karceta ita kuma tana zagaye gado da gudu. Umma ta rike baki kawai. Asmau da Safinanta sai Allah. Tare suka ga wahalar rayuwa shiyasa shakuwarsu take bawa mutane sha'awa. Sakin fuska tayi ta shiga ta daga Amatullah. "Gudu wurin Hajjo kinji yarinyar kirki." Ta fice kuwa a guje tana dariya. Asmau kunya ta kamata ta ce "Umma kiyi hakuri don Allah". "Bakiyi min komai ba Asmau. So nake ki fada min abinda yake damunki. Ba'a so damuwa tasa iyaye su rinka hucewa akan 'ya'yansu. Amatullah bata kyauta ba da tayi magana amma ba da haka zaki tsawatar mata ba. Ko don gaba ki kiyaye" "In sha Allah Umma. Nagode" Wuri Umma ta samu ta zauna tace "zauna Asmau, magana zamuyi" Murmushi ta kirkiro "babu komai fa Umma, haushi ta bani ne" "To na tashi kenan tunda kina da wanda zaki fadawa matsalarki bayan ni" Daga magana kamar ance fara kuka kawai ta kwantar da kanta a cinyar Umma ta soma kuka. Tausayi ta bawa Umman ta fara rarrashinta "komai yayi tsanani maganinsa Allah. Yakamata ace kece mai fadawa wani hakan. Wa kike nema a waya har abin ya bata miki rai haka" Muryarta har ta dan shake tace " idan mutum ya dena nemanka a waya sosai alama ce ta ya hakura da kai ko, ko kayi masa laifi" Duk da Umma tasan wa Asmau ke so sai tace "waye baya kiranki a waya" Rufe bakinta tayi da sauri. Maganar ce take cinta amma bata yi niyar fada ba. Dan murmushi Umma tayi. Tun ranar da suka hadu da su Hajiya a asibiti kafin Anti Bintu ta koma Zariya ta fada mata yadda suka yi da Col. Ishaq. Ta sauke ajiyar zuciya "Ishaq ne baya kiranki?" Sake sunkuyar da kai tayi ta kasa amsawa. Umma tace "ki yawaita addua da neman zabin Allah nima zan tayaki." Abinda yake ta cin ranta ta kasa boyewa "cewa yayi zaiyi magana da Hajiya, ina jin saboda Amatullah bata amince ba. *Umma nayi kuskure ne da ban zubar da cikin ba na haifeta*? Wannan karon Umma ma sai hawaye "ko kadan Asmau. Haihuwarta shine maslaha gareki damu baki daya. Mun so bin son zuciya da muka dage sai kin zubar da cikinta. Ki duba ki gani yadda Allah Yayita mai kokari da ladabi. Kema kinsan ba iyawarki bace kawai tasa kike da yarinya mai tarbiya kamarta. Mata da yawa da iyayensu sukan gujewa kunyar duniya su zubar da ciki ko a yar da jariri. Sai anje lahira kuma ido ya raina fata. Ga laifin zina ga na zubar da ciki ko kashe jinjiri. Ko ki sami miji ko kada ki samu ki sani cewa rayuwarki ibada ce. Hakuri da tawakkali shine ginshikin farincikin dan adam. Batun Ishaq kuma kada ki damu zai nemeki da kansa ku kare magana. Da shi da Qasim wanda duk Allah Ya zaba miki ko waninsu sai mu ce Alhamdulillah. ABINDA AKE GUDU🙆🏽47 Batul Mamman💖 *Maman Farida mai Hanyar Ruwa. Ina gaisuwa da fatan alkhairi. Ga naki shafin yar uwa* *Amina Yau, Jikamshi yana gaisheki da kyau.* *Shafaatu mai masaukin baki a gidan Batul ina godiya* *Masu sakonnin gaisuwa bazan taba mantawa daku ba. Allah Yayi mana jagora* Sai yanzu Asmau ta dan sami nutsuwa a ranta. Tun da Jikamshi ya dena kiranta sosai ta fara tunanin ko Hajiyarsa ce bata amince ba. Amma yanzu Umma ta kwantar mata da hankali. Zata sake nemansa daga yau zuwa gobe. Idan taji shiru to zata bar komai ga iyayenta. A yanzu dai Umma da Mama Yalwa sun riga sun san da maganar Col. Ishaq. Mama har fada tayi da basu fada da wuri ba sai a asibiti ta ganewa idonta. Asmau ta san bazata bar maganar ba dole ta fadawa Baba. Bayan fitar Umma tashi tayi ta dauko Al-Qur'ani tana karantawa. Neman sauki kawai take a zuciyarta da ke kitsa mata abubuwa da yawa. Adduarta bata wuce idan Jikamshi bazai aureta ba zata mayar da hankali ga karatu, idan kuma iyayenta sun zaba mata Qasim duk da a yanzu sun san bata son shi to bazata yi musu ba. Fatanta bai wuce ta sami juriya wurin karbar duk wata jarabawa da tazo mata ba. ***** Washegari Umma ta gama shirin zuwa gidan Mama suyi

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});