Chapter 7
Chapter 7
mata ido. A can gefe ta zauna idonta a kasa. Anti Bintu tace " Asmau ki dubi girman Allah da halin da kike ciki ki fada mana gaskiya game da cikin jikinki." Kai a sunkuye ta sake nanata musu cewa na Abubakar ne. Ran Umma a bace tace ta tashi ta fita. Ji take inama Asmau tace fin karfi aka yi mata. Da ta tausaya mata amma da jin bayaninta kasan abin ba haka bane. Shawara aka yanke jibi bayan anyi kwana bakwai da rasuwar suje su sanar da iyayen Abubakar. Haka kuwa akayi. Da yawan 'yan bikin sun koma Wushishi sai kadan suka rage saboda abinda ya faru. Babu wanda ya sake zuwa daga gidan Hajjo dama basu sa a ka ba. Umma da Anti Bintu suka je sai Gwaggonsu da Asmau. Mama na ganinsu ta hade rai Umma ta daure ta bukaci ganinsu ita da Alh Adamu. Harda Abdulhalim da Nasiba suka zauna a falon. Gwaggo ta gabatar musu da dalilin zuwansu. Alh Adamu yayi gyaran murya ya soma magana "duk wannan bayanin naji shi tun a ranar da Abubakar ya rasu. Ina sane nayi shiru har sai an share makoki. Bazan boye miki ba Haj Bara'atu wannan labari yayi matukar muni garemu baki daya. Sai dai kuma tsakani da Allah wanda ake abin a kansa yanzu baya raye. Maganar Asmau kadai bazata sa mu karbi cikin jikinta a matsayin nasa ba. Yau da yana nan ne sai ya karba ko ya kare kansa." Tunda ya fara magana Umma ta soma zubar da hawaye.. " Alhaji duk mun shaida Asmau babu wanda take sauraro sai Abubakar. Idan kuka gujemu a wannan lokacin bansan inda zanyi ba. Dangin babansu dama ba kaunar mu suke yi ba, kune dai a garin nan kuka tsaya mana tamkar 'yan uwa....." Mama ta katseta "maganar 'yan uwantaka da cikin shege fa bata taso ba. Kamar yadda Baba ya fada da Abubakar yana raye sai muji ta bakinsa. Amma babu yadda za'ayi mu karbi cikin nan kawai don Asmau tace nasa ne." "To a bari ta haihu mana sai a gwada a tabbatar da zancenta." Abdulhalim ya fada yana kallon Asmau. Shi tausayinta yake ji. Mama tace " zanci mutuncinka wallahi. Idan an bari ta haihu ya dace da dan uwanka zaka karba ka rike ne? Shashasha tashi ka fita." Baba yace "ina zaunen kike irin wannan abin Yalwa?..." ya juya ga su Umma "kiyi hakuri Haj Bara'atu amma babu yadda zamuyi saboda babu kwakkwarar shaida. Idan har kina bukatar taimako kinsan ni mai taimaka miki ne kodayaushe." Yana kaiwa nan ya tashi ya shige ciki Mama tabi bayansa. Nasiba ma ta tashi babu wata magana da suka ji mai dadi. Umma da Asmau sun sha kuka. Suka tashi suka tafi gida jiki babu kwari. Asmau tana tausayin halin da ta jefa mahaifiyarta. Suna zuwa gida hawan jinin Umma ya tashi aka kaita asibiti. Kuka dai yaki karewa a gidan. Kuma aka ki tafiya da Asma'un asibitin. Sai bayan isha suka dawo Yasar yazo dakinsu Asmau ya kirata fuskarsa babu walwala. Tana tashi yayi mata wani kallon banza " idan kika kashe mana Umma wallahi sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. " A razane ta kalli yaron da ta bawa shekara hudu wanda tsakaninta dashi kullum girmamawa ce. Indai Yasar zaiyi mata haka kowa ma dole ya tsaneta. A sanyaye tabi bayansa. Yanayin da taga Umma ya bata tausayi sosai tace "Umma yaya jikin?" Maimakon ta amsa sai tace "munyi magana da wata ma'aikaciyar asibiti tace gobe mu kaiki karfe goma na safe a cire cikin". A tsorace Asmau ta mike tsaye tana kuka "Umma kada zunubin yayi min yawa. Ga laifin ciki ga na kisa. Don Allah ki janye..." Saukar mari taji mai zafi a kumatunta daga Jafar, marin bai gama shigarta ba yace "banza ana son taimakonki zakiyi mana shirme. Waye zai sake kallonki idan aka bari kika haihu? Dubi yadda kika tarwatsa mana gida Asmau. Ki bari a cire indai ba kuma neman karasa zubar mana da kima kike son yi ba." Shema'u ta taso ta rike kafadar Asmau "cire cikin nan shi kadai ne maslaha garemu baki daya. Waye zai dauki dawainiyarki data abinda zaki haifa? Haba Asmau, ki bari muji da bakinciki daya mana." "Ku kyaleta ta nuna min iyakata. Asmau da kinsan irin radadin da nake ji a zuciyata da baki soma bude baki ba ma. Wallahi nayi nadamar haihuwarki, ina ma barinki nayi tun kafin ki zama mutum da dai naga irin wannan bakar ranar a dalilinki." Umma ta fada kuka mai sauti. Hankalin Asmau ya sake tashi sosai da jin abinda Umma dake matukar kaunar 'ya'yanta take fada yanzu. Durkusawa tayi a gabanta tana ta kuka da rokon ta yafe mata. Anti Bintu mai jin tausayinta tace ta fita ta basu wuri. Tana bakin kofar taji Jafar yana cewa ko ta karfin tsiya sai sun kaita asibitin ko a kira likitan har gida a cire. Umma dai bata sake magana ba amma sauran sun amince. Har Gwaggo na cewa akwai wasu saiwoyi da basu fada a asibitin ba sai tasa a kawo daga Wushishi a bata tasha cikin zai zube. Kasa tsayuwa tayi a bakin kofar ta koma daki. Ita da Abubakar sunyi kuskure babba amma tabbas zubar da cikin nan karin laifi ne. A yadda ta janyowa gidansu bacin suna a duniya bazata so ta zama silar karin zunubi a garesu ba a lahira. Da wannan tunanin ta janyo akwati daya cikin na lefenta ta hada 'yan kayayakinta ta zuba a ciki. Dan kudin da ta samu na biki da dan sauran kudinta ta saka a jakar hannu mai girma sannan ta ciro wasu sarka ,dankunne da awarwaron daga wata drawer duk ta saka a ciki tare da wasu kayan kala uku. Ko kadan bata runtsa ba a daren. Asubar fari Jafar da Yassar suka bude gate suka tafi masallaci. Suna fita Asmau ta lallaba ta fice daga gidan tayi hanyar titi. ABINDA AKE GUDU ๐๐ฝ6 Batul Mamman๐ Ta tsakanin gidaje ta rinka bi don kada ta hadu da idon sani idan an idar da sallar asuba sun fito daga masallaci. Ta jima tana tafiya zuciyarta cike da fargaba. Ba ita ta iso titi ba sai da hasken rana ya fara bayyana. Jefi-jefi ababen hawa suke wucewa don ma titin nasu na hotoro wurin wucewar matafiya ne. Kusa da wani kanti da yake rufe ta shimfida dankwalinta tayi sallah sannan ta koma titi ta tare dan sahu. Mutumin ya kare mata kallo sama da kasa sannan yayi magana "Hajiya ina zuwa?" "Tasha zaka kaini." Ta amsa masa tana kara rungume jakarta da akwati. "Garin Kano kuma mai tasha da yawa sai ki fadi wadda zaki je" Sai da ta danyi tunani ta tuno sunan tasha daya " kaini ta unguwa uku, nawa zan baka?" Yadda dreban dan sahun ya kula ta matsu ta shiga yace "kawo dari biyu tunda kinga yanzu safiya ce sosai" Babu musu ta zuba kayanta ta shige tana kare rufe fuskarta da hijabinta. Sai da ta sauka ta fara rarraba idanu domin ko kadan bata san inda zata je ba. Ummanta 'yar Niger state ce to amma tasan zuwa yanzu duk 'yan uwanta sun gama jin labarin komai, idan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103