Chapter 61
Chapter 61
yi dariya sannan ya yiwa Asmau alama da ta biyo shi. Sai da suka je bakin motarsa yace "Matar Jikamshi kin tashi lafiya, ya jikin princess dina?" Tana kallon kasa saboda kunyar tunowa da yadda jiya ta nuna masa tana sonsa tace "lafiya kalau Alhamdulillah" "Yau 'yan kunyar sun zo ne zasu hana ace min I love you" ya karashe maganar yana kwaikwayonta. Bata san lokacin da ta soma dariya ba yace "jiya duk bana cikin hayyacina ne sosai nima bance miki Matar Jikamshi ina sonki ba. Amma yanzu na fada. Zan wuce office sai an taso zan dawo ko kuma bayan magrib. Ki kular min da matata da 'yata" "Allah Ya tsare Ya bada sa'a kuma Ya kareka daga dukkan sharri" Kasa bude motar yayi ya kalleta "Matar Jikamshi" "Naam Jikamshi _na_" Yana murmushin jin dadi yace "komai naki ina sonsa, ki rinka yi min adduar nan kullum don Allah. Kuma idan zamu rabu ki kada ki rinka kirana Jikamshina. Sawa kike naji kamar kada na tafi" Tayi dariya ta sake cewa "Jikamshina" Ya dan marairaice mata "don Allah ki bari" Ta sake bude baki zata maimaita tana dariya yace "kina fada zan wuce wurin Umma na fada mata irin kalaman da kike yi min wanda yasa nake so a daura mana aure a yau dinnan" Ba shiri ta rufe bakinta. Ko dai bai fadi hakan ba tasan zai iya kwatantawa. Dan gefe ta matsa ya shiga motar ya dago mata hannu sannan yaja ya tafi. Ciki ta koma Ainau tana yi mata tsiyar yadda duk su biyun yanzu basa iya boye sirrin zukatansu a gaban juna. Sai shabiyu su Umma suka zo ita da Hajjo da Mama. A nan suka yini don likita yace sallama sai gobe idan numfashin Amatullah ya daidaita yadda ake so" ***** Daga wurin aiki gida Col. Ishaq ya wuce. Bazai iya zuwa wurin Asmau ba sai yayi wanka ya canza kaya. Idan Mami ta iso kuma su je da ita dasu Hajiya. Tun a waje yaga motoci a cikin gidan na kannensa da wata da yake tunanin a cikinta aka kawo Mami. Hakan ya bashi tabbacin yau duk sun zo a tare. Mara motar dama daya ce mai bin auta. Dadi yaji saboda yawanci suna zuwa ne kafin ya taso aiki basu fiye haduwa ba. Ya shiga falon yaji shiru sai daga dakin Hajiya yaji ana magana ana daga murya. Karasawa yayi kofar dakin ya tsaya yana karewa 'yan uwansa kallo. Mami ke binsa sai Ismail, Dahiru, Safiyya da auta Musaddiq. Mami ce take magana cikin matsanancin bacin rai harda hawaye a idonta "wallahi tallahi Hajiya bazamu yarda Yaya ya bata mana suna ba." Ismail yace "meye na rantsuwa Mami, kema kinsan babu mai zuwa cikin su Kawu nema masa aurenta. Idan basu san karuwa bace yarinyar ni...." Tsawa mai karfi Col. Ishaq ya daka masa. Duk sai da suka razana don sun san halinsa sarai. Kirjinsa ke bugu da sauri da sauri saboda bacin rai "ko da wasa kada ka kara kuskuren kiranta da wannan sunan" Safiyya tace "ayi hakuri Yaya, Sayyada zamu kirata ko ustaziyya?" Dariya suka yi dukkansu banda Hajiya ta sha kunu "ban taraku a nan don ku zagi Asmau ba. Yarinyar nan kaddara ce ta fada mata wadda babu wanda ta wuce ta a cikinku. Kuma ni ba amincewarku na nema ba. Na dai fada muku tana da 'ya ne saboda bana son kananan zance nan gaba" Musaddiq yace "haba Hajiya wannan ai ba zancen da ya kamata Yaya zo dashi bane ki karba. 'Yar shege da uwarta bazasu sami karbuwa ba a danginmu." Col. Ishaq yayi kansa ya cakumi wuyansa yana huci. Musaddiq sai kakari yake yi don wahala. Hajiya tana ta cewa ya sake shi amma yaki. Cikin zafin rai yace "Musaddiq kada ka kaini bango. Dukkanku nan babu zaman wanda nake yi. Idan na aureta don Allah kada wanda yazo gidana." "Dama waye zai zo" Safiyya ta fada cikin tsiwa. Ya juyo kama ya mareta. Daga nan suka tararwa yayansu ana ta musayar magana. Hajiya taji babu dadi saboda yaranta akwai hadin kai. Yau daya sai fadawa juna magana suke yi akan Asmau. Ita da tayi laifi shekarun baya amma a yau sanadiyar wannan kuskuren 'yan uwa duka magidanta suna fada. Col. Ishaq yace "an fada muku duk matar da ta haihu ko tayi ciki a waje karuwa ce jikinta ta sayar.?" "Yaya ka fada mana gaskiya fyade aka mata ko me? Ni wallahi gara ka auri gurguwa da wannan yarinyar. Kila ma asiri tayi maka duk ka kasa fahimtar mu " cewar Mami Yau duka 'yan uwan nasa haushinsu yake ji "ba fyade aka yi mata ba Mami. Idan su basu fahimce ni ba yakamata ace kin gane inda na dosa." "Tausayinta kake ji?" Dahiru ya tambaya "ina jin tausayin Asmau saboda irin wannan abubuwan naku ma tun farko taki amincewa da aure. Amma ba don tausayi zan aureta ba. Sonta nake yi so you all should better learn to live with that." "Wai Yaya da kake maganar nan hala ka manta cewa baka *haihuwa* ?" Ismail ne yayi maganar wadda tasa kowa yayi shiru. Hatta Col. Ishaq jikinsa yayi matukar sanyi. Hajiya ta taso rai a bace "Ismail wace irin magana ce wannan? Dan uwan naka kake fadawa magana haka" ta daga hannu zata mare shi Col. Ishaq ya rike hannun idanunsa sun kada sunyi jawur. A sanyaye yake magana "Hajiya gaskiya ya fada. Lokaci daya na manta ina da lalura har nake tunanin yin aure." Ya kalli kannensa daya bayan daya "in sha Allah daga yau na bar zancen auren Asmau. Ismail nagode da ka tuna min da waye Ishaq, ni mutum ne da Allah Ya tsarawa yin rayuwa ba tare da naga nawa dan ba. Alhamdulillah tunda duk kuna da yara bazan ce na rasa gabadaya ba. Allah Yayi musu albarka. Bari na shiga nayi wanka zafi nake ji" Hankali a tashe Ismail yace "Yaya" "Kada ka damu kasan gaskiya daci gareta. Na da dan lokaci idan tayi aure zan manta da ita in sha Allah. Fatana Allah Ya tabbatar da aurenta da Qasim ko wanda ya fishi alkhairi gareta." Yana fita yaci karo da Bilkisu. Hawaye take yi sosai ga tray din abinci a hannunta. Tana jin shigowarsa taje ta hada masa abinci don tasan tunda su Mami suka zo bazai fito da wuri ba. Duk zantunkansu taji komai. Ganinsa baisa ta tsorata ta bar wurin ba. Shima baiyi mata magana ba ya wuce abinsa. Tana nan tsaye taji Hajiya tace "kun bani kunya da mamaki. Ban taba zaton zaku iya juyawa dan uwanku baya ba. Ina cewa Asmau tana da 'ya kuka hau surutu babu wanda ya tambayi garin yaya tayi cikin kafin aure." Cikin nutsuwa ta basu labarin Asmau kamar yadda taji kuma ta gani. Safiyya uwar tsiwa sai ta fara kuka "Mun shiga uku. Hajiya kuji wata muguwar kaddara. Allah Sarki" Mami kuwa cewa tayi "duk da haka Hajiya ai bamu tabbatar da cewa a garuruwan da ta zauna bata taba karuwanci ba. Nima ta bani tausayi amma a bar maganar auren tunda ya fasa shima. Kinsan shi baya magana biyu" Suna ta magana akan halin da Asmau ta tsinci kanta wanda ya girgiza tunaninsu ya kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103