Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

'yan uwansa suka fuskanci yadda suke jifan juna da kallo. Ita duk kunya ma take ji musamman saboda su Hajiya da Mama. Amatullah ce ta kurawa Ismail ido tace "kai da Babana iyinku daya. Kaima sunanka Jikamshina?" saboda irin kamaninsa da Ishaq. Ya Salam, Asmau ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige. Allah Ya taimaketa ma Amatullah bata ce irin yadda Ummia ke fada ba. Don kadan daga aikinta ne yin hakan.Col. Ishaq kansa yau yaji kunya karo na farko a rayuwarsa game da fadin magana a gaban kowaye batare da yaji komai ba. Su Musaddiq sai kallon kallon kallo ana dan murmushi. Ismail kuwa yace mata "nima babanki ne 'yan mata" ya karasa wurin gadon da murmushinsa. Ta kalli Col Ishaq tayi masa gwalo " Babana kaga nayi sabon baba ko. Ni yanzu na dena yin baba da kai" Yace "subhanallahi me nayiwa princess dina haka. Kai Ismail tashi ka bani wuri mu sasanta ni da 'yata" 'Yar dramarsu tasa mutanen dakin dariya. Amatullah tayi saurin rike hannun Ismail tace "yanzu baka wasa dani sosai sai da Ummi na. Nima ga sabon Baba nayi" Asmau ta rasa abin cewa. Tsiyar yaro mai surutu fa kenan. Yau Amatullah ta gama bata kunya. Safiyya tace "amma da baban nan naki da Ummi basu kyauta ba. Yanzu ga sabo nan mun baki. Amma kiyi hakuri Babanki so yake ku koma gidansa sai ku rinka wasan tare kullum shiyasa yake yi da Umminki" Kana gani kasan Amatullah taji dadin wannan zancen tace "Ummi kuje kuyi wasa da Babana to idan kun gama mu koma gidansa." Yau kam ta kai karshen jin kunya, shi kuma Col. Ishaq saboda shawarar da ya yanke ta rabuwa da ita shiyasa yau bai bada amsar da zata karasa bata kunya ba. Hajiya da Mama Yalwa sai sunkiyar da kai suke. Ita Mama harda mamakin dama son Asmau sojan nan yake bata sani ba. Ismail ji yayi ta shiga ransa. Dama yana son 'ya mace gashi duk maza gareshi. "Ki kyale wancan Baban kawai kinga a gidana zan siyo miki kayan wasa da alawa" Tace "ai Ummi ma tana siya min. Ta hanani kwadayi. Kuma bana yi sai tace min Allah Yayi miki albayka" Yarinya karama sai basu sha'awa take yi. Mami kallon Asmau take yi. Yanzu mace mai kamannin kamala irin haka ace a waje ta haihu. Kai wannan duniya mai rudin bayin Allah. Amatullah ta sake cewa "sabon Babana in kayanta maka Allahu?" Dahiru yace mata "karatu ake cewa ba kayatu ba" Tuni ta bata rai "kayatu fa nace ba kayatu ba" Daki ya kaure da dariya. Col. Ishaq yana kallon yadda 'yan uwansa duk suka mayar da hankali gareta. Murmushi yayi yana fatan ko nan gaba idan ya roki alfarmar a bari tazo gidansu ta yini wurin Hajiya bazasu yi mata gori ba. Ido suka hada da Asmau tayi murmushi sai taga ya dan sunkuya kamar zai duba waya. Bata kawo komai a ranta ba. Ismail ya samu shiga wurin Amatullah yace "karanta min a kunnena ni kadai kada su ji" Ta fito da ido da mamaki "Ummi fa tace mai yada mai yada dan wuta, mai ji mai ji kafiyi." Nan dariya aka yi suka ce to sai ya kiyaye yarinya tasan rada babu kyau. Daga kai yayi ya kalli Asmau ta danyi murmushin jin kunyarsa. Su Mami suma mamakinta suke yi. Ga dai ta yadda ta haifi 'yar nan amma ga dukkan alamu tana da tarbiya sosai. Tunda ta bude baki ta fara karanto sunayen Allah gudu biyar da tsallake. Musaddiq ji yayi inama 'yarsa ce. Ga muryarta akwai dadi tana yi kamar da addu'a "YA RAHMANU YA ALLAH-AMIN YA RAHIMU YA ALLAH-AMIN YA MALIKU YA ALLAH-AMIN...." Haka tayi ta yi har karshe. Mami ta y kurawa Asmau ido, yarinyar bata da makusa sai abinda tayi a baya. Idan har aurenta zai sa dan uwanta ya dawo mata kamar da, to zata amince da auren nan. Sai dai fa dole su shirya da jin surutu da gorin 'yan uwa da sauran mutane. Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Arewa hausa novels Novels villa Duniyan novels Hayat hausa novels Hausa novels and fashion And Cool novel, makeup and cooking) WHATSAPP NO: +2347039625239 ABINDA AKE GUDU🙆🏽46 Batul Mamman💖 Surutun Amatullah ke tashi a dakin da masu biye mata. Tsakani da Allah ta shiga zuciyar Ismail. A ransa ji yake ina ma yarinyar nan ta cika 'ya kamar kowa. Ta tashi har karshen rayuwarta bazata taba jin wata magana mai muni game da haihuwarta ba. Col. Ishaq kuwa Asmau har ta gaji da kallon inda yake tsaye. Duk iya yinta ta kasa yin sa'ar kallonsa a daidai lokacin da yake kallonta. Shi kuma yana sane yake dauke kansa daga gareta idan yaga ta dago nata kan. Duk son da yake mata dole ya rabu da ita indai tsakaninsa da Allah yana son farincikinta. Duk wani tanadi da yake yi mata da Amatullah maganar Ismail ta rusa komai. Zaiyi kokarin taimakonta ta kowane fanni na rayuwa musamman karatu da tace tana son komawa. A shirye yake ya dauki nauyin hakan idan bazai kawo matsala tsakaninta da wanda ta aura ba. Ko kawai ya hada kudi ya bata a matsayin gudunmawar aure. Shi kadai yake ta tunaninsa har su Umma suka shigo ita da Anti Bintu da Shemau. Ba haka su Mami suka tsammaci ganin dangin Asmau ba. Gashi dai suna da rufin asiri sannan ga hadin kai. Wani abin mamaki wai harda babar wanda yayiwa Asmau ciki ake jinyar Amatullah. Mamakinsu bai karu ba sai da Alh Adamu ya shigo. Mutum mai fara'a jan mutane a jiki. Ya gaisa da kowa sannan ya zauna yana tsokanar Amatullah. Lokacin dakin ya cika sosai shiyasa Haj Lubabatu tace su tashi su tafi. Tun daga kan Mami har Musaddiq sun yaba da 'yan uwan Asmau. Kaddara kam babu inda bata giftawa. Kuma idan ta ratso kamata yayi dukkan musulmin kwarai ya karbeta hannu bibbiyu. Ashe ba daidai bane idan 'yar mutum tayi ciki ko zina a kyamaceta a koreta. Hakan ba komai zai kara musu ba sai bushewar zuciya idan basuyi sa'a kamar ta Asmau ba. Ba'ace a nuna musu sunfi kowa ba ko a shafe girman laifinsu a mayar dasu kamar komai bai faru ba. Amma a jasu a jiki ta hanyar nuna musu kuskurensu da wajibcin tuba da nesanta daga aikin dana sani. Asmau ta zama babban misali. Duk da iyayenta sun yafe mata kuma ta tuba amma fa har abada da gaban abada idan akwai baza'a taba mantawa ba. Ita da ta manta da haka a rayuwarta sai ranar da taji ance *shiga aljannah cikin aminci*. Ya Allah Kasa mu dace. Ita da Anti Bintu suka fito rakiya. Sai a lokacin suka hango Bilkisu da Yassar a wurin wani benci. Kusan kowa ya manta dasu ma. Duk abinda taji daga bakin iyayenta da kakarta ta tambayi Yassar ya tabbatar mata da haka ne. Bilkisu tayi kuka sosai taji tausayin Asmau. Ta fada masa shawarar da kawunta ya yanke na rabuwa da Asmau saboda matsalarsa. Nan fa hankalin Yassar ya tashi. Bai ga wanda ya dace da yayarsa ba kamar Col. Ishaq. Suna wannan tattaunawar ne suka hango fitowar su Ismail. Bilkisu ta rasa inda zata saka kanta

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});