Chapter 21
Chapter 21
murmushi "nagode" "Kaci abinci ko na kawo maka? Bana son ka tafi da yunwa". Abincin ya bukaci ta kawo masa. Ta tashi tana tafiya mai daukar hankali. Har ta shige kitchen ya kasa dena kallonta. Sai da ta bace yace _Astagfirullah_ tare da kudurta niyyar zaice ta suturta jikinta sosai. Tana dawowa kujerar gefensa ta zauna kamshin turarenta ya bugi hancinsa sai ya fasa cewa ta rufe jikin. Yana matukar son Asmau amma yau harda wata muguwar sha'awarta ce ta taso masa. Yana cin abinci suna hira kadan kadan domin duk hankalinsa ya koma kan halittar jikinta. A nata bangaren ta lura da canjawarsa kuma taji dadi a ranta. Da ya tashi zai tafi dubu biyu ya miko mata kudin motar makaranta. A da sai ya bata sau uku bata karba ba har suyi fada wani lokacin. Amma yau kawai don taji hannunsa a nata ta mika hannun a kunyace tana kallon kasa. Tana sane tayi hakan hannunta ya kai kan nasa maimakon kudin. Saurin dauke hannun tayi saboda wani yanayi na daban da taji (dama shaidan komai kankantar haram dada mata dadi yake fiye da yadda take don kawai a cigaba da aikata ta) "yi hakuri ban kula ba" Abubakar yaji dadi fiye da yadda taji domin tana taba hannunsa ji yayi kamar ya janyota jikinsa. "Dama ina zaki kula kina wani sunkuyar da kai kasa. Ni zan tafi sai friday in sha Allah. Ki kular min da Asmy na". Tana murmushi tace " nima ka kular min da Yayana. Allah Ya tsare Ya kaika lafiya." Haka Abubakar ya tafi surar Asmau tana yi masa gizo. Sawa yayi a ransa idan sunyi waya zai fada mata ta dena irin shigar nan har sai sunyi aure. Sai dai yana isa bayan sallar magriba wasu hotunanta suka shigo wayarsa. Duk babu wanda tasa dankwali kanta wasu ma rigunan sun dameta fiye da rigar dazu. Bai iya yi mata maganar da yayi niyya ba ya rasa dalili. A haka suka kwashi wajen wata biyu. Asmau ta dena jin kunyar fita gabansa da shigar bayyana jiki indai tayi sa'a yazo Umma bata gida. Mayafin nan kullum a kafada an baza gashi ta kasan dankwali. Tun yana tsanar kansa idan suka rabu har ya saki rai yana jindadin hakan tunda yasan aurensu yana kusa. Kusa da juna suke zama yanzu ana hira sai su rinka neman hanyoyin taba hannun juna kowa yana nuna kamar ba hakan bane a ransa. Sai yanzu Asmau ta yarda suna soyayya domin tafi jindadin alakarsu. A zuciyarta ta kwantar da hankali tunda tana da yakinin aure zasuyi kuma dai ana aure komai ya wuce. Ita yanzu babban burinta yayi kissing dinta ko sau daya ne yadda take karantawa. Ayi kiss amma sai a nuna kamar bisa kuskure ne ko kuma a nuna na komai yin hakan a addini da al'adarmu. A nasa bangaren shima ya dena damuwa. Kullum sha'awarta karuwa take yi a ransa hakan yasa ya soma rasa nutsuwarsa. Bashi da aiki sai azumi kamar mai kaffara amma wasu ranakun shi kansa yasan a irin tunanin Asmau da yake yi na tsantsar sha'awa azumin nan baya kaiwa ko ina. ***** Su Asmau an gama jarabawa kuma wannan karon suna dawowa makaranta idan aka sake hutu za'ayi bikinta. Ko sati ba suyi ba da fara hutu Anti Bintu tazo Kano ziyara. Kwananta biyu mijinta yazo da zasu koma tace da Asmau zata tafi. Umma bata musa mata ba ta umarceta da hada kaya. Murna tayi sosai Aina'u kuwa ansha kuka gashi ba'ayi hutu ba. Abubakar yaji dadin komawar Asmau Zariya wani satin da ya zagayo ko Kano bai je ba. Mama Yalwa tace ta gane dama zuwan ba nasu bane na Asmau ne. A gidan Anti Bintu yake zuwa su sha hira wadda a hankali ya fara rungumarta da sunan zaiyi kewarta idan ya tafi. Su biyun duk sun san haramcin abinda suke yi amma sunyi nisa. Suna haduwa duk yakin da suka shirya da wannan sabuwar dabi'ar tasu sai ya rushe. Anti Bintu ko kadan bata san me suke yi ba. Falonta take bar musu idan yazo. Nutsuwa da tarbiya irin ta Asmau da Abubakar babu wanda zai taba zargin haka tsakaninsu. Wata rana bayan asuba karamin dan Anti Bintu Haidar yana toilet bayan ya gama ya fara kiran Asmau tazo tayi masa tsarki. Lokacin ko bakwai na safe bata yi ba duk baccin da take ji taki komawa saboda an turo cigaban wani labari da take karantawa. Ko yunkurin tashi bata yi ba tace masa tana zuwa. Haidar ya kirata yafi sau biyar tana cewa gata nan har Anti Bintu ta fito daga kitchen tayi masa tsarkin lokacin har ya fara kuka. Duk abinda suke yi da Asmau ta ji. Dakin nasu ta shiga Asmau tayi nisa a duniyar labari sai ganin Antin tayi a tsaye a gabanta. Da sauri ta tashi a tsorace zata fita. "Dawo indai tsarki zaki yiwa Haidar nayi masa" Duk sai taji kunya sannan ta gaisheta. Anti Bintu ta dauki wayar da ta ajiye akan gado ta bude ta dan karanta wani bangare na labarin. Tayi scrolling sama kuma irin sakon nan ne na kwanciyar aure. Jikin Asmau kamar mazari don tsoro ta gama rudewa. Anti Bintu ta kama hannunta ta zaunar da ita a bakin gado sannan taja kujerar gaban mudubi ta zauna. "Kin bani mamaki Asmau. Wannan wane irin text ne kike karantawa? Yanzu kwanciyar aure har sai wata can da baki sani ba ta koya miki? Wannan abu halitta ce wadda idan lokacin yinta yayi baka bukatar malami. Idan kuma har akayi rashin sa'a mace ko miji suka matsala ta fannin gamsar da juna to ba duniya zaki fadawa matsalarki ba. Mutum daya zaki samu cikin 'yan uwa ko abokan arziki wanda zaki iya bawa amanar sirrinki sai ki fadi matsalar a baki shawara. Amma me ya kaiki karanta irin wannan post din wanda ko matar aure ce ta karanta da wuya idan bai karya mata alwala ba saboda yadda ake bayani 6aro-6aro. Kada ki bari kawayen banza suce ya kamata a koya miki irin wannan tunda kin kusa aure. Komai yana da lokaci. Kodayake masu rubutawa sunfi kowa laifi tunda kayi rubutu ne baka san iya idanunwan da zasu karanta ba. Wayar nan yarinyar da bata fara jini ba ma tana da ita kuma akan same su a groups din manya suyi ta sakin baki a gaban 'ya'yan cikinsu. Wani lokacin sai su tura yara masu karfin sha'awa su karanta a tayar musu da hankali su fara neman mafita. Ki rufawa kanki asiri ki dena karanta abinda bazai amfaneki ba. Abu na biyu wannan novels din da kike karantawa. Nima babarki ina karantawa amma ki sani akwai wanda har ki gama babu wani darasi da zaki dauka sai bata lokaci da tabarbarewar tarbiya. Uwa uba kuma wannan mugun son da muke yiwa labaran yana sawa mu manta da al'amuran da suka fi bukatar hankulanmu. Tun zuwanki gidan nan na fuskanci kin canja sosai. Kina idar da sallah ko azkar baki gama ba sai ki janyo waya. Har akwai wani labari da zaisa ki kasa hakurin minti biyar ki bautawa Allah cikin nutsuwa? Mata irinki da yawa gasu nan. Sau nawa girki yake konewa ko mace ta yini cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103