Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 29

Chapter 29

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kofa ta bata hanya ta wuce. Yaya Tagwai ta soma kiran Sada, Asmau ta fada mata sun fita. "To tunda saboda ke dama nazo ki fada min iyakar gaskiyarki. Shin cikin nan na Sada ne ko wani wanda ya sani? Asmau ta girgiza kai tana hawaye. "Alhamdulillahi tunda ba cikinsa bane ina so yanzu yanzu kafin su dawo ki fita ki bar gidan nan." Gwiwa a kasa Asmau ta durkusa tana rokonta. Yaya Tagwai ta dubi Habu "Kai da nazo da kai meye amfaninka ne? Ja min ita ka datse kofar gidan. Wallahi idan kika sake dawowa gidan nan sai na kirawo miki 'yan sanda. Haka kawai kin tsaface min yara basa jin maganar kowa sai taki. Kin gama karuwancinki zaki nemi bayin Allah ki hadasu da wahala. In dai cikin nan ba na dana bane to ki kama gabanki". Asmau tana kuka tace "ki taimakeni don girman Allah. Bani da wurin zuwa idan na tafi." Yaya Tagwai ta harareta "daga bishiya kika fado da zaki ce baki da wurin zuwa? Tun wuri ki koma gaban iyayenki." Ta sake cewa Habu yaja Asmau sai ya kasa saboda tausayinta da yaji. Yaya Tagwai tace "Idan baki fita ba zan sa iyayensu su zare hannuwansu daga kansu. Idan baki sani ba ina so kisan cewa ina da wannan ikon da kannena". Jin haka Asmau ta juya zata shiga dakin ta debo 'yan kayanta. Yaya Tagwai ta tsare kofar dakin. "Bazan bari ki sake shiga ba bare ki kunna wani tsafin nima naji ina sonki. Fita tun kafin nayi yekuwa a unguwar nan nace ke mayya ce". Habu ma sai da yasa baki akan ta bari ta dauko kayanta amma taki. Haka ta ja hannun Asmau daga ita sai kayan jikinta Allah Yasa da mayafi tayi waje da ita ko takalmi babu. Kuka take yi sosai amma a haka Yaya Tagwai ta ja hannunta har suka bar layin. Sai da suka yi nisa ta jefa mata naira dari biyu. "Matsiyaciya sai ki dauka ki kara gaba wasu masu tsautsayin su dauke ki amma ba gidan 'ya'yana ba. Allah Ya isa idan kika dawo." Kukan Asmau ba karamin tausayi ya bawa Habu ba amma yana kallo tayi gaba Yaya Tagwai ta kama hannunsa suka koma gidan Sada. ***** A gidansu Sada ne Baaba Ta Annabi ta fada musu tun dazu Yaya Tagwai ta tafi gidan nasu. Suna jin haka suka kama hanyar gida hankali a tashe. Suka yi rashin sa'a titin da ya biyo wata mota ta lalace ta hada uban goslow. Kusan tsalle Rashida tayi da suka iso gida ta fito daga dan sahun. Tana shiga ta tarar da Yaya Tagwai tana yin boli boli da kayan Asmau. Kuka ta saka tana tambayarta ina take Habu yace ta tafi. Sada na jin haka cikin fada ya tambaye shi hanyar da tabi ya kwatanta masa. Tare suka bi hanyar ko zasuyi sa'ar ganinta. Sai dai sunfi awa biyu suna nema daga baya wani yace ta shiga wata bus amma bai san inda bus din tayi ba. Da suka dawo gida Rashida ya gani a tsakar gidan ta rungume kayan jariran da Asmau take tarawa tana ta kuka. Yaya Tagwai tace "idan kin gaji kya yi shiru. Irin wannan kuka da kike yi sannan ace ba aikin asiri bane." Ayatul Kursiyyu ta shiga karantawa tana tofawa Rashida a ka wai maganin sihiri. Sada ya dagata ya shigar da ita daki tana ta kuka. Habu da Harira kuwa sai kallo. Yaya Tagwai ko a jikinta. Tasan komai daren dadewa zasuyi mata godiya saboda ta rabasu da masifa. ***** Yaya Babba ke bacci harda minshari Zubaida ta samu ta lallaba da kyar ta fito daga gidan. A iya watannin da tayi duk shegantakar karuwanci 'yar tsohuwar nan ta koya mata. Tun tana nuna bata so har ta hakura tana biye mata saboda a rage matakan tsaron da aka saka mata. Bata taba yarda wani yayi amfani da ita ba. Tace sai ta koma gidan Uwargida. Yaya Babba bata damu ba ita dai aikin da aka sakata tayi. Tunda tazo gidan sai yau ta samu damar fita. Kullum tana tunanin Asmau. Bata sani ba ko ta haihu yanzu. Gidan Uwargida ta tafi da niyyar idan Asmau tana nan su gudu tare. Daga bakin kofa ta hadu da wata cikin matan gidan. "Zuby kin dawo?" Ta fada tana kallon irin shigar Zubaidan da yadda ta kara cikowa. Zubaida ta rage murya "Shiga ki kirawo min Asmau bakuwar nan. Don Allah kiyi sauri ga wannan kada ki fadawa Mama kin ganni." Dari biyar ta bawa matar ta karba sannan tace "wannan bakuwar baki dade da tafiya ba ta gudu. Har an sami wasu bakin biyu bayan tafiyarta." Zubaida tayi wani murmushi cike da jindadi."Alhamdulillah nasan taji shawarata ta koma gidansu." Daga nan ta dauki jakar kayanta ta juya ita ma. Matar ta biyota tana tambayar ina zata je Zubaida tayi gaba ko kulata bata yi ba. Daga nan bata zame ko ina ba sai tasha ta nemi motar Kano. Basu dade ba motar ta cika suka hau titi. Indai bata manta ba Asmau tace sunan umguwarsu Hotoro layin kwamishina Adamu. Gidansu zata nema don tasan in Allah Yaso yadda Asmau ke bata labarin Umma zasu riketa har ta sami mijin aure. Ta dan yi murmushi "ko me Asmau ta haifa" ko meye ma zata tayata raino tunda dai taji shawararta ta koma gida. Allah Yasa dai ta gane gidan. ABINDA AKE GUDU🙆🏽24 Batul Mamman💖 Zuciyar Asmau banda zafi babu abinda take yi. Ji take kamar ta haye tsakiyar titi mota tayi gaba da ita kowa ya huta. A tunaninta babu sauran mai kaunarta a duniya. Tana wannan jan kafar ne taji kwandastan wata hayis yace Hajiya zaki hau? Kai ta gyada tare da shiga motar da bata san inda suka nufa ba. Sunyi tafiya mai dan nisa wasu na sauka wasu na hawa kwandastan nan yana ta tambayarta kudin mota hankalinta baya wurin saboda kukan da take yi. Wata mata ce a kusa da ita ta dan taba ta sai ta kula da yadda kafafun Asmau suka yi futu-futu ko takalmi bata dashi. A tsorace matar ta ja jikinta gefe ta karewa kodaddun kayan jikinta kallo. Daga murya tayi iya karfinta tace "mahaukaciya ce" Nan da nan hankalin jama'a ya dawo kanta aka fara cewa za'a sauka. Dreban hayis din ya hau yiwa kwandasta fadan ya dauko musu mahaukaciya. Tsayawa yayi suka janyo hannunta aka fitar da ita daga motar. Bakincikin da take ji ya hanata magana. Wai yau ita ake yiwa kallon mahaukaciya. Tana kallo motar tayi gaba sannan ta kula da cewa inda take ya danyi wajen gari babu gidaje sosai. Ga wani irin ciwon baya da mara da ya taso mata lokaci guda. Runtse idonta kawai tayi tana tafiya zafin kwalta yana kona mata kafa sai ji tayi an taka burki da karfi motar tayi wata irin kara. A razane ta bude idonta. Wata mota ta gani mai kyau ashe da tana tafiya ta dan hau titi bata sani ba. 'Yan samari biyu ne suka fito suna ta zaginta ta uwa ta uba. Dukkansu bata jin akwai wanda ya shekara ashirin sai tsayin kafa kawai. Kayan jikinsu sun nuna yaran sun fito daga gidan arziki sai dai

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});