Chapter 43
Chapter 43
a gefe ya fita. Col. Ishaq yana zaune akan kujera yana yiwa Amatullah wasa da tambayar ya jikinta. Asmau duk ta takura ta rasa abin yi. "Ki zuba mata abinci mana idan ke baki jin yunwa." Wai mutumin nan ina ruwansa da ita ne. Me yasa ya kara dawowa ma. Ta danyi tsaki a hankali sannan ta hada abincin ta zauna a daya gefen zata bawa Amatullah ya miko mata hannu alamun ta bashi plate din. "Kema ki zuba kici". Gefe kawai ta ja tana kallon ikon Allah. A baki ya rinka ciyar da Amatullah tana ta yi masa surutu. Asmau tana satar kallonsa. "Abinci nace ki zuba ba kallona ba" Ya Salaam! Ba karamar kunya taji ba ta tashi da sauri ta zuba abincin ta dawo tana tsakura da cokali. Ya tashi saboda ya fuskanci kunyarsa take ji. "Safina bari na je naga likitan da ya dubaki na dawo" Fita yayi ko waige babu. Asmau ta tuttura abincin kada ya dawo ya sameta. ***** Tambayoyi ya yiwa likitan game da ciwon Amatullah. Da ya fito ya tsaya bata lokaci don ya bata damar gama cin abincin. Gara da Allah Yasa yayi tunanin kawo musu abincinsa da yake tafiya office dashi ba don haka ba don ganganci fita zata yi ta bar yarinya ita kadai a daki. Wasu na nema ido rufe ita ta samu bata rike da kyau ba. Kafin ya dawo ta gama ta dauke plates din ta dauraye a toilet. Ya shigo yayi mata alama da ta fito waje. Darajar girmansa da take gani da tsoronsa da take ji a yanzu yasa ta fita. Ta tsaya can gefe ta sunkuyar da kanta. "Da ban zo ba sai ki fita ki Safina ita kadai a daki? Kuma shine harda koya mata karya. Allah kadai Yasan me kike koya mata kafin yanzu" Taji haushin maganarsa ta dago kai zata yi masa rashin kunya "ina ruwanka da abinda nake koya mata". Yanayin kallon da yayi mata kadai yasa ta kawar da kanta gefe "Ni kike fadawa haka?" Da wadanda ke karkashinsa zasu ji abinda ta fada kila idan ta fara tsallen kwado sai kafarta ta kumbura. Lallai tana da tsaurin ido. idan kayan jikinsa basu yi mata kwarjini ba ai shekarun da yake jin zai bata shabiyar ko sama da haka ya isa yasa taji kunyar idonsa. Da yake rashin kunyar ba dabi'arta bace sai taji babu dadi "kayi hakuri wallahi nagode da taimakon da kuka yi min. Abinda kaji na fada mata ma don babu wanda zai zauna min da ita ne" "Its ok, zan aiko muku da abinci anjima saboda haka kada ki fita ki barta ita kadai." "Nagode" "Har yanzu baki kira kowa a gidanku ba?" "Uhmmm sun ce zasu zo anjima". "Maman Safina kin iya karya" ya fada yana shafa kansa. Asmau taji kamar ta nutse a wurin. Kai wannan mutumi da bin kwaf yake. "Ance gobe za'a sallameku. Na fadawa likitan kada yayi sallamar sai nazo" Ta dan bata rai "saboda me"? "Saboda na kamaki da kyau. Ina son sanin inda zaki kai min 'ya idan kin fita daga nan" Cikin dakin ya koma ya cewa Amatullah zai je office ya dawo. Har da kukanta ita zata bishi. Asmau ta kalleta bayan ya fita a ranta tace ki gama ganinsa da kyau kafin ki dena ganinsa. Da yamma Haj Lubabatu ta saje dawowa har take tambayar Asmau ina iyayenta. Tace mata yanzu suka tafi za'a kawo musu abincin dare. Hajiya tace "ai mun zama daya nasan zamu hadu ko ba yau ba". A zuciyarta tana kokonton ko da gaske sun zo. Babu wani alamar kayan dubiya ga akwatunansu Asmau a gefe wanda ya kamata ace an tafi dasu gida. Da Ishaq ya koma gida da daddare sai da ta fada masa. Yace shima yana son bincike ne a kanta ko don yarinyar da take tare da ita. ***** Sai wurin karfe tara na safe Col. Ishaq ya dawo washegari amma sau biyu yana aika musu da abinci har da kayan kwalama na yara. A lokacin aka basu takardar sallama da magani. Sauran kudin da ake binsu duk yaje ya biya mutumin da ya kawo musu abinci ya kinkimi akwatunanta. Asmau ta dakatar dashi yace Yallabai ne ya saka shi. Dauka kawai yayi zai fita Ishaq ya shigo yace ya wuce dasu gidan Hajiya zasu biyosu a baya. "Bangane ba" Asmau ta fada a tsorace. "Nima namu gidan zam wuce don Allah kace ya ajiye min kayana" "Kinga ki wuce muje akwai tambayoyin da nake so nayi miki daga nan nayi alkawari zan kaiki gidanku da kaina." "Ni bazan bika ba, haka kawai na sani ko....ko..." Yayi murmushi "karasa mana. Ko satar mutane nake yi. Nima tsoron da nake ji kenan ko sato Safina kika yi". Idonta har ya ciko da hawaye tace "wallahi 'yata ce, don Allah ka barmi mu tafi." Fita taga zaiyi daga dakin tace cikin kuka "zanyi maka ihun barawo" Col. Ishaq yayi dariya ya kalli Amatullah "Safina ina babanki?" Ta sake lafewa a jikinsa "ga ka" "To kinji, idan kina son 'yarki ki biyoni. Taimakonki nake son yi albarkacin wannan yarinyar" "Bana son taimakon ka bani 'yata...." tafiyarsa taga yayi dole tabi bayansa tana dan gudu gudu saboda yadda ya soma yi mata nisa. Gaban wata mota mai kyau suka tsaya baka ya bude gaba ya ajiye Amatullah wanda dadi ya isheta sannan ya zagaya ya zauna a wurin dreba. Babu yadda Asmau ta iya dole ta bude baya ta shiga. Suna hada ido ta mudubi ya kashe ido yana murmushi ita kuwa ta murguda masa baki. Shi da Amatullah suke ta hira tana bashi labarin gidansu Umma Zulaiha. Gidan Hajiya ya wuce dasu zuciyar Asmau tana ta daridari. Duk kunya ta dameta haka tabi bayansa suka shiga gidan. Haj Lubabatu ta tarbeta cikin fara'a aka kawo musu abinci. Col. Ishaq yace Bilkisu taje ta yiwa Amatullah wanka. Asmau tabi bayansu da ido yarinya sai murna takeyi ta sake dasu. Hannunsa ya dan kada a gabanta ta dawo daga tunanin da take yi. Yace "Malama Asmau ina ganin ya kamata ki sanar damu ko ke wace ce. Hajiya ma ta fahimci akwai abinda kike boyewa shiyasa na kawoki nan ki fada mana a gabanta." Asmau ta soma hawaye "naso ace yadda muka hadu cikin mutumci mun rabu a haka batare da na tonawa kaina asiri a duk inda na tsinci kaina ba" Hajiya tace "kada kiga kamar mun takuraki, rayuwar Safinatu muke dubawa shiyasa. Idan har baki da wurin zuwa ga yarinya mai lalura lallai kina bukatar taimako" "Ina da iyaye da 'yan uwa. Kuma a garin nan muke" Col Ishaq yace "to me ya rabaki da gida har kika kasa fada musu kuna asibiti"? Asmau tayi ajiyar zuciya sannan ta basu labarin rayuwarta. Tun Haj Lubabatu tana kada kai ha[truncated by WhatsApp] ABINDA AKE GUDU🙆🏽33 Batul Mamman💖 Gidan suna dai ya koma wurin zuwa kallon Asmau da 'yarta. Bayan anyi sallar la'asar ne ta tuna da Col. Ishaq da ya kawo su. Dafe kai tayi saboda tasan bata kyauta ba. Ganin su Umma yasa ta manta da kowa. Shema'u ta fadawa cewa dan matar da suka zo tare shi ya kawosu kuma yana waje. Haj Lubabatu tana jinsu sai dai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103