Chapter 10
Chapter 10
pure water. Yunwa take ji sosai. A gefen wurin sallar ta zauna taci abincin. Da akayi la'asar ta sake yin sallah ta kuma samun wuri ta zauna. A nan dai magariba da isha suka riske ta tayi sallolinta cikin fargaba. Ga dare yana yi gashi bata da wurin zuwa. Bayan tayi Isha ne hankalinta ya kai kan akwatinta. Dama jakar na kafadarta. Akwati dai babu shi babu dalilinsa wani ko wata ya dauke batare da ta sani ba. Bakin cikinta ya karu ta soma kuka. Ita ga tsoro bare tayi cigiya. Tana kallon yadda mata ke fada a cikin tashar da maza amma bazata iya ba. Tayi sa'a ma akwatin babu kudi a ciki. Tana wannan kukan ne taji muryar wani daga gefenta yace "Gani nazo sai kizo mu tafi." "Mu tafi ina?" Ta fada a tsorace ga wurin babu wadatar haske. Wata dariya mutumin yayi. Babba ne don a kalla zai shekara hamsin. Yasa riga da wando na yadi ga taba a hannunsa. Bakinsa kuwa hakoran Makkah ne har biyu daga sama. Tsoro ne ya sake shigarta ta dan matsa baya. "Kinga ki kwantar da hankalinki yarinya kinzo gida. Irinku sunfi a kirga da nake taimakawa a tashoshin garin nan." Ya dan zuki tabar sannan ya sake kallonta. " ki taho mu tafi idan ba a tashar nan kike son kwana ba 'yan iskan gari su danneki anjima kadan.." Asmau ta manne jikin bango zuciyarta na dukan uku-uku "Don Allah ni dai ka kyale ni." Mutumin ya girgiza kai alamun ya saba jin irin haka. "Kinga 'yata ta kaina. Ni dinnan da kike gani ba cutar dake zanyi ba. Billahillazi masauki zan kaiki." Cikin tsiwa tace "bazani ba" Ya dan tabe baki "kinyiwa kanki, irinku- irinku yawa garesu. Ku fito daga gidan iyayenku duk garin da kuka ga mota zata kuje. Sai kun sauka a tasha kuke gane kunyi kuskuren barin gida. Irina kuma sai mu nuna muku cewa ku kadai zaku iya rayuwa batare da iyaye ba. Akwai gida na mata zalla dama can nayi niyar kaiki saboda kwanan tasha ga zukekiyar mace irinki ba karamin hatsari bane." Maganganunsa kara tsorata Asmau suke yi sai dai haka kawai bazata bi mutumin da bata sani ba. Dauke kanta tayi ya gaji da tsayuwa ya juya abinsa bayan ya bulbuleta da hayakin taba. Ajiyar zuciya ta saki bayan ya tafi sai dai kafin ta motsa daga wurin da take taji wasu maza na tahowa wurin da take. Tana jin su suna tattaunawa a tsakaninsu waye zai fara amfani da ita. Abin nasu kamar fada mutum biyu suka dage harda zage-zage. Kafin su karaso da sauri Asmau tabi bayan mutumin da ya gama yi mata magana dama baiyi nisa ba. Tana kankame da jakarta tace ya tsaya zata bishi. Wani shu'umin murmushi yayi yana kare mata kallo. Shiyasa yake son aiki da su Shoki yaran da ya biya suka tsorata ta. Addu'a kawai take yi tabi bayansa suka mike wata hanya da tayi kudu da tashar. ***** Su Umma sun sake taruwa a falon gidanta inda Malam Musa ya bada shawarar a dage da addu'a da binciken mutanen da take da alaka dasu. A cewarsa babu wani abu yanzu mai mahimmanci a gabansu sama da sanin inda Asmau take. Sannan ya ce " a gaskiya dukkanku kunyi kuskure akan yadda ku ka karbi al'amarin yarinyar nan. Dukkan dan Adam ajizi ne, Allah da Ya haliccemu mai gafara ne da jinkai. Idan mutum ya aikata ba daidai ba musamman abu irin nata dolene mu nuna mata kuskurenta sannan kuma mu jata a jiki don gudun sake faruwar makamancinsa. Mu nuna mata mahimmancin tuba da karbar kaddara. Amma idan muka watsar da lamarin 'ya'yanmu saboda sunyi laifi hakika muna tura su ne ga aikata wanda yafi shi. Wani lokacin idan hantara da kyama tayi yawa sai kawai yaro ya fandare gabadaya yace bari yayi ta laifin tunda bashi da sauran gata. Mu kula sosai idan mutum yayi laifi fada, nasiha da jankunne yakamata muyi ba sharesu ba har su bi hanya mara kyau. Allah ma muna masa laifi Ya yafe mana duk girmansa indai ba shirka bane balle mu 'yan Adam. Wani abin yana faruwa ne domin ya zama izina ga sauran mutane. Kuma na tabbatar yadda kuka nemi tilasta ta akan a cire cikin shi ya koreta. Sannan ta fiku gaskiya domin cire ciki ba tare da wata lalura ba bashi da muhalli a addininmu. Allah Ya tsare mana ita a duk inda take." Jikin kowa kuma sai yayi sanyi da jin bayanin Mal Musa suka ce Amin. Haj Bara'atu dai babu abinda ke damunta sai irin yadda ta rinka fadar maganganu marasa dadi ga 'yarta cikin bacin rai. Da ta sani bincikar ta tayi taji yadda al'amarin ya faru domin a kiyaye faruwarsa ga sauran yara. Bacin rai da fushi dole ne amma yin komai cikin hikima da ilimi shine daidai. Da ta sani fada tayi mata wanda ta tabbatar halin da take ciki ma ya isheta abin kunya. Daga nan sai a kiyayi gaba,yanzu kuwa tana iya zuwa inda rayuwarta zata iya gurbacewa gabadaya. ABINDA AKE GUDU🙆🏽8 Batul Mamman💖 Tafiya su Asmau suke yi a inda tafi tunanin kasuwa ce saboda yawan shaguna da ta gani da mutane suna kai kawo kamar ba dare ba. A bakin kofar wani gida suka tsaya mai kofa daya. Sai da suka shiga ta ga ashe gidan yana da girma ta ciki. Dakuna ne birjik ta bangaren hagu , dama da tsakiya. Ga 'yan mata kamar ba dare ba suna ta bidirinsu babu mai shigar arziki. Harda masu daurin kirji. Tun daga nan Asmau ta fara dana sanin biyo mutumin. 'Yan matan taga suna gaisawa da mutumin da ta biyo suna tambayarsa bakuwa ya kawo musu yace eh. Tafiya suka cigaba da yi har sai da suka je kofar wani daki daga gefe. Dan mukulli yasa ya buga kofar dakin wata budurwa ta fito a fusace. Wani mugun kallo ta watsa musu shi da Asmau sannan ta matsa gefe wata babbar mata ta fito. Doguwa ce da gani shekaru sun ja, jikinta kuma yayi jaja-jaja alamun anci bleaching lokacin da ake ji da sauran kuruciya. Ganin su Asmau yasa ta washe baki tana murmushi. " Bulayi kaine a daren nan? Bakuwa ka samo mana ne?" Shima murmushin yayi "a bamu wurin zama mana sai muyi magana a nutse". Yarinyar da take ta hararsa a kofar dakin matar ta kalla ta koma ciki ta dauko musu tabarma aka shimfida a wurin. Sauran 'yan matan gidan kowacce harkar gabanta take yi. Mutumin da ya amsa suna Bulayi yace " ina shirin fita daga tasha nayi gamdakatar. Dubi tsaleliyar da na gano. Ina ganinta nace wannan taki ce don duk garin nan gidanki ne gidan kyawawa." Matar ta maida kallonta ga Asmau " yarinya ina miki barka da zuwa. Ni sunana Uwargida haka kowa yake kirana. Kuma tunda kika zo gidan nan zamu taru mu sharewa juna hawaye. Babu ruwana da abinda ya fito dake bariki indai zaki kiyaye dokar gidana shikenan." Asmau ta mike tsaye domin ta gano wane irin gida aka kawota. Jakarta a hannu tace "Hajiya kiyi hakuri ni ba yawon bariki na fito ba. Bazan iya zaman gidan nan ba. Nagode". Takalminta ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103