Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 44

Chapter 44

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kunya ta dan fari ta sanya taki tuna mata dashi. Kuma tasan yau rana ce mai matukar mahimmanci a wurin Asmau. Ta hadu da iyayenta da 'yan uwa bayan tsahon lokaci. Shema'u ta sanar da Umma. Nan da nan aka samu food flasks aka hada masa duk wani na'uin abinci na gidan sunan. Jafar aka kira akan su wuce gidansa domin bako ya samu yaci abinci ya huta. Jafar da Sabira suka fito dauke da kayan abincin tare da Asmau dake binsu a baya rike da hannun Amatullah. Zaune yake a gaba ya kwantar da kansa a saman kujera yana sauraron karatun Al'Qur'ani kira'ar Shiek Mishary Rashid. Tausayinsa Asmau taji saboda kunyar abinda tayi masa. Babban mutum kamarsa sun shanya shi a kofar gida. Kuma ta tabbatar baici abinci ba kafin su taho. Yana dawowa daga masallaci ko zama baiyi ba yace su taho kawai. Amatullah ta tafi da gudu ta fada jikinsa. Hakan yasa shi saurin bude ido yana murmushi. Jafar ya karasa gaban motar ya mika masa hannu suka gaisa. "Kayi hakuri don Allah an barka a waje tun dazu. Duk laifin Idon kuka ne da bata fada mana tare kuke ba" Col. Ishaq yace "Idon kuka kuma?" Dariya Jafar yayi kana ganinsa kasan yana cikin farinciki, ya nuna Asmau "ai sunanta kenan." Kyakkyawan murmushi Col. Ishaq yayi yana kada kai "sunan ya dace da ita" Duk akayi dariya sannan Jafar ya fada masa yana son ya biyo shi gidansa domin yaci abinci. Da farko Ishaq ya nuna baya jin yunwa sai da Asmau ta bashi hakuri tare da rokonsa. Yayi yar dariya "Haba Idon kuka, bayan ko introducing dina a wurin yayanki baki ba?" Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Jafar ya sake mika masa hannu murmushinsa yana kara fadada "nima da laifina, sunana Jafar ni Asmau take bi,wannan matata ce Sabira. Idan kaci abinci zamu shiga ciki ka gaisa da duk 'yan uwa." Col. Ishaq ya dafa kan Amatullah "ni kuma sunana Baban Safina" Sabira ta kalli Asmau "kice kawai biki zamu sha kwanan nan" Da sauri Asmau ta daga hannuwa "ba haka bane, Ama ce kawai take kiransa babanta. Sunansa...." Shiru tayi duk suka zuba mata ido. Kunya taji ta kasa fadin sunan sai ta wayance tace ya kamata su tafi saboda kada abincin ya huce. Col. Ishaq ya nuna su shiga motarsa. Jafar ya shiga gaba, Sabira na baya sai Amatullah da ta dage zata bi babanta. Asmau tana tsaye suka ja mota suka tafi ta koma ciki. Hira aka dora daga inda aka tsaya. Shema'u tana goye da Abid din Sabira sai jijjiga shi take kafin Sabirar ta dawo. ***** Mata kamar kara turo su akeyi gidan ana ta zuwa kallon Asmau. Hajjo duk ta matsu su firfita don su samu ayi hira yadda ya kamata da Asmau. Duk dakin da ta shiga mata ne harda wadanda ma basu zo ba da farko. Su Umma ma dai kara kawai suke yi amma duk a matse suke da a basu fili suyi hira da 'yarsu. Da suka ga abu yaki karewa Hajjo da kanta ta shiga falo rai a bace tana mita yadda masu hankali zasu fahimta "Kai jama'a ace anzo taron suna anci tatsotse dinnan anci salak, anci tuwo anci wannan anci wancan amma mata sai tururuwa suke yi. Fisabilillahi ko irin karar nan ta a fita a bamu waje da jikarmu muyi hirar yaushe gamo ya gagara". Wasu nan suka fara jin kunya suka fara hada kayansu suna fita. Sauran da suka yi biris kuwa Hajjo ta rufe idonta ta sallamesu. Umma da Mama dai sunji kunya to amma halinmu na mata wurin saka ido da bin kwaf ya janyo musu. Basu samu gidan yayi daidai ba sai bayan karfe tara. A falo suka zazzauna. Duk 'yan uwan Asmau makusanta suna wurin har da Kawu Garzali ga kuma Haj Lubabatu da danta. A nan aka shiga bada labarin abubuwan da suka gabata. Kowa jikinsa yayi sanyi musamman da suka ga Asmau tana ta kuka da rokon a yafe mata. Suka yi ta kukan wannan kaddara da ta riga fata. Mama Yalwa tace "ai wannan bala'i na waya sai an dage da addua sosai. Akwai alkhairi tattare da ita amma sharrinta a bayyane yake. Kuma kullum kara samar da sabuwa akeyi mai saurin hada mutane da barna." "Haka ne" Haj Lubabatu ta amsa mata. " Sai kiga yara kanana sun yini da waya a hannu ki rasa me suke tattaunawa. Wani lokacin a haka ake haduwa da mutane babu sanayya idan kika yi rashin sa'a ba nagari bane sai su bata maka tarbiya ba tare da ka lura ba. Kwanakin baya jikata dake karatu a nan wurina Bilkisu na fuskanci ta soma nacewa waya fiye da yadda ta saba. Kullum suna hira da wata yarinya da suka hadu a irin group dinnan na waya. Kunsan yanzu tsakanin mace da mace ko maza ma babu abinda ba'ayi. Na kula kawancen ya soma yawa bata da zance sai nata. Abun ya fara bani tsoro. Shabiyun dare sai kiji suna waya sai da nayi mata tas akan hakan." Hajjo tace "ni idan babu hali ba sai a hakura da wayar ba. An fara abu da gaisuwa da sada zumunci a hankali waya ta zama tamkar kana dauke da duniya a tafin hannu. Idan kaki bawa danka waya ma zai fita ya gani a ta wasu." Tattaunawa suka yi ta yi a game da tasirin waya ga al'umma yanzu. Babu babba babu yaro kowa yana da ita kuma ya iya amfani da ita. Jankunne sosai manyan suka yi garesu akan su dubi yadda rayuwar Asmau ta kasance su kula da kawunansu da na yaransu. Kasancewarsu masu aure duk bashi bane domin yanzu hatta mata da mazan aure suna fadawa tarkon waya. Daga group sai kaga matar aure tana mu'amala da 'yar uwarta mace ko namiji mai aure ko mara shi wanda a da ba halinta bane. Sun jima suna hira har shadayan dare tayi basu kula ba sannan Haj Lubabatu da Col. Ishaq suka tashi tafiya. Sun sha godiya a wajen dangin Asmau sosai tare da neman a cigaba da zumunci don yanzu sun zama daya. Fitowa suka yi har bakin mota rakiya Amatullah na makale jikin Col. Ishaq tana bacci. Tashin da yayi zasu fito yasa ta farka ta soma rigimar binsa. Shi kan shi baya son rabuwa da ita. Ana ta lallabata taki yin shiru sai da Asmau ta karbeta ta karfi tana mata fada. Hakura tayi amma bata dena kukan ba. Col. Ishaq ya bata rai sosai saboda fadan da tayiwa Amatullah. Kallon da yake mata ya nuna rashin jindadinsa sai kawai ta sunkuyar da kanta. Bayan tafiyarsu Umar ya tafi kai Mama Yalwa gida shi kuma Abdulhalim ya dauki matarsa da yara suka wuce. Dakin Umma suka koma Amatullah tana ta kuka har sai da Asmau ta goyata duk girmanta don taki yarda da kowa. Daga nan aka soma wata sabuwar hirar har aka zo kan Kawu Rabe Asmau tace shi kadai ne bata gani ba . Shema'u tace "hmmm Asmau mutum babu kyau. Ashe duk tsahon lokacin nan Kawu Rabe wurin wani malami yake zuwa ana rufe bakin Hajjo da su Yaya Abu. Bayan tafiyarki Hajjo tazo ta nemi gafarar Umma

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});