Chapter 70
Chapter 70
ina da shaidar da duk wanda ya kalleta bazai manta da cewa Asmau ta taba bayar da jikinta ga mutumin da babu aure a tsakaninsu ba. Ni abar gudu ce da kyama a cikin mutanenmu. Bani da sauran daraja da kima a idon jama'a sai dai kawai ayi min kara. Da wannan ciwon nake kwana nake tashi kuma dashi zan koma ga Mahaliccina. Idan aka kallemu sai an sake. Ga wadda tayi cikin shege nan. Amma duk da wannan nakasar ta rayuwata kake sona saboda Allah. Ka rike 'yar da bata da uba na aure a matsayin taka. Ka nuna min ina da sauran darajar da zaka iya zama dani. Shine yanzu zaka ce zaka barni saboda rashin haihuwa.?" Sai da yayi tunanin haka zata iya faruwa. Ba yanzu yake jiye musu ba. Kada ayi aure hakurinta ya kare musamman da yake tana da kuruciya. "Matar Jikamshi, haihuwa ba abin wasa bace nakasa ce mai girma. rashinta ya kashe aure da yawa. Ya bata soyayyar shekaru da dama. Ya hana zaman lafiya tsakanin kishoyoyi" Innalillahi wa inna ilahi rajiun take karantawa tun da ya fadi maganar don ta sami kwarin gwiwar magana. Kada tayi kuka ya tursasa mata amincewa da bukatarsa. "Sayar da jiki a waje ko haihuwa babu aure shine babbar nakasa a rayuwar musulmi. Amma rashin haihuwa ta sunna ba nakasa bace. Jarabawa ce daga Allah Madaukakin sarki. Shi kadai Yasan ladan da Ya tanadarwa masu hakuri da rashi. Ita fa aba ce da duk kudin duniya bazai siyeta ba kuma marasa ita su kadai suka san halin da zukatansu ke ciki sai Allah. Amma mutuncina da ba fin karfi akayi min ba wurin rabani dashi kaga bani da uzuri. Taka jarabawar kenan, hakuri da ita sai yasa Allah Ya yafe maka dukkan zubunanka Ya baka aljannah. Ni kuwa fa? Ni na jawowa kaina. Bani da masaniya Allah Ya yafe min ko kuwa...." Sai yanzu ta soma kuka mai cin rai. Wayyo Allah son zuciya. Babu wanda yayi musu dole ita da Abubakar suka biyewa shaidan. A rayuwa bazata taba manta groups da ake hira ko litattafan da ake rubutawa ba masu sanya mace budurwa taji bukatar namiji, mai aure idan mijinta na nesa taji ta kasa hakuri. Duk su biyun idan shaidan na kusa ga kaddara sai su fada ga halaka. 'Yan mata nawa ne a sanadiyar karamce karance irin wannan suke burin samarinsu su dan taba wani bangare na jikinsu ko don su rage musu shaawa? Da yawansu sun koshi da tarbiya kuma suna kokarin kamewa. Rana daya tsautsayi zai sa suci karo da irin wadannan masu yada alfashar shikenan komai nasu sai ya lalace. Col. Ishaq ji yake kamar ya tayata kuka. Tausayi tare da son Asmau ke karuwa a zuciyarsa. Bude baki yayi zaiyi mata magana ta riga shi "Jikamshina idan kaki aurena saboda rashin haihuwarka ka cutar dani kuma ka raina son da nake maka. Idan so kake ka rabu dani saboda Allah zanyi hakuri. Amma idan wannan ne dalilinka to ka sani *wallahi* bazan taba rabuwa da kai ba. Har zaka iya son auren mace irina sai nice kake tunanin zan gujeka" Dafe kansa yayi saboda ta daure shi da zantukanta. Ya kara yarda Asmau mace ce tagari wadda kaddara ta gifta mata. Yana jin kukanta har ransa. Saukowa yayi daga kan kujerar da yake ya zauna a kasa dan nesa kadan da ita. "Look at me please" Babu musu ta dago kanta. Wannan idan su Umma suka ganta sai a zata wani mugun abin yayi mata ai. "Har mamaki nake yadda kika shiga zuciyata Matar Jikamshi. Ban taba jin zafin so da tsoron rabuwa kamar akanki ba. Ina tsoron muyi aure ki kasa hakuri da lalura ta. Kada son da muke wa juna ya koma zaman hakuri kawai a nan gaba. Kada kiga kamar saboda abinda ya wuce a baya dolenki ki zauna dani duk yadda nake. Kiyi tunani sosai, bani da niyar cutar dake." Idonta cikin nasa abinda bata yi ko bisa kuskure suka hada ido tana saurin dauke nata. "Gobe Baba yace yana son ganina kuma nasan so yake yaji wa na zaba cikinku. In sha Allah sunanka zan fada masa. Idan kaki amincewa zan hakura nasan Allah bai kaddari aurenmu ba. Amma bazanyi aure ba har abada. Bazan yarda na kara son wani ba balle na kara haduwa da irin ciwon da nake ji a zuciyata yanzu." Tana gama magana ta tashi tayi hanyar da yasan zata kaita cikin gidan sosai. Kasa motsin kirki yayi sai daga baya ya tashi duk jikinsa babu kwari. Wannan ciwon kan ne ya sake dawo masa ya tashi jiri na dibarsa. Yana son Asmau amma yana tsoron kada Allah Ya kamashi da tauye mata hakki. Da kyar ya iya zuwa bakin motarsa. Duhu duhun da yake gani yasa ya dauko wayarsa ya kira Yassar. Bai dade ba ya fito ya tsorata da halin da yaga Col. Ishaq. Mukullin motar ya bashi yace don Allah Ya kaishi asibiti daga nan ya ajiye shi a gida amma kada ya fadawa su Umma balle Asmau. A rude Yassar yaje yace da Umma zai raka Col. Ishaq unguwa tace to sai sun dawo. Asmau kuwa daki ta wuce ta fada kan gado tana kuka. Bata da abinda zata sakawa Jikamshi dashi sai aure da yi masa tsantsar biyayya. Zata aure shi ta nuna masa haihuwa ba ita kadai bace aure. Ita dai tana karawa maaurata jindadi ne. Amma idan Allah Ya hanaka to bai hanaka saurin jindadin rayuwa ba. Bai hanaka lafiya da arzikin ibada ba. Ko yanzu kukanta na tsoron kada yaki amincewa ne. Da Umma taji shiru bata fito ba tace karshenta tana can tana kuka Ishaq ya gaya mata ya fasa. ***** Da Yassar ya kaishi gida yaso tambayarsa abinda ya faru amma ya kasa saboda yanayin da yake ciki. Sunyi sallama ya bashi kudin mota yaki karba ya tafi gida da wasiwasi. ***** Washegari Asmau tayi wanka da wuri tana jiran zuwan Shemau da Jafar. Tun bayan asuba ta tura musu text tana rokon su zo kafin taje gidan Baba. Umma dai addua take yi mata a zuci da fatan Allah Ya kawo mafita cikin sauki. Tayi mamakin ganinsu Shemau suka ce Asmau ce ta neme su. Suma hankalinsu ya tashi. Hajjo na bacci lokacin suka shiga dakin Umma bayan ta hada Amatullah da kayan wasa don kada ta dame su. Duk yadda sukayi da Col Ishaq ta fada musu. Babu wanda yayi mamaki domin kuwa duk sunji komai a wurin Umma. Maganarta ta karshe ce ta dauki hankalinsu da tace shi zata cewa Baba ta amince ta aura. Shemau tace "Asmau baki da hankali ne. Rashin haihuwa da kuruciyarki ba abu bane da ya kamata ki bari soyayya ta rufe miki ido a kai." "Yaya Shemau ki tuna shi fa da 'yata ya ganni kuma yace yaji ya gani. A irin rayuwata ko 'ya'ya yazo dasu yanzu ai dole na hakura na aureshi tunda nima ina da ita. Duk yarinyar da ta tafka kuskure irin nawa wallahi zabinta ya zama ragagge a rayuwa. Dole idan tana son jindadi ta hakura da wasu abubuwan. Sharrin zina kenan. Yanzu ko auren mai duka nayi indai ina son rufawa kaina asiri dole na hakura
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103