Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 58

Chapter 58

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

asiri, wayyo Allah" Gabadaya ta manta da inhaler din da aka basu a asibiti ta dauketa sai dakin Hajjo. Kuka take yi sosai tun kafin ta shiga su Umma suka fara fitowa saboda muryarta da suke ji. Ganin Amatullah na numfashi da kyar Shemau ta karbeta Sabira kuma ta kira Jafar a waya. Lokacin Umma har ta dauko mukullin tata motar. Yassar baya gidan shi tun safe ya fice. Sabira na fadawa Jafar ya tashi da sauri. Lokacin an gama gaisawa da dangin Qasim kenan. Abdulhalim ya tambayeshi abinda ya faru ya fada musu. Kowa sai salati suka tashi don ta nan su Umma zasu wuce. Kafin kace meye wannan suna mota Asmau ta cire dankwali sai hijabinta kawai tana yiwa Amatullah fifita. A can gidansu kuma Alh Adamu ya gama gigicewa. Yana matukar son jikarsa shiyasa hankalinsa ya tashi. Karshe yace don Allah suyi hakuri zai bisu asibitin. Idan komai ya lafa sai su karasa abinda ya tara su. Duk da wasu basu ji dadi ba to amma lafiya tafi komai. Haka suma aka samu wasu cikinsu suka bi bayansu aka tafi asibiti. Ainau ce ta kira Yassar ta fada masa. Kafin ya karasa asibitin ya kira Col. Ishaq ya sanar dashi da kuma sunan asibitin. Shima hankalinsa a tashe ya tafi. Dama yayi ta kiran wayar Asmau yau baya samu. Niyarsa bayan magariba yaje gidan. ***** Emergency suka kaita nan da nan likitoci suka fara aikinsu. Sun tabbatar musu ba abin damuwa bane asthma dinta ce ta tashi amma abin baiyi tsanani ba. Ana ta rarrashin Asmau ta kasa shiru. Dama can hankalinta ba a kwance yake ba. Suna nan aka canza mata daki lokacin numfashin ta daidaita ta sami bacci. Qasim ya shigo dakin aka gaisa ya duba Amatullah ya fita. Bai dade da fita ba Jafar yace taje waje Qasim na kiranta. Bata son nunawa mutane rashin son auren shiyasa ta fita ta same shi. Kokarin kwantar mata da hankali yayi tace ta gode. Suna nan tsaye Col. Ishaq ya iso. Tunda idonsa ya gano masa Asmau da Qasim yaji wani bacin rai sai dai jikin Amatullah ne a gabansa. Daya karaso suka gaisa da Qasim. Itama ta gaisheshi sai ya shareta kawai. Tana kallo Yassar ya fito ya kaishi dakin ya duba Amatullah. Kasa nutsuwa yayi ya fito ya dawo inda suke. Gaban Asmau sai faduwa yake yi. Yana zuwa yace "Naga dakin a ciki da mutane da yawa. Tun yaushe ta fara ciwon ban sani ba?" Qasim ne ya bashi amsa "ko awa daya ba'ayi ba. Mutanen ciki 'yan uwana ne dana Asmau. Kayi hakuri naso sanar da kai ma abin ne yazo a kurarren lokaci." Idon Col. Ishaq akan Asmau yace "wane abu kenan?" Da dan murmushi Qasim yace "kawo kudi aka zo sai ciwon Amatullah ya tashi" Guntuwar fara'ar fuskar Col. Ishaq tuni ta bace "kudin aure??? Na wa?" Kirjin Asmau sai bugu yake da karfi don tsoro. Gashi yq tsareta da ido. Qasim yace "kin barni ina ta magana ni kadai ko, wallahi daga fadawa iyayena kawai sai suka yanke shawarar gara ayi komai lokaci guda. kudin *aurenmu* aka zo kawowa." Sabanin bacin ran da tayi tunanin gani a fuskar Jikamshi sai taga yayi dan murmushi "Kasan mata da kawaici da kunya. Musamman ma dai _Matar Jikamshi_. Asma'una baki fada masa muna soyayya bane?" Qasim ne yaji kamar an sauke masa guduma a kansa. Sai ya kalli Asmau da tayi mutuwar tsaye sannan ya kalli Col. Ishaq wanda yake binta da kallo mai nuni da tsantsar soyayya kamar ya sanyata a jikinsa. Daga bayansu Yassar ne yazo kiran Asmau ya fada mata Amatullah ta farka. Jin abinda Col. Ishaq ya fada yasa shi daka tsalle ba shiri. ABINDA AKE GUDU🙆🏽43 Batul Mamman💖 Shiru suka yi gaba dayansu sai Col. Ishaq da yake murmushi kamar bai san abinda yayi ba. Shi kuwa Qasim nema yake maganar da yaji ta gama shiga kwakwalwarsa. Ihun tsallen Yassar ne yasa duk suka kallo inda yake. Baiyi wani dogon tunani ba don kada a gano shi ya durkusa kasa tare da rike kafarsa ta hagu "Wayyo Allah wani abu ne ya cije ni" Asmau tayi kansa da sauri dama neman hanyar da zata bar wurin take yi don ji take kamar idan ta kara minti daya itama sai dai a bata gado kusa da Amatullah saboda irin bugun da zuciyarta take yi. "Mu gani a ina ne?" Ya dago kansa yana kallonta, duk sai ta bashi tausayi. Karyar kafar ma saboda ita yayi "Barshi kawai bari na cire takalmin. Kije Amatullah ta tashi tana kuka" Kamar an harba walkiya haka ta bar wurin ko waigowa baya bata yi ba. Qasim da Col Ishaq suka dawo kusa dashi suna tambayarsa abinda ya sami kafar. "Ji nayi kamar abu ya cije ni. Ku shiga ciki Amatullah ta tashi." Qasim ya dawo hayyacinsa daga abinda Col. Ishaq ya fada har ya yiwa Yassar sannu harda kokarin cire masa takalmin zai taya shi duba kafar. Yassar yayi saurin jan kafar yana mai jin kunyar karyar da yayi "ya dena ciwon, zan karasa motar Umma ina da silifas a ciki ina jin cinnaka ne ya shiga." Daga haka ya samu Qasim ya shige. Kafin ya mike tsaye yaji an kama wuyan rigarsa an tayar dashi. Ba don yasan wanda ya rike shi ba sai yayi ihun gaske. Col. Ishaq yayi 'yar dariya yana kallonsa "ka kyauta da ka taimakawa yayarka don sauran kadan ta suma a wurin nan. Har na fara tunanin me zan fadawa su Umma" Shima Yassar dariyar yayi yana murza wuyansa "haka kawai kun sata a tsakiya. Ga soja ga dan sanda da wanne zata ji" "Laifinta ne da tasa duk muka kamu da sonta. Allah Yasa kada ta kwaso mana lauya ko alkali kuma." Murmushi Yassar yayi tare da jin kunyar amsar da aka bashi. Shi dai komai na Col. Ishaq yana burge shi. Ina ma ace shi zai aureta. Ba kuma don baya son Qasim ba sai dai wannan maganar aure ce. ***** Asmau na shiga dakin Amatullah ta dena kuka. Kan gadon taje ta zauna tana yi mata fadan dalilin kukan don bata ganta ba kamar bata san sauran mutanen wurin ba. Mama tace "kiyi mata a hankali Asmau. Yarinyar nan taji jiki. Haka muka sha fama da Abubakar da yana yaro. Idan ta kara wayo zata san yadda zatayi ta rinka kiyayewa sai kiga attacks din basa zuwa sosai." 'Yan uwan Qasim suka ce zasu tafi sai dai su dawo wani satin. Alh Adamu yayi ta basu hakuri yace tunda Amatullah taji sauki suna iya komawa a karasa. Hakan ya razana Asmau sosai ta shiga rarraba idanu taji me Jikamshi zai ce. Sai tayi sa'a yayi kamar baya jinsu. Su din ma sun nuna babu damuwa tunda yamma tayi zasu sake saka rana. Ita dai Asmau ko kallon Qasim din ta kasa. To da wane idon zata kalle shi bayan abinda Jikamshi ya fada masa. Shi a rayuwarsa ta kula baya jin shakkar fadin magana ko a gaban waye indai yana tunanin akan gaskiyarsa ne. Gashi yau ya fadi maganar da tasan dole Qasim ya kullaceta a ransa. Shima a nasa bangaren gani yayi gara ya kyaleta saboda asibiti ba muhallin maganar bane. Sannan

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});