Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 31

Chapter 31

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

barandar da zata kaita bakin gate ne taji muryar mai sharar nan tace "ba dai guduwa zakiyi ba". ***** Hajjo ce ta farka daga bacci a gigice ta rinka juyi akan gado har ta tabbatar dai a dakinta take. Hawaye ne kwance a fuskarta sakamakon mafarkin da tayi da jikarta Asmau. Kuka ta ganta tana yi tana kiran Hajjon da ta taimaketa. Duk yadda taso ta kama hannun Asmau ya gagara har ta farka. Jikinta sai karkarwa yake ta tashi ta dauko mayafinta a gefen kujerar dakin ta tafi dakin Garzali. Ko agogo bata duba ba tayi sa'a ta same shi yana fesa turare da alama fita zaiyi. Tsayuwar kirki ta kasa cikin tsawa tace yazo ya kama karnukansa zata fita. "Hajjo ina zaki je da yamman nan. Biyar da rabi fa". Harararsa tayi fuska a murtuke don kada ya kawo mata wargi "inda ka aike ni zani. Kaga kada ka bata min lokaci wuce muje". Suna fitowa yayiwa karnukan fito suka yo kansa Hajjo ta samu ta fice. Don sauri kafarta har zafi take yi mata taji takun mutum kamar ana binta da gudu. Duk da a tsorace take haka ta dake bata juya ba take magana "Rabe wallahi yau ko me zaka ce sai naje wurin Bara'atu. Ba kai ka haifa min Shu'aibu ba shiyasa baka san ciwon iyalinsa ba." Garzali yayi yar dariya "Ni ne Hajjo. Raka ki zanyi. Nima rashin mu'amala dasu ba karamin damuna yake yi ba." Tayi murmushi "Allah Yayi maka albarka" daga nan ta bashi labarin mafarkin Asmau da tayi suna tafiya. ***** Tun kafin azahar Zubaida ta iso garin Kano ta samu mai tasi suna ta yawo a unguwar Hotoro basu gane gidan ba. Gajiya yayi ya sauketa bayan ya karbi dubu biyu a hannunta. Har zai tafi sai ya dawo saboda ta bashi tausayi yace ta sami mai adaidaita sahu sunfi sanin layukan cikin unguwa. Tayi sa'a kuwa ta sami wani ta fada masa inda take nema. Da ya kula bakuwa ce a garin ya tsula mata kudi sai dai bata damu ba. Biyan bukata yafi dogon buri. Kusan dubu talatin ta dauko a cikin kudin da Uwargida ta bawa Yaya Babba. A cikin layin mai adaidaita sahun ya nuna mata gidan kwamishina. Tayi masa godiya ta bashi kudinsa. Daga nan tasan Asmau tace gidansu babu nisa. Wata tsohuwa ta hango da wani mutum a bakin gate din wani gida tayi saurin karasawa kafin su shiga. Sallama ta rinka yi musu suka juya suna kallonta a tare. Riga da siket ne a jikinta sun dameta sosai ga katuwar jakar kaya sai wani siririn mayafi da ta rataya a wuya. Da murmushi a fuskarta ta dan rissina ta gaishesu sannan tace "don Allah gidan Umma nake nema. Umman Asmau". Garzali ya sake kallon Zubaida sannan yace "nan ne". Ko jiransu batayi ba ta shige ciki tana kwalawa Asmau kira. Yassar da yake shanya ne ya fara ganinta bai san lokacin da ya saki wandon da yake kokarin dorawa a igiya a kasa ba ya nufota. Zubaida na ganinsa ta saki murmushi. "Tabbas nan ne gidan don naga kamarku. Kai ne Yasir ko?" Kallon rashin sani yake mata yace "a'a sunana Yassar" Zubaida tace "hakane kaini wurin Asmau". Hanyar falon ya nuna mata sai ya kula da Hajjo da Kawu Garzali. Har dan tsorata yayi sai yaga Hajjo tana hawaye "Zo nan Yassar, zo naji duminka a jikina" Ji yayi kamar mafarki yake ya fara tunanin gudu Garzali ya damko wuyan rigarsa ya hada shi da jikin Hajjo. Kuka ta fashe dashi na takaicin yadda jikanta yake nuna tsoro da fargabar ganinta har yana neman gudu. Tana rike da hannuwansa tace "kuyi hakuri Yassar. Ku yafewa wannan tsohuwar". Shima kukan ne ya zo masa ya kankameta. Ashe akwai ranar da Hajjo zata nuna masa so? Tana rike da hannunsa suka shiga cikin falon. Umma suka gani da Aina'u da kuma Jafar sun saka Zubaida a gaba suna kallonta jin tace daga Azare tazo wurin Asmau. ABINDA AKE GUDU🙆🏽25 Batul Mamman💖 Cikin matsanancin tsoro Asmau ta juyo tana kallon matar. Hakuri ta soma bata murya na rawa ga hawaye na wanke mata fuska tana sanar da ita bata da kudi kuma bata kowa da zai taimaketa. Matar sai tayi murmushi "kada ki damu ni ba wani abu zanyi miki bane. Hasali ma na rasa dalilin da yasa tun da na shigo dake cikin asibitin nan hankalina yake kanki. Amma dai biyoni mu koma ciki". Ba yadda ta iya haka tabi bayan matar suka tafi wurin wata mai sharar. Matar babba ce don da gani zatayi sa'a da Umma. Wadda ta biyo ta gaisheta cikin ladabi sannan ta gabatar da Asmau a matsayin 'yar uwarta wadda bata da komai. Rokonta tayi akan ta ranta mata kudi su biya a sallameta ita kuma tayi alkawarin biyanta a hankali cikin albashinta. Babbar matar ta kalli Asmau tayi wuri wuri da ita tana jijjiga goyonta. Da gani ma a tsorace take tace "kudin ba wasu masu yawa bane Zulaiha, ga wannan kije ki biya. Sai mu warware daga baya. Ki gaida mutan gidan." Zulaiha tayi mata godiya itama Asmau ta saka baki suka yi tare. Bayan sun fito ne Asmau ta rasa bakin godewa wannan matar mai suna Zulaiha. Matar bazata girmeta da yawa ba. Tuna mata take da Anti Rashidan Azare. Bayanta tabi suka koma wurin likita aka sallameta duk da yaso kwarai ta kai washegari. Zulaiha tace "babu komai yiwa kai ne. Bari na canza kaya nazo muje gidana tunda dare yayi". Asmau sai mamaki take yi meyasa wannan matar ta taimaketa alhali bata san komai a game da ita ba. Suna fita daga asibitin bus suka hau maleji suka sauka a wata unguwa da Asmau bata sani ba. Daga nan suka bi cikin lunguna suka karasa wani gida mai karamin gate. Idan kaga gidan dole zakayi tunani masu shi suna da rufin asiri. Sai ka shiga zaka ga babu wasu abubuwan more rayuwa. Yara ne har shida suka fito suna yi mata sannu da zuwa ta amsa fuska a sake sannan suka gaishe da Asmau. Zulaiha ta dauki karamin ciki da baifi shekara ba ta soma shayar dashi. Falon da ta kai Asmau ko leda babu ta dauko tabarma ta shimfida mata. Yaran ta tambaya ko su kadai ne a gidan suka ce eh. Babbar cikinsu mace ce da bata fi shekara tara ba sai namiji dake binta. Duk yaran babu wata tazara tsakaninsu. Ta dauko naira hamsin daga gefen zaninta ta bawa namijin "Muhsin siyo mana kan kifi, ke kuma Humaira dauko attaruhu hudu da rabin albasar nan ta safe ki jajjaga min. Sannan ki dauko katuwar tukunyar nan ki wanke a cikata da ruwa yanzu zan zo na dora" Da murna yaran suka fita tunda suka ji batun kan kifi sun san yau gidan za'a ci dadi. Asmau na nan zaune Zulaiha ta kunna kyandir sannan ta tashi ta dora mata ruwan wanka ita da baby ta kuma dora girki. Wankan Zulaiha ta fara yiwa jaririyar itama Asmau tayi da taimakonta dai. A ranta sai mamakin matar take yi. Haka kawai daga haduwa sai taimako? Bayan tayi wankan taji dadin jikinta tana zaune Zulaiha ta sakawa jaririyar kayan karamin danta Ali irin wanda

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});