Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kaunar Asmau a ransa. Tunani yake har me ta gani a tattare da Col. Ishaq take sonsa haka. Yasan mutumin dai ya hadu amma ko babu komai shi Qasim ya fishi kuruciya. Duk da bai san komai game da Col. Ishaq ba amma yana da tabbacin da wuya idan bashi da mata daya ko sama da haka. Shi da yake da burin bata dukkan kulawa ta yadda babu wata mace mai suna kishiya da zata takura mata shine zata kai kanta cikin mutanen da basu dade da sanin juna ba. Yanzu idan ta aure shi danginsa suka wulakanta ta fa? Hawaye yaji yana neman zubo masa. Duk laifinsa ne da ya zama mugun aboki ga Abubakar. Ba don shawarar da ya bashi ba ai da haka bata faru ba. Ko Abubakar ya rasu ya tabbatar duk inda tayi aure zata tsira da mutunci da martabarta. Sai kuma tausayinsu da yaji. Asmau tayi masa halacci da har bata kalli tsabar idonsa ta nuna masa bata son shi ba. Yayi dan murmushi, dole yasan yadda zaiyi ya janyo ra'ayinta gareshi tare da nuna mata illolin da auren wanda basu gama sani ba zai iya jawo mata. Idan kuma hakan bai samu ba......kasa karasa tunanin yayi. ***** Col. Ishaq yana zuwa gida ya kira Asmau. Jin wayar a kashe yayi dan murmushi. Ya fuskanci tana cikin matan da basa bawa waya mahimmanci. Yau ta kashe gobe tace wayar tana daki ne. Sai da yayi wanka yaci abinci sannan ya tafi dakin Hajiya. A zaune ya sameta a kasa Bilkisu tana matsa mata kafafu. Ya zauna a gefenta ta dan janye jiki ita a dole ga dan fari. Dariya Bilkisu tayi ya rankwasheta a ka don yasan tsokanar Hajiya take yi, sannan ya fuskanci Hajiyar. "ciwon kafar ne ya tashi,akwai maganin ko ya kare? "Na sha ma bayan naci abinci dazu. Yau ina ka tsaya daga cewa zaka ganin abokinka" "Asthma din Safina ce ta tashi suna asibiti an kwantar dasu." Cikin tausayawa Haj Lubabatu tace "Allah sarki, ciwon yaro babu dadi bare ciwo irin wannan. Da ka fada mana tun dazu ai sai Sabo ya kawo mu kafin ya tafi gida. Ya kamata su hada mata da maganin gargajiya, zan tambayi Kawunku suna masana a bangaren. Kasan ciwon yana bukatar kulawa" Yaji dadin yadda mahaifiyarsa ke nuna damuwarta akan abinda yake so duk da bata son fada. Bilkisu yasa ta tashi hado masa abinci ya samu ya sanar da Hajiyan duk abinda ya faru a yau bayan zuwansa asibiti. Haj Lubabatu ta kalle shi cikin damuwa "Yanzu kai bazaka hakura da ita ba tunda iyayenta sun fi son wancan yaron?" "Hajiya itama bata son sa. Kuma don ban gabatar da nawa magabanta bane da wuri. Kin sanar da su Kawun kuwa?" Ta girgiza kai tana mamakin wannan soyayya da danta yake yiwa Asmau. "Na fada musu don Yaya Auwalu ma yace zai kiraka kuyi maganar. Ni dai bana so azo a sami matsala daga iyayenta gara kawai tunda har an fara batun kawo kudi ka janye." Dan murmushi kawai yayi "Hajiya idan kina kyamar aurena da Asmau ki fada min. Nasan hakan zai iya zuwa ranki saboda irin yanayin data tsinci kanta a baya. Kin sani duk yadda nake son abu bazanyi batare da izini da neman albarka daga gareki ba" Akwai shi da iya tsara zance da ladabi shiyasa take sonsa. "Ko kadan bana kyamar aurenku. Kuma ni wacece da zanki karbar kaddara. Ka sani babu wata uwa a duniyar nan musulma da zata ji farat daya hankalinta ya kwanta idan danta ya nemi auren macen da ta taba haihuwa a wajen aure. To amma kowa da abinda Allah Ya tsara masa. Yarinyar nan kana ganinta kasan ta fito daga gidan tarbiya sai gashi tsautsayi ya fada mata ta tsinci kanta a irin wannan yanayin. Bazan ki ta ba don da Allah Yaso da daya daga cikin nawa 'ya'yan za'a buga misali. Idan Asmau matarka ce fatana Allah Ya baku zaman lafiya da hakuri da juna" A take fargabarsa na kin amincewarta ta gushe daga zuciyarsa. "Nagode Hajiya Allah Ya kara lafiya. In sha Allah zan nemi Kawu Auwalun idan ya bukaci naje Jikamshin sai naje. Ina so su zo da wuri ne." Yanaa tashi Bilkisu ta shigo da abincin ta ajiye a gabansa tana murmushi "Uncle albishirinka" "Goro maigadon zinare" Ta danyi tsalle kamar karamar yarinya "gobe Mami zata zo" Dena zuba lemon da yake yi yayi yace "da gaske" fuskarsa na nuna farincikinsa. Hajiya tace "to sarkin surutu. Ke da tace kada ki fada masa sai da ya ganta kika fasa kwan saboda kina murna mamanki zata zo ko?" Bilkisu ta turo baki "kai Hajiya nifa ba haka nake nufi ba" Col. Ishaq yace "Hajiyar tawa kike turawa baki. To na mayar da goron albishir din banji abinda kika fada ba" Tashi tayi ta bar dakin tana buga kafa yana mata dariya. Ya juya ga Hajiya cikin murna "gara tazo taga yayarta kuma kanwarta" Mami ita ce 'yar Haj Lubabatu ta biyu. Shekara daya da rabi Col. Ishaq ya bata. Ba karamin shakuwa suka yi ba kamar ba sako da sako ba. Komai nasu tare suke yi. Hatta zancen Asmau ya fada mata ya sami wadda yake so amma sai tazo Kano ko shi yaje Jos din zasuyi maganar sosai. Ita kanta murna da doki ya isheta saboda ta matsu yayi aure. Tun bayan rabuwarsu da Badariyya bata kara jin yayi zancen mace ba sai yanzu. ****** Washegari litinin su Asmau sun kwana a asibiti. Da sassafe Umar yazo ya kai Mama gida ta yi wanka sai ya taho da Ainau ta taya Asmau zama. Ko goma bata yi ba suka ji sallamar Col. Ishaq. Asmau na jin muryarsa taji wani irin dadi a ranta. Soyayyarta da Jikamshi kullum jinta take sabuwa. Cikin khakinsa yake na sojoji yayi kyau ta bishi da ido a lokacin da yake shafa kan Amatullah dake kwance tana bacci. Ya amsa gaisuwar Ainau sannan ya juya yana kallon Asmau. Saurin sunkuyar da kai tayi tana jin kunyara tan cigaba da yiwa Husna dake hannunwa wasa. Bai dauke idonsa daga kanta ba yace "Ainau dake ake shirin kai Matar Jikamshi gidan wani?" Ainau ta zaro ido "wallahi babban yaya nima har kuka na tayaka. Ba don kada kuga wautata ba sai nace asthmar Amatullah tayi min daidai." Wani wawan dundu Asmau ta kai mata harda harara. Ainau tace "ba fa har raina naso ciwon ba." Ta dan juya " kaga tana hararata ko" Col. Ishaq ya karbi Husna daga hannun Asmau yana dariya "nima harararki nayi a zuciya. Ya zaki ce asthma tayi. Duk da dai na dauketa a matsayin tazo hanawa a raba Jikamshi da matarsa" Irin kallon da yake yiwa Asmau yana wani lumshe ido yasa Ainau jin kunyar kasancewa a wurin. Sai murmushi suke yiwa juna. A ranta tace ba dole Yaya Asmau taso shi ba. Shi kuwa Yaya Qasim bata ga alamar ya iya nunawa mace soyayya ba. "Allah Ya baku hakuri to. zan fadawa Baba Amatullah ta warke ko gobe Yaya Qasim ya kawo kudi" "Kinga kina jego shiyasa nake tausayinki. Idan aka aura mata wani ranar zaki kwana a guardroom don nasan adduarki ce taci" Col Ishaq ya fada suka

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});