Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 86

Chapter 86

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta jure ta kawar da kai ga dukkan maganar da zata ji musamman daga dangin miji. Haka Allah Ya kaddara mata dole ne kuma sai an sami masu yi mata wannan gorin. Hakuri, ladabi, biyayya, tsafta da iya girki kuma sai ta dage. Ishaq yayi mata karamci da yake sonta a haka ya aureta. Ta zage damtse ta kyautata masa. Kowa ya fadi nasa Asmau tayi kukanta son rai. Bayan ta fita daga dakin ba jimawa Zubaida tazo ta kirata dakin Yassar. Abin mamaki Uwargida ce a dakin Zubaida ta rufe kofar. Sake bawa Asmau hakuri tayi da taso bata mata rayuwa "idan naje muka gana da 'yan uwana zan koma Azare ne. Gidan nan ba zan barshi a cigaba da sabon Allah ba. Da kika ganni babana Limami ne. Da kuruciya muke sauka. Ina da ilimi na daidai gwargwado. Zanyi amfani dashi wurin bawa matan dake gidan shawara da koyar dasu sannan su koma gaban iyayensu. Ba ido gareni ba kada ayi abinda bazan gani ba. Za'a raya gidan da bautar Allah in sha Allah" Asmau taji dadi sosai haka ma Zubaida. Uwargida tace "Asmau ina so ku saurareni da kyau. Nasan sana'ata ba mai kyau bace kuma ina ta rokon Allah gafara. Amma ina son sanar daku wasu 'yan sirrikan rike miji da muke amfani dasu a da muna raba mata da mazansu muna aikata haram. Wannan abin idan kunyi a gidan miji riba zaku samu da lada. Ku zama marasa kunya amma ba tsiwa da fitsara ba. Duk abinda miji yake so kiyi masa kada yaje nema a waje. Wani kinkime jiki da hijabi a dakin miji sai a sallah ko kunyi baki. Ku zauna da kayan da zasu ganku da kyau suji suna sha'awarku." Zubaida da Asmau sai kunya aka fara sunkuyar da kai. Uwargida da taji sunyi shiru tace "kunga ni babarku ce. A bariki nayi amfani da wannan banga riba ba saboda aikin haramci ne. Amma ku gwada a gidan aure wallahi miji sai ya yaba muku. Da ajiye kunya mu kyautata musu muke raba auren soyayya. Matan hausawa kamar munfi kowa kunya. Muyi a waje sannan a gidan auren ma miji yana binki kina nokewa wai ke kin girma. Ai kullum ku nuna musu kamar yau kuka fara kasancewa tare. Sunayen soyayya na zamani samo ki kira abinki. Wani maigida ko baban wane an wuce wurin. Idan miji bai zo da kansa ba ke ki nemo shi. Hanyoyi gasu nan barkatai. Ku dan matso kada aji daga waje ace Uwargida zata bata ku. Allah Ya gani sharrin irinmu nake guje muku. " Ai kuwa su Asmau sunji batu a bakin Uwargida. To dama kunya a wurin irinsu sai a hankali. Baro zance kawai take Zubaida ta gama jin kunya. Ko da ta gama bayani sai dai su kalli juna suyi murmushi. ***** Wanka Asmau tayi saboda ance masu daukar amarya suna hanya. Amatullah kamar tasan ba da ita za'a tafi ba yau ta like mata. Da kyar da dabara Shemau ta hadata da yaranta tasa Yassar yayi saurin kai mata su gidanta. Nan da sati biyu sai a dawo da ita lokacin itama Asmau ta saba. Ana fita da ita kuwa Asmau tasa kuka. An rabata da Ama ji take gara kawai a bata ita su tafi tare. Da kyar tayi shiru ta shirya cikin wani material mara nauyi riga da skirt. Fuska tasha kwalliya sosai ga katon mayafi har ka ta lulluba. Jammu cikin kawayen Shemau ita ta matso kusa da Asmau ta damka mata wani abu kamar zuma kadan a kofi. Asmau ta dan dago kai ta kalleta. "Nasan kin sha abubuwa da yawa shiyasa na zuba miki kadan. Kinsan yadda muke da Shemau kanwa na daukeki. Na bata sauran za'a ajiye a gidanki." Wannan kayan idan batayi da gaske ba cikinta sai ya baci. Kowa da nasa kuma duk abu daya ne. Suna son daga darajarta a wurin miji. Kafa kai tayi ta shanye tsumin. Jammu tayi dan murmushin jindadi. Tasan nan gaba Asmau sai ta nemeta da kanta. Sirrinsu ne na Sokoto. ****** Dirar motoci aka ji wanda yayi daidai da faduwar gaban Asmau. Shikenan ta zama matar aure. Auren da ta fitar da rai ashe tana da rabonsa. Gashi zata bar Umma ta kama rayuwar ibada. Su Mami ne suka zo daukar amarya da wasu 'yan uwansu manya. Da aka tashi fita da kyar aka bambare Asmau daga jikin Umma, ita ma Umma kukan take. Su Anti Bintu ma da Mama Yalwa sunyi nasu kukan. Motoci sunfi goma daga bangaren ango banda na dangin amarya masu motar gida da ta haya. Mata ne kawai suka cika gidan. Biki yayi albarka. Mutan Jikamshi sun dauki amaryarsu Asmau. A motarsu daga wanda yake ja wani soja ne abokin aikin Col. Ishaq sai Walida a gaba. A baya kuma Yaya Abu ce da Mama Yalwa suka saka Asmau a tsakiya. Gida ne flat mai kyau tun daga waje ga filawoyi sun fito ta saman katanga. Gate din a bude yake da yake bazai dauki motoci sama da uku ba dole aka bar wurin da za'a shigo da motar amarya. Tun a nan zaka san anzo gidan amarya saboda kamshin dake tasowa daga ciki. Wannan aikin su Shemau, ne da Rashida, Sabira da Suwaiba. Mata sai son barka ake gida yayi kyau sosai. A cikin falon aka kai Asmau wurin wasu mata iyaye ga Col. Ishaq ta bangaren Hajiya da babansu. Anyi barkwanci suka kare da nasiha. Babu mai iya tanka Asmau domin sun sha gargadi a wajen iyaye maza. Col. Ishaq yana da kwarjini basa son bata masa, ihsani ya sami tangarda. Daga nan aka wuce da ita dakinta wanda Umma tayi namijin kokari wurin sayan kayan kawata shi. kanta a rufe yake tana hawaye har aka zaunar da ita a bakin gado. Wata da tace gidanta na jikin na Asmau mai suna Husna tazo ta dan bude fuskar amarya tana murmushi "Masha Allah amarya Allah Ya bada zaman lafiya. Idan kina da matsala ki rinka nemana. In kina so ma ni kullum sai na shigo na taimaka miki." Ainau dake gefe tayi dariya, Husna baki san wannan angon ba. Sai da aka hada da magiya aka samu matan suka fara fita. Gidan ba babba bane sosai. Daidai mata da miji da 'ya'yansu. Gida ya watse sai makusantan Asmau. Har lokacin bata bude fuskarta ba. Walida tace "kinga ki tashi kiyi sallar isha in da hali kiyi wanka ki canza kaya. Kinsan saboda mutane dakin yayi zafi gaki a kunshe cikin mayafi" "Nima abinda zan fada mata kenan. An taho da kayanki sai ki sami 'yar rigar bacci mai kyau ki saka" Asmau bata san lokacin da ta bude lullubin tana kallon Zulaiha ba harda harara. Dariya suke mata sosai Zulaiha tace "meye na hararata, ki tashi ko na tonaki wallahi" Zubaida tace "don Allah tona" sauran suka rinka naci ita kuma Zulaiha tana ta ja musu rai. Da yake yau bakin yayi lakwas Asmau bata ce komai ba ta shiga inda aka nuna mata bandakin dake cikin dakinta. Sai hamdala take, ko a toilet ba karamin kashe kudi aka yi ba. Duk kayan toilet Abdulhalim ne yayi mata su. Wanka tayi da alwala ta mayar da rigarta akan tawul din.

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});