Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

'yarsa ta bata ta wani ai ya jira nasa lokacin. In Allah Ya yarda sai ta dauko masa abin...." Mama da Umma suka dakatar da Hajjo daga yin mummunar addua. Daga nan suka yanke shawarar washegari da sassafe zasu tafi Azare neman Asmau. Anti Bintu da Shemau duk an sanar dasu haka Abdulhalim da Qasim. ***** Annur da Gaddafi tunda suka isa masaukinsu ko abinci sun kasa ci. Abokin da suka zo wurin party dinsa yayi ta damunsu da su tashi suyi wanka a tafi sai su kalli juna su sunkuyar da kawunansu kasa. Gabadayansu dana sanin baro gidajensu suke yi. Sun baro iyayensu musamman matan cikin tashin hankali domin sun san yanzu ana nan ana nemansu. Yau da suka ga yadda mace ke wahala wurin haihuwa kowannensu shiriya ta saukar masa. Sannan ga adduar da tayi musu bayan taimakonta da suka yi. Suna kallo aka shirya duk 'yan samari sa'aninsu suka fice sai su kadai. Karshe ma shawara suka yanke gobe zasu koma asibitin neman wannan matar daga n[truncated by WhatsApp] ABINDA AKE GUDU🙆🏽26 Batul Mamman💖 Da asuba Zulaiha ta tashi ta dama koko sannan dora ruwan wanka cikin tukunya. Dakin da Asmau take ta shiga ta gani ko ta farka ta tarar da ita a zaune rungume da 'yarta. Zulaiha tayi dan murmushi "Wannan yarinya kamar za'a kwace miki ita. Ke ko dan kunyar nan ta dan fari bazaki yi ba". Asmau ta sunkuyar da kanta tana murmushi suka gaisa. Allah kadai Yasan irin son da take yiwa yarinyar nan. Yanzu bata da burin da ya wuce yadda zata yi ta inganta mata rayuwa. "Wane suna zaki saka mata?" Tambayar Zulaiha ce ta katse mata tunani. "Sunanta Safinatu, sunan kakarta ne". Zulaiha ta karbeta tana kallo "Allah Ya rayaki Safina. Tubarakallah ba dai hanci da idanu ba. Ina tsammanin nan gaba kadan sai an cike takarda zan bari a ganta. Zaki boye mata suna ne?" "Zan kirata Amatullah, baiwar Allah. Burin babanta kenan mu sakawa yaranmu sunan iyayenmu." Muhsin ne ya shigo dakin a guje kamar an biyo shi. "Umma gudu bandaki ki rufe kofa ga Abba nan da wayar radiyo yana nemanki". Kusan faduwa Zulaiha tayi garin sauri ta mikawa Asmau jaririyarta ta fita a guje. A tsorace Asmau ta tashi tana kokarin buya a bayan labule don duk ta kidime da taji muryarsa. "Ke Zulaiha fito nan barauniya. Na ajiye dubu biyar a aljihun wando yanzu na duba babu". Inuwar mutum ya gani a bayan labulen ya daga wayar zai saukewa Asmau a jiki yaji kukan baby. Sai a lokacin ya dan nutsu yana kallonta. Ita ma idonta a kansa ta zaro su a tsorace. Yayi saurin gyara tsayuwarsa. "Ashe bakuwa mukayi a gidan. Sannu da zuwa. Ya mutan gida?" Sai a lokacin Zulaiha ta shigo muryarta na rawa tace "Gidado ashe ka tashi. Bakuwa mukayi jiya zata kama hayar daki a nan. Mijinta ne tafiya ta kama shi." Hankalin Gidado duk yana kan Asmau yace "babu komai, ai kin kyauta da kika bata wurin zama. Dama kudin kosai zan tambayeki na nawa za'a siyo?" Yana magana yana bin jikinsa da susa. Zulaiha tace masa ta bayar da kudin yace to idan ta shigo daki sai ya bata. Kana ganinsa kasan karya yake yi ko kuma bai saba bada kudin komai a gidan ba. Fitowar da yayi da niyyar dukanta dama salon ta tsorata ne ta bashi kudi. Har ya fita motsi kadan sai ya juyo ya kalli inda Asmau ke tsaye. Da yasan da bakuwa bazai yarda ya kunyata kansa haka ba. Banda abin namiji yaushe mutum zaiyi tafiya ya bar mace kamarta a gida. A tsorace ta samu wuri ta zauna tana tunanin kyau irin na mijin Zulaiha. Duk da kana ganinsa kaga mai shaye shaye amma hakan bazai hana mace ganin kyansa ba. Duk da taga kyan 'ya'yansa amma babu wanda ya kama kafarsa. Zulaiha tayi dan yake "kinga irin tawa kaddarar ko? Kiyi hakuri nayi karya nace haya zakiyi. Da ban fada masa kina da aure ba babu abinda zai hana shi nemanki." Asmau ta sake zaro ido tana dafe kirji "duk da kinsan hakan shine kike zaune dashi"? "Hmmm ke dai indai _abinda ake gudu_ ya riga ya faru to sai dai hakuri." Darajar Asmau yau Gidado ya bayar da kudi banda kosan da Zulaiha ta siyo an karo bredi. Zinaru babar Gidado ko abinci bata ci ba ta dauki kayan miyarta da kayan kadi da take siyarwa ta fice daga gidan. Sai da suka ci abinci kowa yayi wanka sannan Zulaiha ta zauna bawa Asmau nata labarin. "Kamar yadda kika ji sunana Zulaiha. Iyayena duka yan Yobe ne zama ya kawosu nan. Ina da yayye maza uku ni kadai ce mace kuma auta. Babanmu yana zuwa saro kaya daga Kano da Lagos shiyasa duk wani abu na yayi ko kayan burgewa to zaki gani a jikina domin ba karamin gata suke nuna min ba shi da Inna. Nayi makaranta har na kai aji biyar a sakandire sannan na hadu da Gidado. Na tabbata da kika ganshi dazu kin fahimci mutum ne shi da Allah Yayiwa baiwar kyau. Haduwarmu ta farko Allah Ya dora min masifar sonsa. A lokacin Zinaru mahaifiyarsa tana dillancin kaya. Da zarar Baba ya dawo daga saro kaya zata zo ta diba ta sayar. A hankali aka fahimci ni da Gidado mun fara soyayya. Duk wani dan kudi da abu mai kyau idan Baba ya bani sai na bashi ya sayar saboda tausayinsa da nake ji. Shiyasa ya like min yake nuna min soyayya ni kuma duk na makance da irin halayyarsa ta shaye shaye da neman mata wanda mutanen unguwa da yawa suka sani. Ita kuma Zinaru babu wanda yasan mijinta ko danginta. Kawai ganinta akayi da danta. Baba yayi min fadan ya dokeni duk a banza. Ya dena bawa Zinaru kaya ya hana Gidado zuwa gidanmu. Amma daga makaranta sai na gudu na tafi gidansu. Idan naje nice wanki, wanke wanke, shara da duk wani aikin wahala nashi da nata. Idan zan tafi na kawo kudi na bata. Itama baki ga yadda take sona ba." Zulaiha ta share hawaye "A lokacin gani nake babu abinda zai nema banyi masa ba saboda so, bana taba ganin laifinsu. Aka hanani zuwa makaranta, karshe ma wan Baba ya kawo dansa don ayi min aure su huta. A ranar auren na gudu muka je gidan mai unguwa ni da Gidado muka kai karar iyayena. Mai unguwa ya aika aka kirasu ya bawa Baba shawarar ya barni na auri wanda nake so Baba yaki amincewa. Guguwar so na dibana nace idan ban auri Gidado ba zan shiga duniya." A nan ma Zulaiha sai da ta tsaya tayi kuka sosai "Baba yana kuka yace ya amince ayi auren. A nan aka daura sai dai gidan su Gidado ciki da falo daya ne suke haya. Haka iyayena suka rufe ido suka yi min kayan daki sannan Baba ya bani wannan gidan da kike gani amma ya gargadeni duk ranar da na tako zuwa gidansa tsinuwace zata biyo baya. Wannan dalilin yasa nake ta shaye duk wani bakincikin da na fara gani tun kafin na cika sati a gidan. Kaf kayan dakina sun sayar sannan babu abinci. Matar da ta ranta min kudi

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});