Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na amfani Shu'aibu da Bara'atu sun saka. Kwanan amarya biyu su Bara'atu suka iso Kano. Kayansu ta kwatantawa masu mota aka kai hotoro ta wuce kofar mazugal. Makota ke sanar da ita su Hajjo sun tashi. Tayi mamaki sosai to ina suka koma? hotoro ta wuce da sa ran zata je gidan Lami a kwatanta mata inda suka koma. Suna isa gate din gidan Jafar ya fita ya budewa mijin Anti Bintu da ya tuko su a motar da yanzu ta zama ta Bara'atu ya shiga. Yaran Rabe su biyu ta gani suna wasa a waje ga Hajjo zaune karkashin bishiyar goba tana shan iska. A sanyaye Bara'atu ta karasa kirjinta na dukan uku uku. Hajjo ta washe baki tana yiwa jikokinta maraba. Bara'atu ta gaisheta tana kallon kofar gidan a bude. Hajjo tayi tsaki "ya naga duk jikinki yayi sanyi ne? Ki kwantar da hankalinki nayi tunanin bai kamata na matsa miki ki auri Rabe ba shine muka dawo gabadaya a taro a kula da marayu. Kuka ne ya tasowa Bara'atu sai dai kafin ya kai ga fitowa ta ga Sagira yar kanwar Hajjo ta fito Garzali yana binta a baya yana tsokanarta. Hajjo ta saki murmushi "ga amaryar Rabe fa shekaranjiya ta tare. Bari tazo ta nuna miki dakunanku ke da yara. Daki har biyu Rabe yace a baku. Su Jafaru dakinsu yana nan kusa da na kawunsu Garzali" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Bara'atu ke fada saboda tsananin bacin ran da take ji a wannan lokacin. ABINDA AKE GUDU🙆🏽16 Batul Mamman💖 Wannan karshen satin tun alhamis Abubakar yazo. Kullum sai yaje wurin Asmau sunyi hirarsu yadda suka saba. Ranar asabar ya wuce Shanono wurin Qasim suka je daurin auren wani dan uwan Qasim din. Daga nan suka koma gidansu sai zuwa yamma yayi niyar komawa cikin Kano. Zaune suke a dakin Qasim suna kallon ball wayar abokin nasa tayi kara. Rage sautin TV din yayi ya amsa wayar. Ya dan jima suna hira d wadda Abubakar ya fuskanci mace ce sai daga baya yaji akalar hirar ta canja. Qasim yana tambayar yarinyar wane irin kaya ta saka. Murmushi yayi bayan ta bashi amsa "me kika saka a ciki?" "Ni kwance nake a daki da shorts(gajeren wando) ina shan iska ina tunaninki" (karya yakeyi. Kufta da wando ya saka). Irin wannan hirar ya kusa rabin awa suna yi da budurwarsa. Abubakar sai kada kai yake don takaicin wannan hali na Qasim. Yayi fadan da nasihar har ya gaji gashi ya kasa rabuwa dashi saboda shakuwarsu. In dai hirar banza ce a waya to Qasim ya ciri tuta. Sai ance ya fidda matar aure yace duk mata babu tagari. Mugun kallon da Abubakar yake jifansa dashi yasa ya katse wayar yana dariya. "Ya Ustaz irin wannan harara haka. Ni fa bance ka tsaya jin hirar ba duk ka wane hade rai." "Yanzu bazaka dena wannan muguwar dabi'ar ba? Ina jiye maka tsoron kada watarana kayi me gabadaya. Kasan zuciya bata da kashi". Kujerar kusa da Abubakar ya dawo ya zauna. "Kaima kasan duk abuna bazan yarda nayi lalata da 'yar mutane ba. Irin wannan hirar dai da dan abinda ba'a rasa ba shi muke yi don mu rage yawa. Sanin kanka ne yadda aure yayi tsada ni kuma ba wani abu na tara ba. To kuma ga abu mu muna so suma matan suna so. Sai a taimaki juna". Runtse ido Abubakar yayi "ji yadda kake cewa a taimaki juna kamar wani aikin kwarai. Kana dan malam har ka manta haramcin taba jikin macen da ba muharramarka ba? Ko ka manta inda Allah SWT Yake cewa : *WALA TAQRABUZ ZINA INNAHU KANA FAAHISHATAW WA SAA'A SABILA* (ISRA' 32) Ma'ana _KUMA KADA KU KUSANCI ZINA DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA HANYAR BATA_ Taba jikin budurwa da niyar gusar da sha'awa batare da kunyi abin gabadaya ba yana cikin abinda Allah Yayi hani dashi. Kallo wannan da irin maganganun nan da kuke yi duk yana ciki. Wata rana sai kaga anyi abinda ake gudu azo ana cizon yatsa." Qasim yayi murmushi jikinsa ya danyi sanyi sai dai shaidan bai barshi ba. "Naji kuma duk nasani to amma ka manta cewa Allah SWT mai yawan gafara ne da jinkai? Idan mutum ya aikata irin haka tuba fa kawai zanyi a kankare min zunubin. Haba Abubakar kaima kasan yadda zuciya take. Ni a haka nasan ina kokari don ban taba ketawa kowace mace haddi ba. Za'ayi abin sama sama gayyar ta watse." Abubakar yace "Muna cikin wani zamani ne da hanyoyin gurbata tarbiya musamman masu nuni da zina suke da matukar yawa. Cartoon wannan sai kaga mage da bera suna kiss. Duk a haka ake lalata mana zukata. Na dade da sanin ina cikin maza masu karfin sha'awa shiyasa kaga na dage da yawan azumin litinin da alhamis. Idan naga abin zai dameni har sauran ranaku inayi. Manzon Allah SAW yace a lokacin da mutum yake zina fa babu imani a tare dashi. To me zaisa mu biyewa son zuciya haka kawai kana kan wata mace mala'ikan mutuwa ya ziyarce ka". Qasim ya dubi abokinsa. Tabbas Abubakar ba tun yau ba baya cikin maza masu kallon mata. Shiyasa ake masa kallon mai kunya sosai shi kuwa yana yi ne don ya kare zuciyarsa. "In Allah Yaso zanyi kokarin denawa sai dai fa abin sai a hankali. Bazan maka karya ba wallahi na saba sosai. Allah mun tuba." Da haka hirar ta kare bayan la'asar Abubakar ya koma gida. ***** Washegari lahadi Umma ta tafi da Aina'u yinin 'yar wata kawarta sai Asmau da Yassar a gida Abubakar ya kirata a waya zai zo suyi sallama don yau da wuri yake son tafiya. Sauri tayi ta karasa girki sannan tayi wanka ta canza kaya. Kwalliya tayi sosai irin yadda take karantawa 'yan matan littafi na yiwa samarinsu. Ta saka wata doguwar rigar atampa maimakon ta daura dankwali tasa hijab ko mayafi mai mutumci yadda ta saba sai ta dauko wani karami a kayan Aina'u ta yafa rabin kanta da yasha sabon kitso duk a bude ta gaba. Falo ta koma ta zauna sai taji kunyar ya ganta a haka. Ta tashi ta koma zata canza wata zuciyar tace tayi zamanta abinda sun kusa aure kuma dai haka ake yi yanzu don ita duk abinda ta karanta har ranta gani take yi daidai ne saboda a yadda ta dauki marubuta masu buga littafi da online komai suka rubuta basa kuskure. Sake shafa hoda tayi ta dawo falon. Tana zama Abubakar yayi sallama tare da neman izinin shigowa ta amsa masa. Gabansa ne ya fadi da yaga Asmau. Tayi kyau sosai gashi tana da 'yar kiba sai rigar ta kamata a kirji da kugunta. Ba wai bai taba ganin yanayin jikinta ba saboda yau da gobe yakan ganta babu mayafi amma sai bisa kuskure. Yau kuwa shigar ta tsaya masa a kokon rai har ya kasa dauke idonsa daga gareta. Murmushi tayi na nasara saboda yadda taga yanayinsa ya canza. Tunda ta fara karance karance da hirarsu da Walida taji ta matsu ko hannunta ne ya dan rike itama taji yadda ake ji. Wani juya ido tayi duk sauran kunyar suka bace "Mine ka zauna mana." Wani jan numfashi yayi "Asmy kinyi kyau" Tayi masa

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});