Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Abinda Ake Gudu Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mata kashin kaza. Jafar ya juya ya matan dake binsu kamar jela yace duk su fita. Surutai da gunaguni suka rinka yi har suka watse. Aina'u da Yasar ma yace duk su tashi. Yasar baiso hakan ba a ganinsa shima ya girma ransa a bace ya tura Aina'u suka shige ciki. Kowa a zaune banda Asmau dake rakube a jikin kofa. Alh Rabe ya zare mata ido "munafuka algumguma ai sai kizo ki zauna kin wani tsaya mana a ka kamar sa'anninki." Da sauri ta zube a wurin da take tsaye ta dukar da kanta hawaye na kwarara a kumatunta. Hajjo ta furzar da goron bakinta a kan kafet tace "hankalinki ya kwanta ko Bara'atu? 'Yarki ta janyo mana abin kunya ta bata mana suna a gari. Tun rasuwar Shu'aibu babu yadda bamuyi dake ba akan ki bari 'yan uwansa su raba 'ya'yan a tsakaninsu kika ki amincewa. Yau wa gari ya waya uhmm? Dama tarbiyar mace mai zaman kanta har wata tarbiya ce." Hanci ta tsaya fyacewa tana kukan Bara'atu ta cuce ta. Umma tayi shiru kawai, tun dazu da aka aika musu da rasuwar Abubakar babu wanda yazo cikinsu. Yinin bikin ma cewa suka yi tayi a gidanta suma zasuyi nasu ko babu amarya. Sai yanzu da wannan abu ya faru shine duk suka taho. Harda Yaya Abu da babu abinda ta halarta na bikin wai tana ciwon wuya. Alh Rabe ya doka tsaki "dama me kike tsammani daga mace irin wannan Hajjo? Saboda na taimaki rayuwar 'ya'yan dan uwana fa har shahada nayi nace zan aureta duk da yadda nake kyamar mayu 'yan garinsu amma taki. Yanzu ta fada muku shegen da ya dirka mata cikin ko kuwa saboda samarin sunyi mata yawa bata san waye uban ba?" A kufale Jafar yace "Kawu nayi tunanin zama akayi na maslaha akan matsalar nan ba bakaken maganganu ba." Umma ta watsa masa harara don yayi shiru amma duk da haka sai da Yaya Abu ta hado masa ashar ta kunduma masa. Sannan ta dubi Asmau "to karuwar cikin gida wadda ake nuna mana kunfi kowa tarbiya. Cikin na waye don ko ni ban yarda na yaron nan bane Abubakar bawan Allah. Gara da Yalwa taki karba zaku gurbata musu asali." Jin batayi magana ba har Hajjo ma ta sake tambaya yasa Kawu Rabe yayi kanta yana haurinta da kafa. Tun tana zaune har sai da tayi kasa yana tattaka ta. 'Yan uwan Umma suka tashi aka rike shi sannan suka janyeta. Umma dai sai kukan zuci. Duk abinda aka yi musu a yau Asmau ce ta janyo mata saboda haka bata da bakin magana. Kallonsu take yi suka ci gaba da caba musu bakaken maganganu 'yan uwanta suna karewa sannan suka tashi. Hajjo tace "ki shirya sati mai zuwa ki turo min Yasar da Aina'u gara nasa su a gabana don bazan bari zuri'ar Shu'aibu ta gama lalacewa ba ina raye. Ranar gidan Umma ansha kuka kala kala. Shema'u duk yadda suke da kanwarta ko inda take taki kallo. Asmau ta bata kunya sosai. Anyi ta tambayarta kuma taki magana tunda sunki yarda cikin Abubakar ne. Abu dai har tsakar dare suna dakin Umma ana ta magana daya. Asma'u kuwa babu wanda ya shigo dakinta. Kawayenta da suke gidan gabadayansu bata san inda suke ba har da aminiyarta Walida wadda take ganin kamar bazata gujeta ba a wannan yanayin. ABINDA AKE GUDU ๐Ÿ™†๐Ÿฝ5 Batul Mamman๐Ÿ’– Zaune take kan abin sallah tana addu'a tana zubar da hawaye. Bata taba tsammanin ganin rana makamanciyar wannan ba a rayuwarta. Babu Abubakar ga cikinsa a jikinta batare da aure ba. Yau da cikin aure ne bata san irin soyayya da gatan da Umma da Mama Yalwa zasu nuna mata ba. Ashe haka ake ganin bambancin rayuwar wadda aka shafa fatiha akanta da wadda ba'a shafa ba? Gashi dai duk abu daya suka yi, amma mai aure sai ta zama tauraruwa har idan batayi ciki ba ayi ta korafi ko aji tausayinta. Ita gashi kuskure sau daya tak, tayi cikin da bata bukata gashi hatta mahaifiyarta tana nuna mata kyama. Aure ibada ne, zina kazanta ce. Wani kukan ne yazo mata da taji cikinta na kukan yunwa. Yanzu idan taci abinci abinda ke cikinta ma zai samu? A hankali ta shafi cikin zuciyarta na kuna. "Wayyo Allah, Ya Allah Ka jikan Abubakar Ka karbi tubanmu" abinda ta fada kenan cikin raunanniyar muryar da ta gama dashewa don kuka. Akan abin sallar bacci ya saceta tana rungume da AlQur'ani. Gari na wayewa ta rinka jin muryarsu Umma a kitchen ana dafa abincin da ta fuskanci na sadaka ne da za'a kai gidan Kwamishina. Tana son fita amma tana tsoron abinda zai biyo baya. Duk wannan tashin hankalin wata muguwar yunwa take ji sai dai ko zata mutu bazata fita neman abinci ba. Sai wurin karfe goma taji gidan ya danyi shiru. Tana nan zaune Anti Bintu ta shigo dakin. Itama dai ba sakin fuska tayi ba, ta shigo dauke da plate din abinci da ledar pure water. A gaban Asmau ta ajiye ta juya ko gaisuwar da take mata bata amsa ba. Sai da ta fita ta fashe da kuka. Rana daya Asma'u ta zabge idanu sunyi ciki kamar ta shekara a kwance. Tana jin tausayinta sai dai dole a nuna mata kuskurenta. Abincin da ta kai mata ma babu wanda yasan ta kai. Kuka tayi sosai sannan tabi bayansu Umma da suka riga suka tafi gidan rasuwar. Su Umma zasu shiga gidan taji Mama Yalwa tana cewa alajirin da ya kawo abincin ya mayar musu da abincinsu bata so. Dama tasan tun faruwar al'amarin jiya dole Mama ta canja mata. Sai dai mutuwa ta kori komai shiyasa ta daure tazo. Sallama tayi suka shiga sai tayi kamar bata ji abinda Mama ke fada ba. Itama kunyar ganin Umman tayi sai ta bar gaban kulolin abincin. Haka suka gaisa kowa fuskarsa a cunkushe su Umma suka sami wuri suka zauna. Babu mai cewa komai dama gidan rasuwa ne. Mutane 'yan kallo suka taru suka zuba musu ido. Haka ce ta kasance kullum Umma zatayi abincin sadaka kuma su je gidan su zauna sai anyi la'asar su koma gida. Tsakaninsu da Asmau kuwa ko kallonta batayi duk da tana fitowa ta gaisheta. A rana ta shida ne da daddare wata dattijuwa cikin 'yan uwan Umma tace ya kamata su zauna suyi magana akan lamarin Asmau. Umma tace "kayya dai Gwaggo, me ya rage mana kuma banda zubewar mutumci." Gwaggo tayi dan murmushi "Bara'atu nayi tunanin ke mace ce mai hangen nesa da tawakkali. Me kike tsammani ga yarinyar da take cikin yanayi na Asmau ace kowa ya juya mata baya? Idan abin ya isheta dole tayi tunanin nemawa kanta mafita koda kuwa mafitar halaka ce fiye da halin da take ciki yanzu. A 'yan kwanakin nan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin damuwa kuma muna fatan ta yi nadama. Kamata yayi a sake tambayarta lallai ta fadi gaskiya game da cikin sai a san matakin dauka." Kowa a dakin yayi na'am da shawarar. Shema'u dama mijinta yayi mata fada akan rashin kula Asmau da suke yi ba shine mafita ba. Umma tace aje a kirawo Asma'un. Gabanta na faduwa ta shiga dakin kowa ya zuba

Table of Contents

Chapters

103 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});