Chapter 78
Chapter 78
haifa? Tausayi Uwargida ta rinka basu. Asmau ta soma kuka saboda yadda ta tuna Uwargida da iya gayu duk girmanta. Yanzu kuwa sai da dauriya zaka iya zama kusa da ita saboda warin jiki. Su Umma sun gama gaisawa da Uwargida sai Haj Lubabatu ta dan yunkura zata tashi. Col. Ishaq yace "Hajiya kafar ce?" Bata bashi amsa ba sai matsawa da tayi gaban Uwargida ta zauna kusa da Zubaida tana kare mata kallo. Kuka sosai ya kwace mata tace "Habiba" Uwargida ta fara mika hannu inda taji kira. Rabonta da amsa wannan sunan tun ranar da ta baro garinsu. Hannunta har rawa yake tana ta mika shi ko zata kama mai kiran tace "wace ce don Allah, babu wanda yasan sunana sai 'yan garinmu" Hajiya sai kuka ta kara shigewa kusa da Uwargida. Col. Ishaq ji yake kamar ya janyota. Me ya hadata da wannan matar. Hannuwanta duka biyu ta rike "Lubabatu ce, Luban gidan Sarkin dorin Jikamshi" Salati sosai Uwargida ta saka kafin ta rungume Hajiya. Babu kyama Hajiya ta rungumeta itama suka barke da kuka. Kowa sai kallosu yake. Matan gidan sun fito ganin kwaf Qasim ya daka musu tsawar da ta kidimasu suka bar wurin suna karo da juna. Uwargida ta share majina da kasan zaninta tace "Allah mai iko, ashe zan sake ganin na gida. Luba ina Baba da Inna, ina 'yan uwana?" Cikin kuka Hajiya tace "Liman da Inna sun dade da rasuwa. Yayarki Indo ma babu ita. Sauran 'yan uwanki duk suna nan an tara 'ya'ya da jikoki" "Allahu Akbar, Allah Ya jikanku Baba, Allah Yasa sun yafe min kafin su rasu" Tana kuka ta labarta musu yadda almajirin Liman yayi mata ciki ashe ma fyade ne yayi mata kuma ya gargadeta kada ta fada har ciki ya bullo. Babu uzuri ko neman ba'asi iyayenta suka tsine mata. Wannan kuskure ne babba. Yana da matukar amfani jurewa wajen kula da yara idan sunyi kuskure domin a toshe kofar gaba. Tunda ta fiti take aikatau da ayyukan wahala domin taci abinci. A haka cikin ya bare tana yawo a gari. A wani gidan aikinta ne a Bauchi maigidan ya kuma yi mata fyade da ta fada matarsa tayi mata duka duk da lokacin shekarunta sunyi gaba don da jima tana rayuwar kunci da wahala. Maigida ya karyata kamar yadda aka saba ji. Shine da ta fito ta sami uwardaki. Bata zubar da cikin ba ta haifi Zubaida. Da girmanta ta fara sana'ar karuwanci kuma tace ta gwada rashin imani kamar yadda mutane suka gwada mata. Sai shekaru biyu da suka wuce da ta kamu da lalurar ido tayu nadamar rayuwarta. Duk matan gidan sun dena bata kudin haya ga rashin abinci. Ta kare da bawa mutane shawara da su rinka taimakawa masu raunin imani da wadanda ke cikin matsanancin hali don gujewa samuwar karin mugayen dabi'u a cikin jamaa. Su Mama duk anyi kukan tausayin labarin Uwargida da kuma dadin handala da Asmau tayi dacen haduwa da mutane nagari. Wannan kuma zamu iya cewa harda adduar da suke yi mata ba tsinuwa ko zagi ba. A gidan aka bar Zubaida da Kawu Garzali. Sun yanke shawarar idan zasu koma Kano a tafi da ita sai a kaita Jikamshi taga 'yan uwanta ko da basa maraba da dawowarta. ***** Daga nan gidan Rashida suka wuce. Dama tasan da zuwansu. Sada ma yana gida yana jira ga su Abba duk an zama samari. Cikin gidan aka yi musu shimfida mazan kuma suna dakin nan da Asmau ta taba zama. Tana shiga gidan sai kuka da ta tuna lokacin da ta zauna ga ciki ga rashin iyaye a kusa. A falo taga Sada ya kalleta fuskarsa dauke da murmushi yace "Asmau kece kuwa?" Tana kuka ta durkusa har kasa ta gaishe shi. Sada ne mutum na farko da ya fara taimakonta a rayuwa sosai bayan Zubaida mai bata shawarar kada ta zabi gurbatacciyar rayuwa. Wurinsu Abdulhalim yaje inda aka ajiye musu kayan abinci. Sai da suka yi sallah suka ci abincin. A ciki suma matan sallar suka yi aka ci abinci. Nan hira ta barke ana tuna baya ana kuka da dariya. Rashida tace "yakamata watarana muje kiga Yaya Tagwai fa" Asmau tayi murmushi, Yaya Tagwai ai ta janyo mata kara shiga garari. Cikin yaran kuwa babu wanda ya tuna ta sai Abba. Sai da suka yi laasar a ranar dai suka kama hanyar Jos. Rashida da Sada sai lokacin biki zasu taho Kano. Sun sha tafiya jiki kuma ya fada saboda zaman mota. Duka matan a gidan Mami akayi musu masauki sai gari ya waye zasu gidan Zulaiha. Asmau ta damu sosai da ita saboda dena samunta da tayi a waya. Col. Ishaq ne ya samarwa mazan masauki a cikin barikinsu na sojoji dake garin. Shi da Matarsa sai dare suka sami damar yin waya aka biya bashin soyayyar da ba'a yi ba a ranar. Mami da yaranta sunyi kokarin karrama bakin Kano. Bilkisu sai murna anzo gida. Da safe wurin shadaya suka gama shiri aka dunguma zuwa gidan Zulaiha. Motarsu na tsayawa Asmau ta hango Humaira da karuwar roba a kanta cike da ruwa. Da sauri ta fito ta kira sunanta. Ai tuni Humaira ta saki robar ruwan ya kware a jikinta ta rugo da gudu ta dafe jikin Asmau. Sai ga kannenta suma duk ruwan suka. Yara sai murna suke suna tambayarta ina Ama. Kusan janta cikin gidan suka yi tawagarsu Umma suka biyo baya suna mamakin yadda yaran ke murna haka. A durkushe bakin murhu tayi tozali da Zulaiha tana ta hura wuta tana tari. Tsaye a gefenta kuma Zinaru ce ta harde kafa tana masifa "malalaciyar banza, tun dazu hada wuta ya gagareki. Yanzu idan suka fito da me zasuyi wanka. Kinsan Gidado baya son ruwan sanyi...." Zulaiha tace "Zinaru kiyi hakuri itacen ne mai danshi" Tun a bakin kofar Asmau ta soma hawaye. Rayuwarta ta gyara ga Zulaiha cikin matsanancin kunci har yau. Duk ta kara figewa sai dan wuya kamar kazar mayu. Cikin sauri ta karasa shigowa tace "Zulaiha" Tashi Zulaiha tayi da sauri itama ta nufo Asmau cike da murna da mamaki. Rungumar juna sukayi suna kukan yaushe gamo. Zinaru babu bakin magana saboda yadda gidan ya cika da mutanen da Asmau tazo dasu. Borin kunya ta soma da taga su Shemau na binta da mugun kallo. "Haka ake tarbar baki kin tsareta a hanya kuna kuka. Ke Humaira maza shimfida tabarmar nan a rumfar babanku. Kai kuma Ali jeka ka taso babanku. Yau Asmaun da yake ta jira ta dawo" Wata mace ce wadda da kadan zata girmi Humaira ta fito tana yatsina fuska. "Hayaniyar me nake ji haka? Zinaru wannan banzar ta dafa min ruwan wankan ko kuwa?". Zinaru ta galla mata harara zata bata musu harka. A yadda taga mutanen da shigar Asmau tasan akwai maiko. Har ta fara nadamar barin Gidado da tayi ya auro 'yar mutumin da ya bashi shago a kasuwa. Zulaiha sai murna take ta shimfida musu tabarma da zannuwanta wankakku biyu don babu abinda zata basu su zauna. Basu zauna ba sai tausayinta da suka rinka ji. Zulaiha tana cikin mawuyacin hali. Yaranta kaf babu mai zuwa makaranta yanzu. Duk abinda ya rage mata dashi Gidado yayi aure. Watarana ya sha
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103